Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 35

Sponsored Links

Jikin Aneey har wani rawa yakeyi tsabar tashin hankali Mom ta zaunar da ita tace “karki sanya damuwar wannan abin a ranki ki kwantar da hankalinki ki zauna anan da kansa zai nemeki” bata iya cewa komai ba sai jinjina kai da takeyi anan sashin Mother ta zaunar da ita har dare bai nemeta ba itakuma hankalinta na gurinsa da lkcn kwanciya yayi ta kwanta a ɗakin data zauna farkon kawota gdan anan ta zauniyarta kwanaki suka yita tafiya babu bayanin Abdu ko sashin Mother baya shigowa.
Ranar da sukayi sati basa tare ne ya shigo sashin ya tarar da ita a zaune ta ɗago idanunta cikin nasa suna kallon juna sosai ya tako ya matso gabanta ya kama hannunta ta janye tare da sunkuyar dakai ta gaisheshi da girma.
Numfashi ya sauke yace “Kina lfy ya babyna” sunkuyar da kanta tayi idanunta ya ciko da ruwa batakai da yin mgn ba ya wucce yace “ki tashi ki koma gdanki banson shirmen nan naki kinzo kin zauna anan babu ruwanki da lamura na” ciki ya shiga gurin Mother ya jima sannan ya fito bai ko kalleta ba ya fice taja fasali gabaɗaya tun ranar da abin ya faru tsoronsa takeji.

 

Ya lura da hakan shiyasa daya fito baice mata komai ba bata wani bawa mgnrsa muhimmanci ba taci gaba da harkokinta saida yamma sosai sannan Mom tace ta tashi ta shirya ta tafi sashinta gabanta na faɗuwa tayi wanka ta shirya Marry ta rakata sashin nata suka zauna suna ƴar hirarsu Merry nason yi mata tsegumi tanajin tsoron ta kife da ita wannan tasa taja bakinta tayi shiru har isha tayi mata sallama ta tafi sashinta tananan zaune so take ta tashi nauyin jikinta ya hanata har taran dare taji an buɗe ƙofar an shigo ana dariya jin Muryar mace yasata ɗagowa da sauri ta miƙe gabanta yabada wani rass ganin Hasina taci wasu uban riga da wando taci attachment da farcen kanti fuskarnan tayi fayau ansha mai.
Saurin fuskewa Abdu yayi ya zauna a inda ta tashi yace “Na manta ban sanar dake ba ta dawo nan da zama inda taje ta kama haya hankalina bai kwanta dashi ba garanan kya rinƙa jin motsinta” kafeshi tayi da manyan idanunta shima itan yake kallo ta buɗe baki tace “Amma Prince…..” Ɗaga mata hannu yayi yace “Dakata Malama banson jayayya akan abinda na tsara gdannan dai nawa ne saboda haka hakan shine abinda nakeso idan kinga bazaki iyaba ki kama gabanki Ni banyi miki dole ba”
Jin ya fusata ya fara sababi yasata buɗe bakinta jikinta a mace tace “kayi hƙr yanda kakeso haka za’ayi” juyawa tayi ta shige ɗakinta Hasina ta rakata da wani dogon tsaki daya caki zuciyar Aneey amma bata juyoba saboda ranta a matuƙar ɓace yake batason ta gane shiyasa ta zaɓi barin falon.

Related Articles

 

Ganin tabar musu falon yasa Hassy isa gareshi ta zauna a gefensa tare da ɗora kanta a kafaɗarsa tace “Babe matarka tanada kishi bansan meye yasa bata ƙaunar taganni tare dakai ba….” Kissing kuncinta yayi yace “karki wani damu babu abin fah data isa tasa ko ta hana kawai zata zauna ne saboda cikin dake jikinta amma tana haihuwa zata barmiki Ni muyi aure muci gaba da rayuwarmu banason wannan rayuwar da mukeyi” fari tayi masa da idonta tace.
“Na ko yi maka tanadin farin ciki me yawan gaske” miƙewa yayi ya nufi ɗakin Aneey ya isheta kwance a kan gadonta tanata sharar hawaye ji yayi jikinsa yayi sanyi ya zauna kusa da ita yace “nifa ba wani abu ne yasa na dawo miki da ƴar’uwarki nan ba sai don banasonki cikin kaɗaici tunda bakiso bari zan kama mata gda” miƙewa tayi tace “kabarta tunda hakan yayi maka” murmushi yayi ya kwanta kusa da ita ya janyota ta ɗora kanta a jikinsa tanajin wata nutsuwa na saukar mata ƙaunar mijinta na ratsa ruhinta da wannan ya kawar mata da duk wata damuwa da take ciki wannan dare ya nuna mata ƙauna matuƙa kamar babu wani abu dake faruwa da safe ma abin gwanin gwasama.

 

Zamanta tayi a ƙaramin falonsu bata fito ba sai rana bayan ya fita koda ta fito Hadiman gdan har sun gama gyaranshi ta zauna tana danna wayarta Hassy ta fito shirye cikin shigarta ta banza ta kalli Aneey ta watsar itanma batayi mata mgn ba taja tsaki ta fice daga gdan mamaki.
Ya cika Aneey ita da gdan mijinta amma itace baason gani
Murmushi tayi ta miƙa ta koma ciki yinin ranar bata ƙara fitowa ba sai dare ta fito sanye da rigar bacci doguwa me yauƙi milk tayi mata kyau sosai ta tsaya sake da baki ganin Hassy zaune a falon tana busa shisher zuciyar Aneey tayi baƙi ta dubeta tace Mgn ta gaskiya Hassy bazan ɗauki wannan bushe²n a da’irata ba wannan gdan mijina ne inada ikon sawa ko hanawa kamar yanda yakejin ikon ya isa nice mataimakiyarsa sai dani ne cikar ikonsa zai cika saboda haka ki bari banaso”
Kallon Abdul-ahad dake shigowa Hassy tayi ya dubesu dukkansu Ya tsayar da idanunsa akan Aneey yace “Ya akayi ne Wyf” numfashi ta sauke tace “ba komai bane kawai nace mata banason tanamin bushe² a gdana idan zatayi ta rinƙayi a waje tunda haka ta zaɓawa kanta” tana faɗin haka ta juya ta shiga kitchen Hassy ta saki baki tana kallonsu yaja fasali yace “toke tunda matar gdan bataso ki daina nima banaso”

 

Yana mgnr yanabin bayan matarsa Hassy ta haɗiyi wani takaici taja ƙwafa wato da gaske asirinta bazaiyi dogon zango a gdannan ba ta shiga tsakaninsu cikin sati biyu har komai ya rushe dole ta sake shiri.
Miƙewa tayi ta shiga ɗakin da aka bata ta kwanta zuciyarta na saƙa mata irin matakin daya kamata ta ɗauka akansu bata fatan ta barsu su huta da wannan tunanin bacci ya ɗauke ta ba sallah ba salati sai mugun tanadi.
Shiga kitchen ɗin yayi ya tsaya a bayanta ya dora hannunsa a cikinta yayi kasaƙe yanajin yanda cikin yake motsawa yayi murmushi yana ƙaunar cikin nan ji yake kamar ya janyo lkcn haihuwarsa ya matsu ya gansa a hannunsa, janye hannunsa tayi ta juyo ta sumbaci ƙirjinsa ta sanya hannunta tana shafawa ya sauke ajiyar zuciya ya ɗora bakinsa a saman kanta tare da tura hancinsa cikin sumarta yace “i….inasonki Wyf meyesa kwana biyu nakejin damuwa game dakene?” Murmushi tayi tace “ni banajin komai sai soyayyar mijina”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button