Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 39

Sponsored Links

PAGE THIRTY-NINE*

 

Da gudu sukayo kanta cikin tashin hankali Hajiya taja da baya tace “mun shiga uku Kaka jini ta bakinta da hancinta kinga wani yana fita ta qasanta zata mutu Kaka anya Adamu bashida mental problem kuwa yaraba uwa da yarta a daidai wannan lkcn da kowacce uwa tafi buqata da tausayin danta Kaka ina Hameed zaikai Shurafah yanzu idan Umaimah ta mutu akan wannan dalilin me Adamu zaice da ubangiji?”

Related Articles

 

Riqeta Kaka tayi tace “me..mekike cewa Zulaiha maza ku tafi Asibiti ina zuwa nima” tana fadin haka tayi sama da gudu gurin Daddy ta fara buga qofar kamar zata balleta fitowa yayi ya bude ta cukuikuiyeshi tace “ina ka bari Hameed ya tafi da yarinyar nan to wlh ka fita da gaggawa ka nemoshi ka karbowa Umaimah yarta kafin fushina ya hau kanka ku baku da hankali da tunani kullum baku da aiki sai yanke hukunci cikin fushi”

 

Tana fadin haka ta sake juyowa ko mayafi babu a jikinta ta fito waje ta tsari taxi ta sanar dashi inda zai sauketa suna tafiya tana cewa dashi ya qara gudu cikin saa tana zuwa qofar gdan nashi dake FRW Layout ta hangi motarsa da wata motar a qofar gdan ta cillawa driven 1k tayi ta fada cikin gdan a guje amma me sai ta rinqa jiyo wani kakari yana fitowa daga parlourn da sauri tasakai ciki idonta kan Shurafah ya fara sauka dake dauke hanun Sarah tanata kukan neman uwa shikuma yana kwance a qasa sai fitar da dafara yakeyi mijin Sarah yanata bashi taimakon gaggawa tare da danna masa.

 

Cikin tashin hankali Kaka tace “mun shiga uku mukam wannan wacce irin masifa ce ta nufomu ne” daidai lkcn Daddy ya shigo don cika umarninta.

 

Dafe bango yayi da sauri tare da furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji’un” mantuwa daya Daddy yakeyi a rayuwarsa shine matsalar zuciyar da aka haifi dannasa Hameed da ita.
Da sauri ya qarasa inda yake kwance yana fitar da wani wahalallan numfashi ya rungumoshi yana jijjigashi yana cewa “Abdulhameed! Abdulhameed!! Abdulhameed!!! Babana ka tashi kada ka fada a bakin mala’iku kada muyi irin wannan rabuwar dakai kada ka mutu kabarni babana ba qinka nakeyi ba wlh inasonka”

 

Kuka yakeyi sosai kamar qaramin yaro yana girgiza dannasa Kaka itama tana kuka tace “Shikenan ai kun kashesu kun huta saura yar itama gatanan Adamu kasa wuqa ka yankata sai ayi jana’izarsu gabadaya su ukun kukuma ku rayuwa a duniyar ku dawwama babu jarabawar ubangiji amma inaso ka sani nidai bazan yafe maka haqqi yarannan ba kuma Allah bazai yafe maka ba saboda shugabanci ba hauka bane Allah ma daya haliccemu munayi masa laifi ya yafe mana balle kai abin halitta Mai tarin dauda da zunubi”

 

Tana gama fadin hakan Hameed yaja wani dogon numfashi komai na jikinsa ya daina motsawa, wani ihu Daddy ya saki yace.

 

“Shikenan na kasheshi da kaina Innanillahi wa innah ilaihir raji’un Hameed….” Abubakar ne ya matso ya daga hanun Hameed din ya matse wata jijiya ya zubawa yatsun qafarsa ido babban yatsansa yada ya motsa yayi ajiyar zuciya yace “bai mutu ba akwai sauran numfashi a jikinsa ayi saurin kaishi asibiti”

Ai kafin Abubakar ya ida rufe bakinsa Daddy ya hada qarfinsa ya dago Hameed din Abubakar ya taimaka masa suka sashi a mota tun a hanya ya kira likitansa ya sanar dasu abinda ke faruwa.
Suna zuwa aka rufar masa aka fara jorner masa na’urori.

 

*************************

 

Ita kuwa Umaimah tunda aka kaita asibitin batasan waye a kanta ba daqyar likitocin sukayi nasarar tsayar da jinin dake zuba ta qasanta na hancinta da bakinta kam basusha wahalar tsayar dashi ba saboda kawai buguwa ce, saida aka farke dinkin da akayi mata aka kankare aka sakeyi mata sabo sannan aka daura mata drip Hajiya tana zaune a kusa da ita ta zuba mata ido tausayinta yana qara narkar Mata da zuciya Kaka ta shigo dauke da Shurafah a hanunta.

 

Da sauri Hajiya ta tareta ta karbi yarinyar da tayi kukanta harta gaji ta koma bacci tanajan zuciya tayi hamdala tace.
“Hankalina yana gurin yarinyar nan Kaka ina Hameed din?” zama Kaka tayi tace “yana emergency section kunsan matsalar danku kunma fini sani tunda kune kuka haifeshi saboda haka idan kun kasheshi hankalinku zaifi kwanciya”

 

Da sauri Hajiya ta tare Kaka da cewa “wai kina nufin ciwonsa ne ya tashi?” girgiza kai Kaka tayi tace “abubuwa da yawa daya dade yana binnewa a zuciyarsa sune suka hadu da wannan abun da kukeyi masa akan qaddarar da baku isa ku canzata da bacin ranku ba na tabbata da ace ana dawowa da mutum book din predestinations dinsa da Hameed yana cikin mutane na gaba² da zasuyi gaggawar sauya tasu qaddarar amma kun kasa fahimtarsa kun kasa yi masa adalci da uzuri a cikin rayuwarsa komai fa da kuka gani yana faruwa ne cikin sahalewa da buwayar ubangiji wlh na tabbata idan yaron nan ya rasa rayuwarsa ta wannan hanyar kema kina da kamasho kuma kece umul aba’isin faruwar komai Zulaiha kinada kaso me tsoka cikin abinda ya faru tsakanin Baby da Hameed saboda haka kiyi gaggawar tuba kema don basu kadaine suke cikin fushin ubangiji ba harda ku da kuka kasa sama musu mafita me kyau”

 

Sosai kalaman kaka suka daki zuciyar Hajiya kuma sukayi mugun sanyaya mata jiki qafafunta taji suna neman gaza daukarta ta sulale ta zauna a qasa kan tiles tana kuka me tsima zuciya tana qara shigar Shurafah jikinta tace “Allah na tuba astangafurullah ya Rabbil samawati wal ardi kaicona dana kasance me yanke hukunci cikin fushi kaicona dana zamo me gyara barna da barna kaicona dana zamo silar zuwanki duniya bata hanyar aureba Zulaihat me zan fada miki ranar da kikaji labarin nice silar zuwanki duniya ta wannan qazamar hanyar wayyoh Allah dama ka karbi rayuwata kafin wannan lkcn na zamo uwa mara amfani uwa me qoqarin rusa farin cikin yayanta da furucinta na tabbata da banyi furucin tsinuwa ga Hameed ba da babu abinda zaisa ya saki matarsa…..”

 

Ta qarasa mgnr cikin wani irin kuka me ban tausayi sun jima a haka kafin ta samu qwarin gwiwar miqewa ta fita ta nufi pharmacy din asibitin ta siyo madarar da zaa iya bama yarinyar ta dawo ta jorner kettle ta dafa ruwan zafi ta hadama yarinyar ta sanya a cikin feeder ta sanya cikin ruwan sanyi kafin Shurafah din ta tashi.

 

Sunanan zaune zaman jiran tsammani Daddy ya budo qofar ya shigo dukkansu suka zuba masa ido guri ya samu ya zauna ya hada uban tagumi yana share hawaye, Hajiya ce ta sake fashewa da kuka tace “Nikam naga ta kaina ni Zulaihatu ya mutu ko Alh shikenan Hameed ya mutu….” Dakatar da ita yayi ta hanyar girgiza mata kai yace “bai mutu ba amma yana tsakanin mutuwa da rayuwa Zulaiha Hameed yana fama da heart attack wanda zai iya zamowa sanadin salwantar rayuwarsa yanzu haka ya shiga commar wanda ko babu heart attack zaiyi wahala mutum ya shiga commer ya tashi yaci gaba da rayuwa….”

 

Ya qarashe mgnr cikin kuka tare da tashi ya bude fuskar Umaimah da taketa baccin wahala yayi ajiyar zuciya sannan ya koma ya dauki Shurafah da tunda aka haifeta sai yanzu ya dauketa ya zuba mata ido yanajin son yarinyar na ratsa jinin jikinsa ya rungumeta a jikinsa yana ajiyar zuciya.

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/21, 7:02 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *GIDAN UNCLE*

 

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button