Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 28

Sponsored Links

Arewabooks;hafsatrano

Page 28

**** Shigewa toilet din tayi tana jin ta wani irin sakayau kamar an sauya ta, sai da ta tsaya tana fara kare kallon toilet din sanyayyan kamshin body wash dinsa ya mamaye toilet din ga wani kamshi da bata ma san wanne iri ba. Ko ina tsaftsaf a shirye a gyara kamar akwai mace yar gayu da take rayuwa a wajen. Shi dai koman sa unique ne kaman yadda yake unique din da wata irin charisma. Cikin yanayi me dadi tayi wankan ta dauki towel daya cikin drawer da aka jera su ta tsane jikinta sannan ta fito a hankali kamar me sanda bayan ta leko kanta taga baya dakin. A gurguje ta shirya ta zura doguwar rigar ta dauko madaidaicin Hijab ta saka sannan ta isa wajen sallar sake dake kuryar dakin dauke da lallausar darduma ta kabbara sallar isha da akayi dazu. Tana sallar ya shigo sai ya sake fita ya hado mata snack da milkshake ya kawo dakin.
Tana addua bayan ta idar ya karaso wajen fuskar sa dauke da wani irin tsadadden murmushi me tafiya da duk wanda akayi ma shi. Cikin sauri tayi kasa da idon ta daga kallon sa dan yana so ya saka mata wani irin kaifaffan miki a idon nata da ba zata iya jurewa ba.

“Get up.” Ya mika mata hannu alamar ta kama, nokewa tayi ta mike a hankali tayi gaba kamar zata fice. Riko ta yayi ya dawo da ita baya sannan ya zare mata Hijab din jikinta yana girgiza mata kai.

“I don’t like this please.”

“Zan tafi dakin chan.”

“Um um, anan zaki zauna inaso muyi magana, but before then… Zauna.”

Ya kama kafadarta ya zaunar da ita a rug din dake gaban gadon nasa.

“Kan ya daina?” Ya kai hannun sa goshin ta ya taba.

“Um. Ya daina.”

“Masha Allah, yanzu kici wannan please, kinga headache din hadda yunwa da kukan da kikayi tayi, idan kika ci zaki sake jin dadin jikin ki.”

“Me yasa kake mun kirki?”

Ta tambaya ganin yadda be nuna mata ko a fuska kyama ko wani abu da zai nuna mata akwai wata manufa da yasa ya aureta ba. A zaton ta kiyayyar sa gareta yasa aka koreta sai gashi taga akasin hakan, daga jiya zuwa yau ta kasa gane takamaimai kalar tunanin da zatayi akan Family din gaba daya.

“Kirki nake miki?”

Sai yayi yar dariya kadan wadda ba kasafai ya cika yin ta ba yafi ga murmushi. Daga kanta tayi alamar umm sai ya kara yin dariya kawai yana kama hannun ta, ya dora mata sabuwar iPhone 15 pro max da ya hada mata ita dazu. Kallon sa tayi da sauri sannan ta kalli wayar tana karanta abinda yake rubuce a jikin box din.

“It’s yours, ki kira Baba ki kira kowa amma banda mutum daya,I can’t take that.”

Sai ya mike ya fice ya barta rike da wayar da ko a mafarki bata taba kawo ta mallake ta ba iya rayuwar ta, latest wayar da kudin ta zai iya sauya mata rayuwar su ita da mahaifin ta, ranar da ta fara jin ana maganar wayar a class dinsu sai da taji kamar zatayi sabo saboda yadda idan da zasu samu kudin ita da babanta shikenan tasan zasu fita daga rayuwar da suke ciki.
Jujjuya wayar ta dinga yi tana hawaye ta rasa me ma zatayi ne wai? Dan kadan ta dauki snacks din taci ta shanye milkshake din sannan ta mike rik’e da plate din ta dora wayar saman gado tana kallon ta kamar ba gaske ba ta fito. Bude kofar da tayi yasa shi kallon wajen ta wuce shi ta kai kayan karon farko taji bari ta gyara wajen.
Tana gyaran ya shigo da sauri ya karaso ciki ya rik’e mata hannu yana girgiza mata kai

“Waya saki?”

“Kar a barsu a haka wai.”

“No akwai masu kula dashi, karki damu.”

Wanke hannun tayi a sink yana tsaye sannan ya tusa ta a gaba suka koma dakin ya bude kayan nata tana tsaye ya ciro mata veil yazo ya yafa mata akan rigar tata sannan yace

“Muje ki rakani.”

Jim tayi ta rasa me zata ce sai kuma ta daure tace

“Wayar fa?”

“Waya? Taki ce ai, ko color din be miki ba a chanja?”

“A ah, naga me tsada ce sosai.”

“Bata kaiki tsada ba, oya wuce muje kar dare yayi.”

“Nagode Allah ya…”

Sishsh ya dora hannun sa akan lips dinta alamar tayi shiru sannan yaja hannun ta suka fito.

Saddam na tsaye a harabar gidan sai sauran motocin Rafeeq din guda biyu da yace a ajiye su a gidan daga yanzu, gaishe shi sukayi Saddam ya bude musu kofar suka shiga sannan ya shiga mazaunin driver.
Ba kamar yadda suka zauna dazu ba, yanzu yana daf da ita har babu wata tazara a tsakanin su, hannun sa still yana cikin nata yana jin wani irin nutsuwa na saukar masa. A kaf rayuwar sa idan ka cire kuruciyar sa da yayi ta tare da mahaifiyar sa ba zai ce akwai wani lokaci da yake cikin farin ciki irin yanzu ba, shi kansa be san iya adadin farin cikin da yake ciki ba dan gani yake kamar ba gaske ba, kamar mafarki ne zai farka yaga komai ya chanja. Ko a haka suka zauna ya samu cikar burin sa, be san iya yawan son da yake mata ba, so mara algus irin wanda yake shiga chan cikin zuciyar mutum ya hana shi sakat. Ranar da ya fara ganin ta wata rana ne ta dawo daga madrisa, tana sanye da lemon green hijab da ya karawa farar kyakkyawr fuskar ta kyawu. Yana saman scooter dinsa a lokacin ya saka helmet yana sauri zashi wani waje traffic ya tsaida su, ita kuma a lokacin zata tsallaka titin ta tafi wajen Baban ta dake Sana’a a gefen wajen. Tun daga ranar ya zama kullum sai yaje wajen ya ganta be kuma taba fashi ba, karancin shekarun ta da matsalar gidansu ya hanashi tunkarar su da maganar haka yayi ta dakon soyayyar ta har zuwa yanzu da Allah ya cika masa buri ba tare da ya sani ba. Lallai Allah Me amsa adduar bayin Sa ne.
Dan murza hannun ta yayi ta waigo ya sakar mata murmushi daidai sanda suka iso Jabi Lake Mall. Parking Saddam yayi a wajen da suka saba parking duk sanda suka zo da Rafeeq din ta hanyar da zata shigar dasu ta baya wajen da ba mutane kwata kwata sai masu wajen da mutanen su. Wayarsa ya ciro ya kira manager din wajen wanda dama sai da ya kirashi yace yana hanya. Da kansa ya fito yazo har wajen motar sannan Rafeeq din ya fito tare da Noor din.

“Welcome Sir, welcome Madam.” Yace yana satar kallon Noor din dan be taba ganin Rafeeq din da wata mace ba

“Thank you.” Rafeeq ya amsa ita dai Noor tayi shiru tana jinsu suka nufi wani gini me dan banzan kyau da tsari tana ta kokarin boye al’ajabin ta amma Allah kadai yasan halin da take ciki

“How is family and everything?”

“Fine, ya kasuwa?”

“We thank God oo.”

“Allah ya taimaka.”

Wani parlour ya kaisu sannan ya sa wata yarinya ta kawo musu drinks da small chops sannan yace

“Me za’a kawo Sir?”

“Clothes, shoes, bags, jewelries, just bring everything.”

“Brand?

“Yes, anything unique.”

“Ok sir an gama.” Ya juya yarinyar ta bishi a baya.
Kaya masu kyau da tsada suka dinga jidowa wanda suke ganin zai ma Noor din tun daga kan English wears, Abaya, shoes, handbags laces, atamfa ready to wear da sauran tarkashen kayan mata.
Kawo musu akayi yace ta duba idan sun mata, tsawon and everything. Kasa dubawar tayi dan ta zama dumbfounded ta rasa abinda zatayi.
Shi da kansa ya dinga dubawa yana zabar mata har sai da taga kamar zai kwashe komai na shagon sannan tace yayi, be ji ta ba ya cigaba da abinda yake yi ya gama kwasar mata har da abinda bata ce ba kananan kaya na musamman da underwears sannan Saddam yayi payment aka zuba musu kayan a mota sannan suka nufi gidan su.
Lokacin goma ta kusa saura kadan suka shiga gidan, jikin ta duk a mace ta bi shi zuwa cikin gidan tana tsoron abinda zata tarar. Mummy na zaune a living room din gama wayar su kenan da Asim tana shirin wucewa shashen ta bayan yan matan biyu sun gama matsa mata kafa sai gasu sun shigo. Hannun sa cikin nata tun daga fitowar su daga motar dama ya rik’e mata hannun ko da taso ta zare sai ya hanata yaki kula kallon ta dan ma kar tace zatayi abinda ba haka ba.
Aikuwa hannun nasu dake sarke da juna ta fara kai kallon ta kafin ta dawo dashi fuskar sa tana tuna abinda su Aneesa suka ce mata dazu wanda bata dauka da muhimmanci ba dan tasan kawai yayi ne saboda ya nuna babu komai amma ganin su yanzu yasa tayi wani irin shock amma sai ta maze cikin iya bariki da duniyan ci tace

“Oyoyo my son, oyoyo daughter nah.”

Yunkurin durkusawa Noor take ya hanata ta hanyar rik’e hannun ta kakam sannan ya jata zuwa kujerar dake facing din ta Mummy din suka zauna jikkunan su jone da juna sannan yace

“Mummy barka da dare.”

“Barka dai son, ashe kuna tafe.”

“Ina wuni?”

“Lafiya lou yar albarka, sai ga ku a tsohon daren nan, maimakon ku zauna a gida ku mori amarci sai ku hau yawo a gari kamar wanda akayi ma auren kiyayya.”

“Mun dan fito shopping ne shiyasa muka ce mu biyo mu gaishe ki, mu kuma kara yi miki godiya, Allah ya saka da Alkhairi.”

“Ah haba haba, ai ba komai. Ku dai ku zauna lafiya kawai.”

“Bari mu wuce, sai an kwana biyu kuma.”

“Ba zaku sha ko juice ba, ko kai ba zaka sha ba tunda ka saba dashi ai a bawa daughter tunda dai ba saba sha akayi ba.”

Murmushi kawai yayi be sake tanka mata ba, dan yasan faking kawai take amma deep down yasan sai taji kamar ta jawo su ta shake, daidai kofar fita daga falon ya jawo Noor din jikinsa sosai ya manna ta da side dinsa a haka suka fice daga falon.

Suna fita ta mike tsaye a masifance ta dakawa masu aikin tsawa suka fice da sauri. Ji take kamar tayi ashar dan tasan da biyu Rafeeq din yayi mata haka. Gashi ko dazu da sukayi waya da Asim sai da ya sake jaddada mata maganar shegiyar yarinyar me zubin mayu. Anya batayi kuskure ba kuwa?

“Lallai ma yaron nan.”

“Idan kasan wata baka san wata ba.”

***Shi kadai a motar sai faman murmushi, yasan ya gama da ita a yau da kyar zata runtsa saboda tunani amma kuma ya santa sarai hakan da yayi zai kara mata karfin guiwar yin abinda tayi niyya din. A shirya yake da ita duk abinda zatayi din kuwa dan ta riga ta gama yi masa komai shi a yanzu.
Sallama sukayi da Saddam din yace ya huta gobe da jibi shima zai neme shi. Godiya Saddam yayi sannan ya tafi. A falon ya tarar da ita rike da wayar tana son yi masa godiya kafin ta wuce bedroom dinta yana zuwa daidai in da take tsaye be barta tayi magana ba yaja hannun ta zuwa dakin sa kawai. A kofar taja ta toge taki shiga ya waigo ya kalleta ganin ta tsaya yasa shi sakin hannun ta sannan ya dawo in da take tsayen ya daga ta daga kofar zuwa ciki dan ba zai iya ciwon baki ba. Dan fitar da sukayi duk ya gaji ruwa kawai zai watsa ya kwanta baya son wani dogon surutu yasan kuma idan ya tsaya biye mata zasu bata lokaci ne kawai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button