Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 26

Sponsored Links

Sunkuyar dakai tayi Abdu yayi saurin cewa “Nop kawai abubuwa ne sukayi yawa auntynmu ashe muna ranki bamuyi tunanin zuwanki yanzu ba munyi tunanin sai kinzo mana Barka…..” Wata dokawa ƙirjinta yayi tace “what kardai har an samu ƙaruwa” murmushi Aneey tayi lkcn da yake cewa da ita kiji da baƙuwarki zanje office” da sauri tace “Prince bafa ka warke ba don Allah kada ka fita….” Numfashinta ne ya dauke saboda jin bakinsa cikin nata ya saketa a hankali yace “Dama kece matsalata kuma kin bani magani nasha sai gaba kuma” binsa tayi da kallo har ya fice daga sashin taja ajiyar zuciya ta zauna suka gaisa da Hasina Hasina ta ware kamar babu komai take bin falon da kallo tace “Wow gdan da nake mafarkin samu My Jinin jiki kin samu wlh ki godewa Allah yana sonki yanzu meye yayi miki saura gashi kin kusa cinye gdan yanzu kina haihuwar cikin nan shikenan kin cinye gdan”

 

Murmushi tayi tace “Yaya kenan wlh banida komi” zaro ido tayi tace “kina me kika sake haka?” Ƙasa tayi da kanta tace “yaya kenan ai abin rabone tunda bani zan bawa kaina ba kinga ai dole na jira abani balle ma yaushe akayi shukar da har zatayi tsiro” ajiyar zuciya tayi ta fara zagaya gdan Hanisa ta nemi guri ta zauna saboda ƙafarta rawa takeyi rashin sabo gashi ta gurzu yau zagaye gdan Hasina tayi sosai itace har ɗakin Aneey harda buɗe wadrobe ganin yanda wardrobe ɗin take shaƙe da kaya wani bakin ciki ya ƙara dasuwa a ranta tace “Hmmm da tuni nice anan fah koda yake lkc tunda nazo bazan bar gdannan ba saidai ita tabarmin gdana dama ita ta cuso kanta”
Ɗakinsa ta shiga ta tsaya tana karewa dakin kallo ga robar drip ɗinnan daya cire gajeren wandonsa bra ɗin Aneey da pant ɗinta ga kuma kayansu duk a yashe a ƙasa wasu hawaye suka zubo mata tayi sauri gogewa kishi ya tokare mata maƙogaro.

Related Articles

 

Buɗe ƙofar da taji anyi ne yasata saurin juyawa suka haɗa idanu da Aneey dake yar duniya ce ta maze tace “Kin samu duniya yarinyar nan wato da ranar ma bazai barki ki huta ba shifa mijin nan naki idan kika sake wlh saiya kwance miki notin tsuliya baya gajiya da sex kamar masifa” haɗe rai Aneey tayi tace “Kizo ki huta” waskewa tayi suka fito suka zauna ma’aikata sukayita hidima a sashin abinci gashinan kala² saida ta zaɓa sannan sukaci Aneey dake a gajiye take suna hirarsu tana tambayarta Mama da Baba Hasina tace “Yo Mama da taso hanani zuwa nifa zuciyata ce taki nutsuwa naji inason zuwa naganki banji daɗin abinda ya faru ba Aneey zuciya ce batada ƙashi wlh sai bayan kin fito hankalina ya tashi maganganunki suka rinƙa dawo min bai kamata ace na biyewa shaiɗan namiji ya shiga tsakaninmu ba kiyi hƙr don Allah wlh daga baya na gane Abdu ba ƙaddarata bace kuma nayi nadamar ƙin tsayawa na fahimci ƴar’uwa me adalci kamarki…..”
Rufe mata baki tayi tace “bantaɓa jin haushinki ba hasali ma kunyar ki nakeji har gobe ina kallon kaina a naci amanarki Yaya banida yanda zanyi da Abdu ne amma wlh ni zuciyata ta kasa karɓar auren nan har yanzu da ace zai yuwu zan iya bar miki shi…..” Saurin rufe mata nata bakin tayi tace “Habadai ai har abada kawai kedai ki zauna ki rayu da mijinki lfy Amma fah gsky kada ki yarda ki bari yayita sukwaneki akwai matsala”

 

Dubanta tayi da sauri tace “Saboda me Yaya?” Murmushi tayi tace “zan fahimtar dake a hankali” bata zafafa ba sukaci gaba da hirarsu har bacci ya ɗauke su tun daga wannan rana da Hasina tazo Aneey ta zamewa Abdu kamar nama abinka da rashin sabo duk saita damu juriyarta ta kasa ɗauke shi shiɗin irin mazan nan ne da basa gajiya da sex a dare sai yayi sau huɗu haka don babu yanda zatayi take jurewa su kwana ba bacci da rana ma ya nema duk bata gaza masa A gefe kuma Hasina na bugun cikinta amma taƙi faɗa mata damuwarta har suka ɗebi wata guda itadai Aneey abin ya fara isarta ganin Hasina batada niyyar tafiya da farko tayi mata mgn sai tace karatu takeson farawa a garin shiyasa tazo take karantar yanayi kullum zasuyi wanka da yamma su fice da Maryam su zaga gari ganin Aneey ta fara nuna mata alamun zata iya cewa tabar mata gida yasata neman Admission ɗin gaske abinka da 9ja kuma tanada abin badawa nan danan ta samu ta fara shirye-shiryen karatunta.

 

Abdu ne ya samu Aneey yake tambayarta yaushe Hasina zata tafi ta dubeshi idonta ya ciko da ruwa tace “nima na matsu ta tafi taƙi yanzu haka ma ta samu Admission anan karatu zata fara a makarantar su Merry Ni bansan waye ya shige mata gaba ba ta samu Admission ɗin” ganin yanda ta damu yasashi kwantar mata da hankali yace “karki wani damu ai kema zakifi jin daɗin zaman kina ganinta zatake rage miki kewar gda” kwantar mata da hankali yayi sosai ya yaudareta suka lula sama ta bakwai, yaɗuwar jinin Marry da Hasina da kuma yanayin ɗabi’arsu da tazo ɗaya shine dalilin da yasa Aneey ta samu sauƙi Hasina ta tattare kayanta ta koma sashin Marry suketa iskancinsu tare babu kwaɓa bare harara ita sai hakan ya zame mata sauƙi ta samu damar kula da mijinta.
Watansu huɗu da aure ta fara rashin lafiya me zafi bata iyacin komai kullum ita kenan bacci likitan gdanne yazo ya dubata yayima Abdu albishir ciki ke gareta yayi farin ciki sosai itama tayi murna abu ɗaya ya fara basu matsala yanzu kwata² bata iya ɗauke buƙatarsa da ya hau kanta saita kama amai, son da ƙaunar daya ɗorawa cikin ne yasashi bai wani damu ba yaci gaba da kula dasu.

 

Yayin da ita kuma Hasina take cikin tashin hankali da samun cikin na ƙanwarta tabbas tana neman wasa da damarta yauma tana zaune a ɗakin Merry ta rafka uban tagumi wayarta tayi ring ta ɗaga ganin number Aneey tayi kamar bazata ɗagaba Marry tace “Sis Matar Bro na kiranki fah” firgigit tayi ta ɗauka tace “Jinin jiki ya jikin?” Kuka taji tanayi tace “ya Salam meye yayi zafi haka?” A gajiye tace “Don Allah kizo inason ganinki” miƙewa tayi ta fita ta nufi sashin ta tarar da ita a kwance a ɗakinta ta zauna tace “meye ya faru?” Cikin kuka tace wai dama haka maza suke?” Da sauri ta dubeta tace “me yayi miki?” Kukanta ta tsayar tace “da baya damuwa amma yanzun ya fara damuwa Jinin jiki na cewa yayi banida wani amfani waishi baiga amfanina ba”……..

 

*Ki tausaya karki fitar mana dashi in kin siya ,Inkin san siya zakiyi don kiyi sharing don Allah karki siya mun hutashsheki,Haƙƙin mallakar marubutanne su kaɗai,Ki tausaya masu plz ,Inkinga wani pages na yawo to na sata ne ki runtse idonki karki karanta ki biyo ki siya*

 

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

*OUM HAIRAN*
[12/16, 2:36 PM] Oum Hairan&Affan: *Wata karuwa*

*Oum Hairan*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button