Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 39

Sponsored Links

39*

 

Koda suka isa gida ɗaukarta yayi kamar jinjira gudun karta wahalar mishi da kanta da babynshi gurin tafiya.

Related Articles

Be direta ko ina ba se kan gadon ɗakinshi,kitchen ya koma ya haɗo musu tea ya soyo musu cheaps da kwai,sannan ya dawo gurinta.

“yaya wallahi naci abinci agun mummy na ƙoshi ni”zahra ta faɗi tana ƙoƙarin zillewa daga kamotan da yayi.

“pls ɗan kaɗan zaki ƙara sabida babynmu kar yunwa ta kamashi,ko kinaso yasamu matsalane?”cewar hammad yana shafa fuskarta.

Cikin ta shafo a hankali sannan ta girgiza masa kai tana murmushi.

“yauwa to maza zo in baki kici ki ƙoshi shima yaci”

ba musu ta sakko ya bata taci shima yaci,ya kwashe kayan,sannan ya haɗa musu ruwan wanka sukayo,suka ɗauro alwala sukai sallah sannan suka bi lafiyar gado.

Sosai Hammad ke ba zahra kulawa da cikin jikinta,ko kaɗan beson abinda ze sameta na ɓacin rai.

Cikin Zahra yanzu wata biyu kenan,tun da aka shaida akwai cikin zahra bata yarda da hammad,duk yadda yaso ta bashi hakkinshi ƙi take tace “mummy tace banda rawar kai,”yayi rarrashin yayi magiyar amma sam taƙi yarda,hakan ne yasa yayi alwashin ɗaukar mataki.

Yau ze dawo daga gun ayki,zahra se hidimar girka masa abinci take,tasa masu ayki sun gyara mata ko ina na gidan.

Tana gama jera abincin a dinning taje tayi wanka ta ɗauro alwala.tazo tayi sallah sannan ta tsantsara kwalliyarta ta ɗaukar hankali.ta ƙace a falo tana jiran dawowarsa.

Hammad ko a gidan mummy ya sauka,yasa surayya ta haɗa masa abinci yaci ya cika cikinsa,sannan ya koma garden ɗin gidan yayi zamansa yanashan iska.

Zahra ganin har kusan tara da rabi na dare be dawo bane yasa hankalinta ya tashi ta fara nemansa a waya,yana ganin kiran nata seya kashe,data dameshi seya kashe wayar gaba ɗaya.sosai yake dariyar shirin nasa dan yasan bazasu wanye lafiya da iya rigimarsa ba.

Se sha ɗaya na dare yabaro gidansu,zuwa gida,lokacin zahra taci kuka har ta godewa Allah,tana zaune turus a tsakar falo.

Bakinshi ɗauke da sallama ya shigo falon,agigice zahra ta miƙe tayi gunshi da gudunta,ta faɗa jikinshi tana kuka.

Sosai ta bashi tausayi,amma sanin da yay zahra zuma ce seda wuta ne yasa ya rabata da jikinshi ya wuce kan kujera ya zauna.

Zahra tsaye tayi kamar gunki, tana kallonshi,shiko ko kallonta bayayi,wayarshi ce ta fara ƙara kamar yadda ya seta alarm ɗin wayar tashi,

Ayko cirota yayi a aljihu ya kara akunne,ya wani lumshe ido ya rage murya yace.

“baby na yana baroki,?”ya ɗanyi shuru sannan yace.

“na iso gida lafiya wlh,sede kewarki gaba ɗaya ta addabeni,ga ɗanɗanon abincinki,da ƙamshin jikinki duk sunbi sun rikitani,gaskiya gobe anan zanyi break fast”ya faɗi yana murmushi dan ya hango wutar kishin dake ci a idanun zahra.

Miƙewa yayi manne da wayar a kunnensa yayi hanyar ɗakinshi yana faɗin “baby kulkin ki yau ya samu kulawa ta musamman wacce be taɓa samuba yanzu ma wanka nakeso inyi in samu inyi sallah in kwanta duk kin taramin gajiya”

Zahra dake tsaye kamar gunki tana sauraron wannan tashin hankali,zuciyarta tafasa take,amma haka ta daure tabi bayanshi,suna shiga ɗakin taji yana faɗin.

“ina zaayi haka ay na bada kuɗi ayomin sex doll kamarki gobe zaa kawomin ta dinga ɗebe min kewarki kan hutuna ya ƙare mu koma tare”

hawaye ne ke bin idon zahra kamar kogi,wato yayanta mata ya fara bi kenan dan ta hanashi kwanciya da ita,

Kashe wayar ƙaryar tashi yayi,ya miƙe ya nufi toilet,a hankali ta taka ta bishi cikin toilet ɗin.

Ruwan wanka ta haɗa masa yana tsaye yana kallonta duk tausayi da shaawarta sun addabeshi ji yake kamar ya kamota ya rungumeta amma seya daure,

Ga mamakinsa se ji yayi tace masa cikin rawar murya”na tsarkin zaka farayi ko ko na sabulun?”tayi tambayar cikin raunin murya.

Sosai yaji kunya ta kamashi amma se ya maze kawai,ya fara cire kayan jikinshi,matsawa tayi ta soma taimaka masa ya cire kayan idonta na kan kulkinta tana so taga alamar ko yayi wani abun amma bata gani ba.

Shiga cikin verb din yayi ya lumshe ido ƙamshin turaren wankan data sa na ratsa masa zuciya,a hankali ya buɗe idonsa,ya saukesu akanta,itama shi take kallo.

“dama ba wankan zakimin ba kika wani biyoni,?”hammad yayi tambayar cikin faɗa faɗa.

A tsorace tace “yi haƙuri yaya ba haka bane,”ta juya da sauri zata bar cikin toilet ɗin riƙe da bakinta da kuka ya taho mata.

“zo nan”ya kirata,

A hankali ta juyo ta dawo gurinshin,be ce mata komai ba hannu ya miƙa mata,ba musu ta kama hannun,yajata zuwa cikin ruwan wankan.

Muje zuwa

Surbajo for life.

“”
[1/9, 8:19 PM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*ku hanzarta ku sayi littafin SHIMFIƊAR AURENA dan maƙurane gurin karatu,shi kaɗaine babu irinsa,karki bari abaki labari,soyayyar da akemin anunawa littafina😊shine nasan ana yina irin over ɗinnan,500 ba tsada*

*Zahra Muhammed Nasir 2084024749 UBA*

*Aturo shaidar biya ta nan 07044600044,banda katin waya ta acct kawai,in baki da acct ki je POS ki turo*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button