Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 11

Sponsored Links

11…
Bude marfin mota yayi yafita ko kulle kofan baiyiba yawuce wajen shagon da sauri kaman zai fadi yakarasa wajen daidai tagama goya Miemie abayanta, dan jakanta ta dauka daga kan table din wajen ta rataya akafada sanan ta juyo, mutum tagani agaban ta ya tsaya chak yay folding hannu akirji yanawani irin kallonta, wani irin mugun tsoro yabata daga juyawa tadau jaka saiga mutum abayanta kaman aljani ta ina yafito. Addu’a tafara azuciyar ta kafin tayi gefenshi sadaf sadaf zata wuce yace “My Eesha” ta gefenshi take kokarin rabawa ta wuce kai tsaye yakara tare ta yana sake kallon fuskar ta yace “My Eesha?” ahankali yarinyar ta kalli gefenta da bayanta dan kara tantance dawa yake magana “Eesha yimin magana, talk to me mesa kika gudu kikabarni eh” matsawa baya tafara yi dan yanzu tafara tabbatar da aljanine wanan dan jibi uban gashin kanshi wanda yafi na Miemie yawa, gabaki daya jikintane yafara bari takoma baya ganin kaman zai sata ajikin shine, hanunta ya kama ya rike gam adan rude, cike da murna, da murmushi yace “My Eesha am soo happy” yakara kamo dayan hanun nata ya rike arude yace “wlh is real, kece fa my Eesha maisa kika tafi kika barni for more than a year eh” da karfi ta fizge hannayenta bakinta har rawa yake tace “stop touching me, kai waye kaganni kawai kafara tabani” share kwallan daya gangaro mata tayi tace “niba Eesha bane” tajuya da sauri zata bar wajen dan idan takara minti biyu da mutumin nan wlh zata iyayin fitsari ajiki, hanunta ya kama ya fizgota saida ta bugu dashi yana mata wani irin kallo yace “is you, karya kike, kece, Aisha nane ke” ya nuna fuskar ta, kokarin fizge kanta take ganin yaki sakinta yana kallon ta kaman zai cinyeta yasa tafara waige waige, mai shagon nan takira da muryan kuka tace “Mallam dan Allah zoka rabani da bawon Allahn nan, wlh, wlh niban sanshi ba, dan Allah kataimake ni” takarashe maganan tana sheshekan kuka, fitowa mai shagon yayi ya kalli Khaleel da hankalinshi nakan yarinyar daya rike gam yace “Yallabai lpy dan Allah maike faruwa ne” kaman zai hadiye ta da kallo yasake rirrike shoulder dinta yana kallon fuskarta ko kyaftawa ba yayi batare dayama bi takan mai shagon ba yace “My Eesha plz come with me, zomuje gida, su Ammi sunyi kewanki sosai, please karki sake barina kinji” yakarashe maganan gwanin ban tausayi, ahankali taji fitsari na gangara yanabin cinyarta tunda take bata taba tsorata da firgita irin nayau ba sosai kuka keson ya subuce mata,, ahankali ta kalli fuskar mai shagon tace “wayyo Allah na, Mallam na shiga uku wlh ni bansan Shiba, dan Allah karabani dashi, na shiga uku… ” “stop saying bakisanni ba it hurts” wani irin tsawa ya daka mata ya daura hanunshi daya akan kirjinshi jin wani irin zafi, hakan yasa ta fashe da kuka tsabagen firgita yasa ta mika hannu tana kokarin kamo rigar Mallam mai shago daya tsaya yana kallon ikon Allah, mutum daizai rirrikeka haka tabbas yasankane to ita ya akayi take cewa bata sanshi ba. Bayason ya shiga case din dan daga ganin motar Yaron yasan dan masu kudine shagon nan nashi dashi yake ciyar da Mata yen shi da yayan shi, ganin anzo siyan abu yasa yakoma cikin shago, sosai tafashe da kuka tace “Mallam dan Allah kadawo karka banni dashi” “My Eesha” yakira sunanta, ahankali yace “muje gida” hanunta yakama yanaja ihu tafarayi da karfi ta tace “Wayyo Allah na shiga uku, dan Allah ka sakeni, Wayyo Allah nabani” ganin yakai ta gaban wani mota yana shirin budewa yasa tai dabara ta take kafarshi hakan yasa yasaki da sauri sabida hill din yamai zafi akafa sosai, da gudu ta arce hakan yasa yabita da gudu shima yace “no my Eesha don’t leave me again, dan Allah come back” sosai take gudu ga Miemie abayanta tana kuka, yana binta.
[6/9, 8:14 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button