Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 77

Sponsored Links

*💖NIHAAD💖*

*77*

A hankali yace “Come…. closer” Ta kafesa da manyan idanuwanta tana kallonsa babu ko kiftawa, ya daga kafada yace “Ohk then” Yana fadin haka ya juya mata baya ya kwanta, murmurshi tayi ta karasa kusa da shi a hankali ta daura kanta a bayansa cikin sanyin murya tace “Ina jin ka” Juyowa yayi ya jawota jikinsa yayi pecking lips dinta yana kallonta da kyau yace “What did u want to know?” Tace “Ina son sanin menene alaqarka da Habibu, da kuma abinda ya kawoka gidanmu” Yana shafa dogon gashinta a hankali yace “Only that?” Ta gyada masa kai, yace “Ohk…. Bayan na bar gidanmu Mami ta so in tafi Uk inyi zamana a can, but i refused saboda bana son rayuwan turai, i then decided to come to kano, i love kano so much but occasionally muke zuwa can, so ban taɓa rayuwa a garin ba…. i have a friend da muka fara karatu tare da shi a India, ɗan nan kano ne, but mind u, we were among the few that were privileged to get scholarship zuwa india to study medicine babu kosisin mu, unfortunately he lost his Mum halfway muna cikin karatun, wanda hakan yayi affecting performance dinsa badly, and sadly he was expelled from the school ya dawo kano, all through our stay together in india ban taɓa nuna masa waye Abbana ba don gaba daya Clique din namu opportunity ne ya kawo mu kasar, so kawai ina rayuwata irin na kowa da kowa da muka taho karatun tare like i am also a nobody….” Nihad dai sai kallonsa take, ya ja dogon hancinta yace “Zaki tsammanin hancinki??” Murmushi tayi tace “Are you teasing me?” Yayi er dariya ya manna nasa dogon hancin da nata yace “Toh naga naki ya fi tsayi” Tace “Ba wani nan naka ya fi” Ya lumshe ido har sannan dogon hancinsa na manne da nata inhaling each other’s breathe, a hankali tace “Ka ci gaba” Ya buda idanuwansa da suka sauya kala murya can kasa yace “Ohk” Ya kwantar da ita saman kirjinsa yana ci gaba da shafa gashinta yace “Still after Mu’azzam left India muka ci gaba da mutunci sosai da shi, though after going back to Nigeria shagon Abbansa ya koma zama a kasuwar kurmi inda Abbansa ke siyar da magunguna irin na gargajiya, bayan na dawo Nigeria na so ya zana jamb ya nemi admission ko a Buk but he told me the zeal to study has left him since his mother’s death, so nayi assisting dinsa in many ways that i can a sannan, har ya bude nasa shago a nan kasuwar shi ma yana siyar da irin abinda Babansa ke siyarwa but in a modernize way, After having issues with my dad wajen Mu’azzam na tafi a kano, then yana hayan wani self contain a wani local unguwa, na dai manta sunan anguwan, a wajensa nake kwana, a nan nake komai na, da safe mu siya abinci mu ci sannan in bi sa zuwa noisy kasuwan mu zauna shagonsa tare, that almost affect me mentally don ban saba ba, amma kuma bana son inje in zauna a hotel even though i can afford it, ina bukatar zama tare da mutane for the sake of my mental health because allegations din da Abbana yayi min is too much for me to bear” Nihad dai sai kallonsa take babu ko kiftawa, yace “Habibu ya kan shigo kasuwan kurmi sosai, don yana da wani aboki me siyar da kayan koli, shagon abokin kuma kusa da na Mu’azzam ne, duk in Habibu ya zo wajen surutunsa ke announcing presence dinsa, a haka dai har muka ɗan fara sabawa da shi don yakan leko shagon mu, and mind u har sannan Mu’azzam bai san wanene mahaifina ba, don ni duk inda zanje bana show off da Dad dina ko dukiyarsa…. i knew Habibu for like 3 months a kasuwar kurmi, har dai muka saba sosai da shi, rana daddaya ne baya shigowa kasuwar, though shi Mu’azzam baya wani kulasa fa, to saboda ni sai ya dade shagon Mu’azzam muna hira, so wataran yake sanar min ai ya kusa komawa kauyensu na Getso gaba daya da zama don uban gidansa ya bude masa shago a can, sai nake tambayansa waye uban gidan nasa, that’s how he started telling me about ur late dad, ya gaya min yayi serving dinsa for almost 10 years now, and he was like ba don ci gaba bane da bazai bar gidan ba don yana jin dadin aiki a gidan, yana jin yan gidan kamar yan uwansa, he told me they are one of the nicest people he have ever met, ya kuma lissafo min workers din cikin gidan da yanda ake basu 3 square meals everyday sannan ga wajen kwana, har cewa yayi idan yana gidan mantawa yake ba gidansu bane….” Ya ɗan kalli Nihad dake kallonsa with full attention, yace “As at then, i was missing the love at home, i so missed my Family, i am not use to zaman kasuwa that is so noisy and polluted, i imagined living with this nice family as a worker also, may be hakan zai rage min kadaici da kewan nawa family din, ban yi kasa a gwiwa ba nace ma Habibu ko zai taimaka min nima in fara tuki a gidan” Nihad ta sauke idonta kasa lokaci daya gaba daya mood dinta ya canxa, Khalil ya lumshe ido ya bude a hankali yace “Habibu refused, saying ya riga da yayi ma wani abokinsa alkawari, kuma ma Alhajin bai ce ya kawo wani ba tukun, bluntly ya nuna bazai kai ni gidan ba, kin san yan kauye da baƙin ciki at times, guess what i did…” Nihad ta daga kai ta kallesa a hankali, yayi murmushi yace “I gave Habibu 200k just to get that Job, cause i need a new family badly…. He was so shocked at first da na basa kudin, amma ko kwana biyu ba ayi ba sai ga Habibu ya zo ya sameni wai yayi ma Alhajin magana yace ya kawo ni, that was how everything started, a hanyar mu ta zuwa gidan yake sanar min ai ce ma Alhajin yayi kauyenmu daya, ga gidansu ga namu, don haka kada inje in canxa baki, I just smiled and said Ohk, kaf yan gidan Habibu bai min maganan kowa ba sai ke, He told me idan ina son in dinga samun extra income in maki biyayya sannan duk inda kika ce in kai ki kawai in kai ki sannan babu ruwana da kalan rayuwarki, komai zan gani in yi shiru ni dai kawai in amshi kudi idan kin ban….” Nihad ta kasa barin su hada ido, shi dai murmushi kawai yake yana kallonta, murya can kasa yace “And you were the second person i met in that house after Aminu….” Nihad taki cewa komai cause she remembered vividly ranan ganinsa tayi zaune a balcony wai yana jiran Abba, tayi ta masifa don me zai zo nan ya zauna maimakon ya zauna kan benci a bakin gate, daga nan kuma ta dinga tunano irin rashin mutuncin da ta dinga yi masa kwando kwando babu ko tsoron height dinsa a gidan har zuwa sanda Abbanta ya daura mata aure da shi, cikin sanyin murya yace “And i found the family i was looking for in that great house, Aminu was more than kind to me tun farkon shigowata gidan, wannan yasa i will make him great in life in sha Allah” Cikin sanyin murya khalil yace “Abba!! Allah ya ji kansa ya gafarta masa, he took me in without second taught, yayi accepting dina lokaci daya, har yayi min tayin zama a gidan if i wish, apart from salaryn da yake bani a ko da yaushe cikin min ihisani yake, he trusted me even with his Atm card a lkcn kuma ko wata hudu ban cika ba a gidan, and Nihal… Duk sanda na ganta ina mata kallon Mimi, she made me feel free staying in that house, she treated me with kindness…. Mumy kuma ina mata kallon mahaifiyata cause she was so nice to me from the start, i still remembered her giving me one of her expensive duvet and many other things, bata taɓa hana kananun yaranta zuwa inda nake ba a gidan, Farooq!!! He ignored i was just a driver and we became friends, idan yana gari tare muke zama da shi baƙin gate mu yi hira wani lokacin har zuwa karfe sha biyun dare, na sha cin abinci a plate daya tare da shi da Aminu, Usman kuma bai taba ganina ya wuce bamu gaisa ba duk da he is an Introvert, Fadil and Sudais made me their new uncle and love me, even Amina bata taɓa wuceni bata gaisheni ba…..” Hawaye ya fara sauka idon Nihad ta kasa ce masa komai, shiru yayi bayan yaji saukan hawayenta, can ya rungumeta a hankali yace “And you made my stay a memorable one wife, i enjoyed almost every bit of ur altitude toward me, it made my stay in the house worth remembering, duk sanda naga kinyi watsi da ni sai inji kawai i need to find a way da zan jawo hankalinki gareni har kiyi min halin, i know i am the cause of most of our fight, wani lokacin kuma ina yin hakan ne just for u to react, sai kuma a hankali na lura u are being used and controlled, Lastly…. ban taɓa kawo kaddaran aure tsakaninmu ba, and i blessed the reason that made me meet u Ummina….” Kuka take a hankali bata ce komai ba, ya rungumeta sosai wani sabon sonta na kara shigarsa, cikin rawan murya tace “I.. i am sorry for everything, i am sorry i treated u badly, i am sorry for all what i have done to you, don Allah kayi hakuri” Whispering into her ears yace “I love you for all what u did to me” Kuka kawai take tana ganin kamar ba haka bane a zuciyarsa, may be he is only trying to calm her down, amma tasan bazai taɓa manta abubuwan da tayi masa a gidansu ba. Sai bayan isha’i suka sauka garin Abuja, tun kan su iso dama Drivern Mami ke jiransu a airport, Nihad bata san if she is happy coming back to Abuja ba or she isn’t, ita dai gata nan gata nan ne kawai, a haka dai har suka iso gidan Janar, Mami ta ji dadi sosai ganin yanda tayi move on bayan rasuwan mahaifin nata don har ta marmaro, nan ko bata san handwork din ɗan ta bane, har parlon Janar suka tafi gaishesa don yana gidan, Janar ya tambayeta su Mumy da Inna, Nihad tace “Suna nan lafiya” Basu wani jima parlonsa ba suka koma bangaren Mami, abinci iri iri Mami ta sa aka ajiye masu a parlon nata kafin su dawo, sai da suka yi sallah sannan Nihad ta fara zuba masa abincin don su biyu ne kadai a parlon, Mimi da Noor sun koma dakinsu, ya sauko ya zauna kasa yana kallonta ta ajiye masa abincin a gabansa, ya girgiza kai yace “Ae tare za mu ci, ba sai kin zuba wani ba” Ta zaro ido tace “Aa ni bazan iya ba….” Yace “Toh return the food inside the warmer nima bazan ci ba” Murmushi tayi murya can kasa tace “Mami fa zata iya shigowa yanzu” Yace “Ita ma zuwa tayi ta ci abinci tare da mijinta” er dariya Nihad tayi bata dai ce masa komai ba ta dau wani spoon din ta fara cin abincin a hankali, yayi murmushi ya dau nasa cokalin ya fara ci, may be don suna ci from the same plate ne yasa suka ci da yawa barin ita, bayan sun gama cin abincin Nihad ta tafi kai sauran abincin kitchen Mami ta shigo parlon, ta zauna tana kallon Khalil tace “Hope the family are doing better now” Khalil yace “Alhamdulillah” Mami tace “To maa sha Allah, Allah ya kara masu hakuri da dangana” Yace “Ameen” He was expecting Mami zata ce su tafi gidansu duk da yasan dare yayi amma bata ce haka ba, sai ma wani hiran na daban da ta kawo masa, Nihad dakin Mimi kawai ta tafi don ta hadu da Mami a hanya sanda zata kitchen. Washegari da safe Khalil na zaune parlon Abbansa ya je gaishesa, Janar yace “So sun shirya maka sanda zaka tafi can Yemen din kenan?” Khalil ya daga kai ya kalli Abbansa don nobody is even saying anything to him about the wedding anymore, kuma ba wai basa waya da Nadeeyah bane don har kusan karfe sha daya jiya yana waya da ita, a jiya da suka dawo ma ya zata Mami zata yi masa magana don sun ɗan yi hira, amma har yayi mata sai da safe ya tafi dakinsa bata ce masa komai game da bikin ba, Janar yace “Tunanin me kake?” Khalil ya sauke idonsa yace “Abba na zata tare za mu je can din ai” Janar yace “No, of course no, sai dai representative dina but my schedules are tight” A hankali Khalil yace “Ohk sir” Janar yace “But let me ask you, Ibrahim kana ganin zaka iya adalci tsakaninsu kuwa?” Khalil yayi shiru yana kallonsa, Janar yace “I am asking this because, ita dama wannan da zaka aura yanzu choice dinka ce, and i know kuna tare da ita for long, ita kuma wannan matar taka…. aure ne da Mahaifinta ya hada ba kai kace kana so ba” Murya can kasa Khalil yace “Zan iya in sha Allah” Janar yace “Toh Madallah, Allah ya baka ikon hakan, i will talk to ur Uncle sai ku tafi can kasar tare da shi, may be this weekend in sha Allah, sai iyayen nata su sanar masu da zuwan naku” Khalil yace “Toh nagode Abba, Allah ya kai mu” Janar yace “Ameen” Bai jima a parlon ba ya mike ya fita ya tafi bangaren Mami ita dama duk asuba yake shiga gaisheta, Abbansa ne dai sai kusan takwas ko tara yake shiga gaishesa, xaune ya sameta a second parlor dinta tare da Mimi da Nihad, Nihad tayi shiru ganinsa, ya kalli Mami da Mimi dake kallonta, Ya zauna saman kujera, Mimi tayi masa murmushi tace “Ina kwana yayanmu” Yace “Lafiya lau” Nihad ta ɗan kallesa tace “Ina kwana” yace “Lafiya lau” Mami na kallon Nihad tace “Ina jin ki” Sunkuyar da kanta tayi kawai tayi murmurshi, sai kuma ta ɗan saci kallon Khalil amma ta kasa ci gaba da maganan, Mami ta yi murmushin ita ma tace “Toh ku je ku shirya….” Nihad ta mike ta nufi kofa, Mimi tayi dariya ta tashi ta bi bayanta har suka fita parlon, Khalil ya kalli Mami yace “Me take gaya maki?” Mami tace “Ina ruwanka da abinda take gaya min” Ya shafa kansa yace “Ohk then” Mami bata sake ce masa komai ba, shi ma yayi shiru, bayan wani lokaci ya kalleta yace “Mami Abba yace da weekend sai mu tafi can Yemen din, So sai su sanar masu a can din about our coming…” Mami dake ta kallonsa tace “Toh ai can gida zaka je ka samesu ka gaya masu ko?” Ya ɗan buda ido yace “Na zata zaki kira Mom din Nadeeyan ki gaya mata kawai Mami” Mami tace “Aa ka dai je ka gaya masu da kanka ya fi” Yace “Toh” tace “Kayi breakfast ne?” Ya bi flask da warmers dake parlon da kallo, sai kuma ya girgiza kai, Mami tace “Su Mimi ne suka yi yanzu, and it’s still hot” Ya sauko ya zauna saman Carpet yana bude warmers din gaba daya, sai kuma ya debi abinda zai ci, ya hada Lipton, jefi jefi suke magana da Mami har ya gama breakfast din ya mike zai bar parlon sai kuma ya juyo yace “Mami naji kince su shirya ina za su?” Kallonsa kawai Mami take yi, hakan yasa ya juya ya fita daga parlon, Direct dakin Mimi ya tafi ya ganta ita kadai a dakin tana fiddo masu kayan da za su sa da Nihad, ita kuma Nihad na bandaki tana wanka, yana kallon Mimi yace “Ina za ku naji Mami tace ku je ku shirya?” Tace “Nima ban sani ba, amma tare za mu fita da ita” Ya ɗan yi shiru sai kuma yace “Ohk, let me disturb you a little, can u pls make me a cup of coffee ki kai min daki” Tace “Ohk” Daga haka ta nufi kofa ta fita, bandakin ya karasa ya bude, Nihad dake kokarin fitowa daure da towel ta koma bandakin da sauri ta zaro ido tana kallonsa a tsorace imagining ta inda ya bi ya shigo, ita dai tasan ta bar Mimi a dakin to ko fita tayi, shigowa taga yayi ya kulle kofar, ta marairaice masa tace “What is this u are doing, Mimi idan ta shigo fa, don girman Allah ka fita” Yace “Ina za ku?” Ta girgiza kai da sauri tace “Wallahi ban sani ba, Mami ce tace in shirya, don Allah ka fita Mimi kar ta shigo yanzu” Ya nufota zata koma baya yayi saurin kamota ya kwance towel din, ta wani hade rai tace “Ni bana son haka, this isn’t proper plss, dakin Mimi ne fa” Yace “Ohk, me kike ce ma Mami dazu?” Ta turo baki tace “Ni dai nace ka fita don Allah” Yace “Kin yi alkawarin idan na fito za ki shigo dakina ki gaya min?” Da sauri tace “Ehh” Yace “Ohk” light kiss yayi mata ya juya ya fita, tana jin ya kulle kofar dakin alamar ya fita, ta ɗan leka cikin dakin taga Mimi bata nan, ta sauke wani ajiyar zuciya ta fito, ko da Mimi ta dawo dakin ta sameta tana shiryawa, Mimi ta shiga bandakin don yin wanka ita ma, Nihad na gama shiryawa ta fito ta tafi bangaren Mami da sauri don bata manta abinda ta gaya mata jiya da daddare ba…. Mami na dakinta tana shiryawa Khalil ya shigo parlon, Nihad dake zaune parlor ta sunkuyar da kanta, yayi kasa da murya yace “Ni kika yi ma wayo ko?” Boye fuskarta tayi taki ce masa komai, sai ga Mami ta fito rike da makullin motarta yace “Mami zan fita sai na dawo” Mami tace “Alright, mu ma yanxu za mu fita” Yace “Toh Allah ya kiyaye” Daga haka ya juya ya nufi kofa, Nihad ta bi sa da kallo, Mami ta koma dakinta don dauko handbag dinta, Nihad ta mike da sauri ta bi bayansa a second parlor ta gansa har ya bude kofar zai fita, a hankali tace “Ina za ka?” Ya juya ya kalleta yace “Nima ban sani ba” Tayi shiru tana kallonsa daga sama har kasa don ba karamin kyau kayan jikinsa suka yi masa ba, lokaci daya mood dinta ya canza, yace “Ba dai ni kika yi ma wayo ba, zaki shigo hannu ai” Juyawa tayi ta bar wajen da sauri yace “Wait…” Amma tuni har ta koma first parlor, ya shafa kansa yana murmushi, sai kuma ya juya ya fita. Gidansu Nadeeyah ya tafi yana zaune compound din gidan yana jiranta bayan ya kirata a waya, ba a dau lokaci ba sai gata ta fito, ta ja kujera ta zauna tana kallonsa da murmushi fuskarta tace “Sannu Kjay” Yace “Sannu kamar wani mara lafiya” Tace “Ohk, weldone KJay…” Yayi mata murmushi yace “How are you doing” Tace “Alhamdulillah, how is ur wife?” Ya ɗan kalleta, amma sai bai ce mata komai ba, tace “Naji Mum tana cewa za mu je can gidan ma Anjima” Yace “Ohk Mum na ciki?” Tace “Yeah, but tana da bakuwa” Yace “Ohk, we will be going to Yemen on Saturday with my uncle don Abba bashi da lokaci, shine na zo in gaya maki ki gaya ma Mum don ta sanar masu kafin Saturday din” Nadeeyah dai tayi shiru tana kallonsa, yace “Ya kika yi shiru Madam?” Ɗan murmushi tayi tace “Kasan a rayuwa muna namu Allah na nasa ne ko?” Yace “Sure…” Tace “And kasan policy dina a baya da nake yawan cewa i will never marry someone’s else Husband, kuma idan baka manta ba a lokacin muna Uk da kaje kara karatu ni kuma ina year 1 farkon haduwarmu kenan nayi wani saurayi me mata da yaro daya da yake zama a Uk, na kuma so sa but na ki aurensa saboda yana da mata, ka tuna ko?” Ya sauke idonsa bai dai ce komai ba don truly tana yawan fadin haka a baya, har tsokanarsa ta sha yi kan cewar duk ranan da zai mata kishiya sai dai fa ita ya saketa yayi aurensa, Jin yayi shiru Nadeeyah tace “Kayi shiru” ya daga idanuwansa ya kalleta but still bai ce komai ba, murmushi tayi tace “To be sincere Kjay, after i found out u are married na sanar ma da Mum dita ni baxan iya aurenka ba na hakura, my Mum tried persuading me inyi hakuri kada ince haka ko don zumuncin dake tsakaninta da Mami, Mami won’t be happy idan nayi hakan, Few months back ai kaga er uwar Mum dita ta zo daga yemen, she came because of the issue saboda i was serious nace bazan aureka ba ni na hakura, idan ka lura har wayarka ai bana dagawa a sannan cause har zuciyata nasan na hakura da kai, amma Mum dita da sister dinta suka saka ni a gaba for almost a week ana abu daya, har yau kuma Mami bata sani ba, almost all my maternal relatives sai da suka min magana a kan issue din nan, and at last babu yanda zanyi haka na janye kudurina na cewa na fasa auren, but still idan ka lura har yau ni da kai ba kamar yanda muke a da bane, kuma kai ma ka sha fadan haka….” Yayi kasa da murya yace “Kiyi hakuri Nadeeyah, Allah ne ya tsara mana haka” Tayi murmushi tace “Haka ne, daga karshe ya kuma tsara babu aure dama tsakanina da kai Kjay” Da mamaki yake kallonta, tace “Yeah, we were not destined to live as husband and wife tun daga farko….” Yace “Why are you saying this Nadeeyah?” Tace “I am saying this because Nihad is my second cousin, kuma ni bazan iya auren mijin cousin dita ba duk da ba haramci a auren namu amma bazan iya ba, Beside even if i should ignore the fact that Nihad is my Second Cousin, in dai da mutunci Mum dita bazata bari in aureka ba ko don saboda Cousin dinta warce ita ce Mahaifiyar Nihad” Cike da confusion Khalil ke kallonta don shi har a lokacin babu wanda ya gaya masa meke faruwa, Yace “Ban gane ba Nadeeyah, u are getting me confuse, what is happening” Ta mike tace “Ina zuwa…” Yace “Wait plss ki fahimtar da ni Nadeeyah” Tace “I am coming” Ya bi ta da kallon mamaki har ta shiga cikin gidan, ba a dau lokaci ba sai ga mai aikin gidan ta fito ta karaso har inda yake ta sanar masa ance ya shigo ciki, tashi yayi ya bi ta zuwa cikin gidan, nan ya tarar da Hajiya Safeenah a parlor, ya zauna ya gaisheta ta amsa da fara’a tana tambayarsa ya ya baro mutanen kano, yace “Alhamdulillah” Tace “Naje har kanon amma bamu hadu ba har na taho” Da mamaki yace “Wallahi ban sani ba Mum” Tace “Ehh nasan baka sani ba Khalil” Bai sake cewa komai ba yayi shiru yana jiran yaji kiran me tayi masa, tace “Kana ji na Khalil” Yace “Ina ji Mum” Tace “Kasan komai ya faru a rayuwa mukaddari ne daga Allah ko?” Shi dai yayi shiru yana kallonta, tace “Don haka ina son ka sa a ranka Allah bai kaddara aurenka da Nadeeyah ba” Da mamaki yace “Mum me yasa kika ce haka?” Tayi shiru tana kallonsa, a nutse ta shiga yi masa bayanin duk abinda ya faru da kuma alaqarta da Mahaifiyar Nihad, he was just speechless and at the same time confuse, tace “Duk da aure tsakaninku bai haramta ba amma sai mu yi masu kara, kuma er uwata ce ta kusa ba ta nesa ba, daga kai har Nadeeyah ku yi hakuri, kai ka zauna lafiya da matarka ita kuma Allah ya bata miji na gari, amma bazan iya barin ‘ya ta ta auri mijin Nihad ba albarkacin zumunci, Nayi ma Hajiya Fatima bayanin komai yau kusan sati uku kuma ta gamsu da duk bayanai na ta kuma min uzuri….” Khalil dai tuni ya fada duniyar tunani yana ganin abun kamar a mafarki, jin Mum tayi shiru ya kalleta yaga shi take kallo, A hankali Khalil yace “Amma Mum babu haramci a aurena da Nadeeyah ai” Tace “Kayi hakuri Khalil, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi, Allah ya ma Nadeeyah zabin alkhairi” Sunkuyar da kansa yayi bai ce komai ba yana ganin kamar dole ma Allah ya kamasa bayan jiran nan nasa da Nadeeyah tayi at the end ace bai aureta ba, Mum tace “Bari in je ina da bakuwa khalil” Bai iya yace mata komai ba har ta mike ta bar parlon, ya Jinginar da kansa jikin kujeran parlon, ba a dau lokaci ba Nadeeyah ta shigo parlon tana kallonsa tace “Hope ka gane yanxu??” Yace “Ban gane ba Nadeeyah…. Don ke da Nihad kun kasance Cousins ba wannan yake nufin babu aure tsakaninmu ba ai” Tace “Toh babu, dama kawai iyayena nake kokarin yi ma biyayya kuma i am happy things later turnout this way at last, and i pray it’s just the best for me”

*Thanks for the calls and messages to check on me, i am much better*

 

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button