Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 13

Sponsored Links

Khalil dake zaune ya miƙe da sauri ya ƙarasa kusa da Majeederh yana riƙe hannunta kamar wani zai kwaceta ya ce “Bari muje” Mami ta ce “Haba Khalil kamar ana korar ku? Ko abinci baku ci ba” Aaliyyah ta ce “To kabar Anti Jeederh kai kaje ko Yaya Khalil?” Fuskarsa ɗaure ba alamun wasa Majeederh dake kallon Abbu wanda ya tsorawa hannunsu idanu dake sarƙafe dana juna sai kunya ta kamata, gashi Khalil yaƙi sakinta “We’re full” Ya ce “Tafiya zaku yi yanzu?” Shortly ya ce “Eh” Daga bakin ƙofa aka ce “You can’t run from your shadow” Uncle Isma’il ya faɗa yana shigowa Anty na biye dashi da Jawaad da Sona, sai Uncle Bello da Maman Alpha Du’a Sahar Widad Yaya Bilkisu Innati da sandanta, Mami ta dinga murmushi ta ce “Lale-lale maraba da manyan baƙi” Aaliyyah ta ƙarasa wajan su Widad tana musu tsiya akan zancan da suke a group na WhatsApp na Manyan mata dana khan family duk suka zauna Latifa Omar da tunda ta shigo bata samu damar yin magana da Majeederh ba ta gaishe su Maman Alpha ta ce “Subuhanallah! Latifa mene wannan a fuskarki?” Ta ɗan yi yaƙe da kunya ta ce mijinta ya daketa ta ce “Wlh tsautsayi ne” Suka haɗa baki wajan faɗin “Allah ya tsare” Mami ta ce “Ya mutanen gidan? Da jikin baban naki?” Ta ce “Yana asibiti ai nan Murtala cikin emergency amma an kusa mai da shi I.C.U” Mami ta ce “Allah ya sauwaƙe zan saka driver ya kaini in sha Allah” Uncle Isma’il ya ce “Assha shi Malam Umaru ne ba lafiya? To Ubangiji ya sauƙaƙa yasa kaffara ne” Maman Alpha ta ce “Amin, sai ga Shari’a ta haɗani da mijinki? Na yaba da ƙwazan shi” Latifa Omar murmushi take hankalinta na kan batun auren shi, tana jin Majeederh ta dawo tazo jin wanne ƙauye take da kuma yadda za taga idanu ya faɗa ya yi zuru-zuru ta nemi shawara a wajanta sai kuma taga mutane kashi da kashi alamar akwai abun da ke faruwa. Zata juya Mami ta ce “Dawo mana” Ta dubi Khalil dake tsaye har yanzu kamar zai shige cikin Majeederh ya riƙeta sosai kana ganin yadda ya yi mata zaka san duk duniya ita kaɗai yake kallo wacce ta rage masa Maman Alpha ta kalle su da kyau idanunta sai ya dinga mata gizau wani abu sai kawai ta share ta ce “New couples kamar sojoji angama honeymoon ɗin?” Majeederh tayi ƙasa da kanta sai kuma ta zame hannunta Khalil ya yi saurin riƙota daidai kunnenta ya ce “Plz stay with me wife” Abbu ya ɗauke idanunsa ya ce “Sannunku, sai ku ce family meeting za ayi” Uncle Isma’il ya yi masa banza Uncle Bello ya ce “Ai fa, akwai dalilin zuwan muma duk jira muke an turo invitation without knowing waye so duk zamu jira a nan ne” Abbu ya jinjina kai yaran duk suka gaida Abbu suka juyawa suka gaida Majeederh ta jinjina musu kawai, suka ce “Yaya Khalil evening mun shirya muku surprise” Kamar ba zai ce komai ba sai ya ce “Thanks” Ba wacce ya sani a cikinsu idan ma ya sani shi ba ruwan shi da kowa Majeederh kunya ta hanata gaida su Uncle’s da matan su, Anty daman ko inda Majeederh take bata kalla ba, Innati daman idan tayi magana to abu ya girgizata ne ainun. Suna nan zaune Khalil na tsaye riƙe da matarsa suka ji sabbin jiniya ta ko’ina kamar gwamna ko shugaban ƙasa yazo shigewa Mami ta ce “Wai meke faruwa a kano ne?” Yaya Bilkisu ta ce “Mu duka bamu sani ba Asabe, amma al’amarin ya tsananta na fara tsoro ba shiga ba fita nima nayi mamakin yadda muka samu hanya, amma lungu da saƙo sojoji ne masu wasu kalar uniform jibge ko’ina da manya manyan bindigo fuska kamar dare biyu ba kyan gani amma farare da su yawancin baƙaƙen na Naija ne sauran kuma kamar na outside country”

Mami ta ce “To Allah ya jisshemu alheri” suka amsa da “Amin” Wayar Uncle Isma’il tayi ƙara ya ɗaga bai ce komai ba ya miƙe tsaye daidai nan suka sake jiyo tashin wasu jiniyar na musamman, Uncle Isma’il ya fita with shock yake kallon sojojin da suke entrance ɗin gidan Abbu zuwa compound da duk wani part dake gidan har zuwa ƙofar shigowa cikin main parlour, motar dake parke a tsakiyar compound ɗin ita ce abar kallo, unguwar kowa babu masakar tsinke banda motocin gidan Abbu akwai sabbi wajan biyar da suka shigo, kasancewar Uncle Isma’il wayayye ne mai dakakkiyar zuciya shi ne kawai ya hana shi ruɗewa aka buɗewa Chancellor mota ya fito shi da ƴarsa Debeka dake yatsuna fuska tana kaɗa iphone ɗinta last version daga ita ba ko wacce, aka ƙara buɗe wata motar Zizi da Badi suka fito su biyu cikin kaya iri ɗaya duguwar riga ce iya qiwwa mai kyau da tsada an musu saloon sun yi cutted hair ɗin su fuskar su mai kyau dake kyawawa ne, sun saka hill hannunsu riƙe da iphone kowanne, ɗaya motar sojoji da yawa ne suka buɗe Mrs President Denial David ya fito cikin wata black Suit sai Kiristi daga ita sai skirt iya qiwwa riga ƴar ƙarama kai babu gashi ta ƙwalƙwale tas sai ƙyalli yake, Uncle Isma’il ya zare idanu ganin Mrs President Denial David President’s of Germany Innalillahi is he dreaming or what? What is happening? Shugaban ƙasar Jamani a gidan ɗan uwan shi Alhj Abdul’aziz Khan? Cikin gidan Abbu? Ruɗewa ta kasa sanyawa ya tsaya yaga ƴar kamar dake tsakanin shi da Abraham Khalil kenan, Uncle Isma’il ya juya da gudu zuwa cikin gidan ganinsa a hargitse yasa Yaya Bilkisu faɗin “Isma’ila lafiya?” Ya rasa me zai ce don kiɗima da sauri ya juya ya ce “Duk ku miƙe tsaye da zarar an shigo?” Innati ta ce “Wacce tsaiwa mu ba sojoji ba? Kamar a garin gaɓa-gaɓa daga an shigo sai mu miƙe tsaye daman haka ake? Me ya sa da muka shigo mu Audil azizu bai miƙe tsaye ba sbd mune ma raina wayonka ko Isma’ila?” Footsteps da suka ji na mutane da yawa yasa Uncle Isma’il yin zuru tsoro duk ya gama cinsa ko Abbu ne ya yi laifi? A irin tafiye-tafiye da yake na ƙasar waje? Banda haka me zai kawo shugaban ƙasar Jamani, Chancellor ne ya fara shigowa cikin parlourn sai Debeka wacce she’s anger to see Khalil har jinya tayi hospital kamar ta mutu wanda shi ya ƙara ɗagawa Dad hankali, basu gama mamakin ganin Chancellor ba sai ga President’s of Germany ya shigo da matarsa Kiristi ba umarnin Uncle Isma’il ne ya sanya suka miƙe ba, tsananin shock da mamaki ya sanya gabaɗaya suka miƙe tsaye banda Innati wacce take kallon kowa ɗaiɗai bakin Uncle I na rawa ya ce “Wlcm Sir, wlcm wclm” Ya rasa mema zai ce, ya nemi saman kujera ya zauna first lady kusa da shi, Khalil dake tsaye ya ƙara riƙe hannun Majeederh da kyau idanunsa jajur a jikinsa ya ke jin kallon da Dad ɗin nasa ke masa, Uncle Bello dake tsaye ya ce “Wlcm Sir, zuwan bazata fatan lafiya dai?” Da hannu ya nuna su zauna, duk suka zauna banda Latifa Omar wacce murna ta kamata maybe Khalil ya yi laifi za a kama shi zuwa gidan maza Majeederh zata dauwama a gida da auren wani, wajan ya yi shiru kafin su yi magana Zizi da Badi suka shigo a tare suna zuwa idanunsu ya sauka akan Khalil suka buga Uban tsalle da ihu suka nufe shi yana ganin haka ya ɗan saki Majeederh suka rungume shi a tare “We miss you spider” Zizi ta ce “Miss you alot spider” Ya yi musu shiru suka sake shi tare da neman waje suka zauna kana kallon su kaga asalin ajeboters marasa girman kai sai dai akwai jan aji kyau ilimi da hawaye gasu yara sai a lokacin Debeka ta hango Khalil tana shirin tashi Chancellor ya riƙe hannunta, Latifa Omar da Anti mmkin yaran da suka rungume khalil bad boy kawai suke. Chancellor ya yi gyaran murya ya ce “Mun zo ba tare da sani ko yardarku ba, we’re very sorry for that, ni ne Chancellor ga ƴata Debeka” Ya nuna President Dad kenan ya ce “President Denial David, Germany’s president yaran shi uku Zizi da Badi gasu can” Ya nuna Zizi dake danna wayarta hankali kwance sai sister ɗinta da attention ɗinta ke kan su tayi murmushi kawai, Chancellor ya nuna Kiristi matsayin first lady. Cikin turanci Uncle Bello ya ce “Ance yara uku amma biyu muka gani” Dad ya yi murmushi ya ce “Waye Alhj Abdul’aziz?” Abbu ya durƙosa ya ce “See me here Sir” Dad ya jinjina kai ya ce “Sannu akwai wani kangararren ɗa daya dameka, wanda ka cewa ɗan fashi ne mai sace waya,ɓaraho, kidnapper mara gata da galihu ɗan iskan titi ɗan daban Lagos ka gane yaron?” Zufa ta shiga yankowa Abbu all over himself ya kasa cewa komai Dad ya ce “Ka saka akai masa duka a cikin wannan gidan naka, ka fashe masa tsadaddun motoci har biyu wanda ko ni ban taɓa siyan irin su ba wannan” Ya gyara zama da kyau ba tare daya kalli direction ɗin Khalil ba ya nuna shi da yatsa ya ce “Abraham is my biological son, wannan yaron da ka yi wa duk abubuwa nan is my one and only son duk duniya, da aure muka haife shi” Gabaɗaya suka juya suna kallon Khalil wanda ya yi kicin kicin da fuska Latifa Omar ta ce “Sir ba kuma kama sukai da ɗan ka ba? Wannan musulmi ne not Christa” Dad ya zuba mata idanunsa da suke iri ɗaya dana Khalil ya ce “Maybe; With my consent he converted to Islam, Since he was mad at you, I once walked up to you and said that he is my son, ya zaɓi ya ɓoye waye shi fine I don’t have any problem with his life tun farko har yanzu” Dad ya ƙara cewa “I will tell you two things about it, whether you agree or not, tun kafin na zama President ina da arziƙi daidai dani, har kuma na zama shugaban ƙasa, ban taɓa kashewa wancan ko sisi ba, ban taɓa bashi ko ƙwandala ba, ban rayu dashi ba amma ina da tabbacin ba zai sata ba, da kuke ganinsa ya fini arziƙi nesa ba kusa ba, kuɗi na halak idan bai shiga jerin top 5 na masu kuɗin Kano ba to tabbas zai shiga top 10 na masu kuɗin Nigeria bakiɗaya, I knew he didn’t really tell you, since he was young he was not the kind of person who wanted to showed people who he’s and he’s position, and I know he never showed you that he has parents in this world, that’s why you look down on him, Abraham ɗana ne ya je mini akan batun naje a bashi matarsa, to abinda zan faɗa muku shi ne daku bashi matarsa ko a’a is doesn’t matter for me, abu ɗaya na sani idan har yana so na saka hannu a bashi matarsa to sai ya amince da batun auren ƴar uwar shi Debeka, ya auri Musulma sai ya auri Christa” Yana sauke maganar Khalil ya ce “That’s exlty who you are Sir, You always want to ruin my happiness, so I have nothing to do with you and I will never marry the girl” Ya matsa inda Majeederh take tsaye kamar an dasata ya koma bayanta dragging her more closer ya yi wrapping ɗinta zuwa jikinsa ya rungumeta da kyau ya ce “I love my wife, she is the only one I love and I will live with her until my last breath” Idanunsa ya yi wani irin rau rau ya ce “Why Dad? Why Dad? ban tambayi komai wajanka ba i neva asked anything sai _love and care_ nayi nisa da kai da ƙasarka, na rayu da daɗi babu daɗi har na kawo yanzu You want to separate me from my wife, ban da bank’s ɗina daka saka aka rufe mini what exlty wrng wiz you Dad?Me na yi maka? Anya you are the one who gave birth to me?” Hannu Dad ya tafa sai ga wasu sojoji guda biyu sun shigo ya nuna musu Khalil ya ce “Separate them” Khalil ya ƙanƙame Majeederh sosai a jikinsa kunya ta rufeta ruf kanta duk ya gama ɗaurewa. Latifa Omar tuni tunaninta ya tsaya all this year’s Khalil ɗan shugaban ƙasa ne? Why Turzum bai faɗa mata ba? Harta asassa auren shi da Majeederh da nufin ta wulaƙanta ta turata rana ashe inuwa ta turata, jikin Latifa ya ɗauki rawa ta ce “Never” da ƙarfi wanda ya jawo attention ɗin jama’a zuwa ƙanta ta ƙara cewa “How can that be possible? Taya Khalil zai zama ɗan President?” Zizi dake zaune ta ce “Hi dear Stop doubting and bothering yourself, my bro is billionaire the richer young man, spider ake ce miki gizo gizo wanda baya gidan kansa sai na wani” Khalil bai an kara ba ya ji an ce “Shoot his wife idan bai zo nan ba” Jin haka yasa Khalil sakin Majeederh yana kallonta sai kuma da sauri ya ƙarasa wajan Dad ɗin nasa ya tsuguna Uncle Bello ya ce “We agreed that he should take his wife and go” Dad ya ce “No!” Ya amshi gun wajan wani ya ɗora akan Khalil ya ce “Oh your name?” Ya haɗe fuska ya ce “Ibrahim” Dad ya ce “Ibrahim wa?” Ya yi shiru ya ce “I’ll shoot you” Nan ma ya yi shiru Dad ya kama kunnen Khalil ya riƙe yana murɗawa ya ce “Ibrahim Jee” Gabaɗaya suka kalli Majeederh Abbu dai kallon komai yake kamar zautacce Dad ya saka ƙasan bindigar ya daki lap ɗin Khalil ya ranƙwafa, Majeederh tayi saurin runtse Idanunta zuciyarta na bugawa da ƙarfi duk yadda takai ga riƙe ƙanta sai da ƙafafuwanta suka fara rawa, Dad ya ce “Uhm” Khalil ya ce “Ibrahimul-khalil Denial David” Dad ya sake shi yana yin baya ya ɗauki ƙafarsa ɗaya ya ɗora a shoulder ɗin Khalil ya ce “You’re still my son sweetheart, no one can replace your space, da kake ta ihun kana son matarka, matar taka bata son ka, baban matar baya son ka, few daga family ke son ka” Abbu ya ce “Na amince da ya ɗauki matarsa” Dad ya ce “Matsayinka na wa?” Abbu ya ce “Uba, mahaifi!” Wani irin murmushin ka rainawa kanka hankali Dad ɗin Khalil ya yi kafin ya ce “Bayan taka Majeederhn ta zama matacciyya?” Abbu ya yi shiru yana son tuna sanda ya ce haka “Idan kana so mu yarda kai ne mahaifinta ka tara ƴan jarida both redio da t.v ka gyara maganarka na wanketa daga zargin al’umma, kai kuma khalil matarka ta tabbatar mini tana son ka, ni da kai na zan turo private jet ya ɗauke ku zuwa Germany ku rayu a can, sannan ka amince da batun auren Debeka zan nuna maka babu wani ɗa a duniya da zai fika gata” Anty ta zare ido jin ance Germany Latifa tayi zuru sai kuma ta ce “Ai kam Majeederh bata son shi, domin akwai wanda take so aka hanata shi yasa bata yi masa ko biyayya ba is better a raba auren ka bashi Debeka ita kuma….,” Bata ƙarasa maganar ba taji saukar blet ta ko’ina a jikinta ta shiga ihu da kururuwa aka rasa mai ƙarfin ƙwatar Latifa a hannun khalil dukanta yake kamar jaka duk wanda ya yi attempting hana shi haɗawa yake da shi, ta faɗo ƙasa sai ga fitsarin wahala yana gudu ya saka ƙafa ya take hannunta ji kake ƙass hannun ya yi ƙara “I’ll kill you” Khalil ya faɗa yana ƙwatar bindiga tare da saitawa zai harbe Latifa Omar da gaske domin babu abinda ya yi masa zafi cikin sauri Majeederh ta shiga tsakiya ya saka hannu ya ɗauketa cak zuwa gefe Latifa banda tusar wahala ba abinda take tuni Uncle Isma’il ya shiga kiran Barrister Aliyu ya zo ya ɗauke matarsa tun kafin a kasheta su shiga uku, Khalil ya ƙara saita bindigar zai harba cikin sauri Majeederh ta ƙara sa ta rungume shi a jikinta da kyau ta saka hannunta tsakiyar kansa tana hargitsa sumarsa a hankali daidai kunnensa ta ce “What is this? Meye haka bayan bani na ce ka sakeni ba?” Ya yi shiru a hankali ta sake zura yatsun hannunta cikin sumar shi tana shafawa ta ce “You can’t run from your shadow” Ya cillar da bindigar ya rungumeta sosai yana sauke numfashi daidai nan kuma kwalba ta faɗo daga jakar Anty tare da wata laya wacce ƴar Du’a ta jawo kwalbar ta fashe wani baƙin hayaƙi ya shiga fita daga ciki daga nan kuma suka ji ihun Abbu ya faɗi a sume Uncle Bello daya ɗauki layar da nufin dubawa ya ya yi kan Abbu hankali tashe……[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *#What did i missed?*

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button