Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 39

Sponsored Links

Da yatsa Ozo dake jikin bangon dakin yasake daga Abba yabugashi da kasa yafesomai wani abu dayake nan kaman hayaki daga bakinshi jikin Abie, wani irin ihu Abie yayi. “wayyo Ozo wlh, wlh, wlh natuba dan Allah azabar nan tamin yawa bazan iya daukar taba, narasa yanda zanyi nahana auren ne mariki nane yahada, saisa narasa yanda zanyi, wayyo Ozo” dawani irin gudu Mami tazo ta tsugunna daidai inda yake kwancen akasa dagashi saidan gajeren wando tarike mai hannu arude takirashi. “Abie” kojinta Abie bayayi sai kuka dayakeyi yana sosa jikinshi dayay rudu rudu kaman anzane shi da bulalan inji, da sauri Mami tasake jijigashi ta kwalamai kira ganin yanda yake abu kaman mahaukaci. “Abie, Abie” afirgice ya kalleta saikuma ya kalli bango dakin ganin Ozo yabace yasa yawani irin rungume Mami ya daura kanshi akan cikinta yana wani irin nishi kaman wanda ake shirin kashewa yagudo, ya ririketa gam yace “help me, Maryama ki taimakamin dan Allah kitaimaka min, Ozo zai kasheni na karya doka akaro nabiyu” sosai gaban Mami kewani irin faduwa all maganganun daya fadi na dawomata kaman yanzu yayisu da sauri tace “me kake nufi dakai kokarin hana auren kakasa marikin kane yahada auren Abie?” da sauri Abie yadago kai ya kalleta suka hada ido yana wani irin nishi yana sauke ajiyan zuciya “kai shiru bakace komiba, waye Ozo? Wani doka ka karya” Mami ta tambaya kaman mai tuhuman shi akan wani abu lumshe ido yayi da sauri dan baimasan lokacin daduk ya faffadi abubuwan nanba, bazai iya jure kallonta ba hakan yasa yatashi ahankali yanadan dingishi jikinshi yay rudu rudu yafada gado yaja bargo tundaga kai har kafa ya lulluba Mami tabishi da kallon tuhuma zaitai magana saikuma tai shiru ta buga tagumi ahankali tana kallon kowani bangare na dakin kaman yauta fara ganin dakin, takai kusan awa daya ahaka kafin ta tashi tai wajen wardrobe tabude wardrobe din ta zaro wani doguwan riga na bacci mai dogon hannu ta zura tadau hula tasaka sanan ta maida sip din tarufe tadau hijabinta tasaka tasa silipas ta fita daga dakin, dakin Aadil ta shiga tana kallonshi har lokacin bacci yake maida kofar tayi tarufe ta shigo abakin gadon ta zauna ta daura hanunta akan kunenshi tana shafa kunen ahankali tana kallonshi maganganun Abie nadawo mata dasuka mugun daure mata akai, abinda ma yafaru gabaki daya ya daure mata kai, ihun me Abie yake, daga ina yake dan ai data shigo daki baya daki bata ganshi ba, tanadai cikin wanka taji kaman an wurgo abu daga sama, menene wai meke faruwa? wani irin ajiyan zuciya ta sauke kafin ahankali takama hanun Aadil din tarike gam tana kallon fuskanshi da sauri ta share hawayen daya zubomata ahankali tace “Aadil, My Hassan, my boy, i want you to be fine, Aadil ka warke, be fine and help me understand everything kaji, yau is a happy day for you, my not so little Aadil, my not so little yaro, Aadil dina is now a grown-up yaro magidanci mai iyalinshi” lumshe ido tayi da sauri jin hawaye zasu zubo mata da kyar ta iya ta hadiye kukan dan she really wanna be strong for her kids takai kusan 2min ahaka kafin tabude idanun ahankali ta kalli sama ahankali tace “Ya Allah, banda abin dogaro saikai, Ya Allah namika dukkanin al’amurana gareka nasan komi dayake faruwa jarabawa ce agareni kuma inaso inci jarabawan ka agareni, Ya Allah kabama Aadil lafiya Ya Allah ka sanyama auren nan dayayi albarka, Ya Allah ka kulamin kakuma tsaremini yarana aduk inda suke, Ya Allah ka tsaremin Aabid kadawo min dashi lpy Ya Allah kabama dan uwanshi lpy” ahankali tace Ameen kafin ta mike tabude bayinsu ta shiga ta dauro alwala tafito ta shimfida dadduma tafara salloli, sai wuraren uku da rabi sanan bacci yay gaba da ita, hayaniyan jama’a ne ya farkan da ita da asuba kallon gadon tayi ganin Aadil na bacci yasa ta tashi ta shiga ta dauro alawala tazo wurin gadon ta bubbugamai kafa tana murmushi yanda yay kyau da bacci. “Aadil, Son” ahankali ya turo baki yace “uhm” murmushi tayi sosai dan Aadil ya iya shagwaban banza, kara saukar da murya tayi dan saiya iya cewa shiba yanzu zai tashiba. “tashi my son time for subhi prayer, tashi kabi Baffa kuje masallaci kaga yanzu you are a married man, Hamida is your wife you need to be praying a jam’i” da sauri yabude ido jin Mami takira sunan Hamida, tashi yayi zaune yana mitsittsika ido agajiye yace “where’s my Hamida Mami?” folding hannu Mami tayi akirji tana kallonshi batare data amsashiba, da sauri yakara bude idonshi yana turo mata bakin shagwaba yace “good morning Mami na, where’s my Hamida” murmushi tayi tace “zaka ganta anjima, go brush ka dauro alwala kazo kai salla in the night zaka tafi chan part dinku” make mata kafada yayi yace “i want to shower first my body is itching” da sauri tace “to sarkin wanka, tashi to kaje kayi” tashi yayi ahankali cikin layin bacci yay hanyar bayin Mami tabishi da kallo, ya bude kofan ya shiga bathroom din yarufo sanan tai wajen wardrobe dinshi taciromai white jallabiya ta ijiyemai kan gado itakuma tahau kan dadduka tafara salla, yadan dade kafin yafito sanye da bathrobe blue hanunshi da dan karamin towel fari yana goge fuskarshi sai kamshi yakeyi, tsayawa yayi yana kallon kan gadon wurin Aabid sosai yake wani irin kewanshi, idar da sallan Mami tayi tace “get dress kazo katafi mosque bari naje naduba babanku” tabude kofa tafita ahankali yadau man yashafa sanan yacire bathrobe din ya shirya tsaf cikin jallabiyan dayamai kyau sosai ya cikashi dam yasa takalmin shi sai wani irin hadadden kamshi yake, zama yasake yi akan gadon yana kallon bangaren Aabid, ahankali yadau wayarshi daya gani kan side drawer yadanna yana turo baki yay dailing number Aabid din dayake fushi dashi sosai dan hakanan yaji yana missing dinshi ringing daya Aabid dake kwance akan gado Vanessa a gefenshi tana bacci, yana rike da wayarshi yana kallo yana tunanin dan uwan nashi wayar tai ringing yaga sunan Aadil.

Picking call din yayi yakai wuyan kunenshi kirjinshi namai wani irin ciwo murya chan kasa yace “hello” jin muryanshi yasa Aadil yakasa daurewa yasakin mai kuka ahankali yana goge ido batare dayace komiba, da sauri Aabid yature hanun Vanessa dake jikinshi yatashi ya zauna shikan shi baisan irin son dayake ma Aadil ba saisa yakasa yafema kanshi akan mugun dukan dayamai saisa kuma yabar gidan dan inhar akai auren agabanshi baisan mezai aikata ba, lumshe ido yayi yanajin kukan har ranshi yace “rascal” yakira sunan asanyaye kaman bashiba, makemai kafada Aadil yayi yana kuka batare dayace komiba, ahankali Aabid yace “I’ve tried many times nacema sorry but kanata fushi dani inka ganni guduna kakeyi, kakimin magana, ka tsaneni, kanata zuciya dani why are you calling me now kanamin kuka kana tadamin da hankali so kake ciwon zuciya yakamani namutu?” yay maganan yana dafa kirjinshi dakemai zafi sosai, da sauri Aadil ya girgiza kai cikin kuka yace “sorry” lumshe ido Aabid yayi kaman zaiyi kuka yace “am sorry too twin Bro, I’ve hurt you, am such a bad brother, am sorry Aadil, am so so so soo sorry” yay maganan while his tone was breaking kaman zaiyi kuka, da sauri Aadil ya share idonshi yace “are you crying?” girgiza mai kai yayo ya share hawayen daya zubomai da sauri yace “a’a” duk sukai shiru Aadil yanajin wani iri kaman something is wrong with Aabid, ahankali yace “are you fine?” gyadamai kai yayi ya gyara muryanshi trying to sound fine and normal yace “yes, where is your wife?” kaman zaiyi kuka yace “i don’t know” gyadakai Aabid yayi yanajin wani iri sosai, ahankali Aadil yace “i miss you, you are not a bad brother, you are very good and I love you so much Bid, yaushe zaka dawo?” murmushi yayi hawaye ya gangaro mai daga ido, murya chan kasa yace “soon, don’t worry i will buy something for you kaji, promise one thing” da sauri yay murmushi yace “what?” murya chan kasa ya runtse ido yace “take care of yourself and Hamida sosai, don’t make her cry okay” washe baki yayi yay fari da ido yace “okay, i promise i will take care of Hamida my wife” murmushi yayi mai ciwo yace “je dakin Baffa kutafi masallaci is time for salat nima zantafi ne” da sauri yace “ok bye” bye yace yakatse wayan yatashi da sauri ya shiga bayi yana goge hawaye ya sakin ma kanshi shower.

 

Related Articles

Tashi Aadil yayi yana murmushi sosai yanajin dadin maganan dayayi da Aabid yafito daga dakin daidai Mami da Baffa sun fito Baffa yakama hanunshi suka tafi masallaci.
Already Big Mum nawajen masu girkin da aka dauko tana gayamusu mezasuyi Mami kuma ta wuce dakinta da sallama ta shiga dakin ganin babu Abie akan gado yasa tai shiru tai tunanin hala yana masallaci ne hakan yasa ta shimfida dadduma tai salla.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button