Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 8

Sponsored Links

*PAGE EIGHT*

 

Juyawa tayi ta fice daga kitchen din ta shiga dakinta ta kwanta da gaske kuwa baccin takeji don tana kwanciya ya dauketa me nauyin gaske bata farka ba sai goma ta shiga bathroom tayi brush ta fito ta nufi parlourn saboda wata mahaukaciyar yunwa da takeji bude qofar tayi ta fito suna parlour yana zaune ita kuma tayi matashin kai da cinyarsa kawar da kanta tayi taje zata gifta yace “barka da fitowa na kiraki ki fito muyi break naji shiru kawar dakai tayi tace “aunty Ina kwana ya gajiyar hanya” amsa mata tayi da faraar ta tana kallonta tana mamakin yanda duk ta canza mata cikin yan kwanaki ta zama wata cikakkiyar mace, zama tayi a dinning din taja tea flast ta hada tea ta farasha ji tayi yana hautsina mata a ciki kamar zai dawo dole ta ajiye cup din ta dafe kanta da hanunta biyu.

Related Articles

Kallonsa Sadiya tayi tace “Uncle Saddiq ya sakeyimin mgn akan Umaimah don Allah kayi mawa su Daddy mgn a turo ayi mgn inyaso sai ta cigaba da karatunta a gdansa” wani mugun kallo yakeyi mata yanajin wani mugun kishi na taso masa janye qafarsa yayi daga jikinta ya miqe a fusace zai bar gurin tayi saurin riqosa ta miqe tace “ni narasa me kake nufi da yarinyar nan Abdulhameed duk Wanda yazo neman auranta sai kace kayi mata miji bayan babu wani miji da kayi mata idan Saddiq ne bazaka bawa auran Umaimah ba to ai ga Nasir ga Bashir kabawa wani dama ya fito mana…” daga Mata hanu yayi a fusace yace “ya isheki haka Sadiya wai a kanki Umaimah takene da kika damu dasai anyi mata aure na fada miki an riga anyi mata miji lkc ne baiyi ba dazai bayyana kansa” yana fadin haka ya fincike hanunsa ya fice daga gdan a fusace daga ita har Umaimah suka bishi da kallon mamaki hawaye ne ya zubowa Umaimah na tausayin kanta, dafata Sadiya tayi tace “kada wannan ya dameki kinsan zafin zuciyarsa zaima sauko ne aidai dole wataran ya aurar dake” ajiyar zuciya tayi ta nufi dakinta ta kwanta.

Bai dawo gdanba sai dare tanajinsu shida matarsa sunata hayaniyar su akan qanin nata da yakeson auran Umaimah shikuma ya kafe akan bazai bayar ba zuciya tayi ta shige dakinta da qudurin zataje ta samu Daddy da kanta da mgnr tunda bashi kadai yakeda iko da Umaiman ba tsaki yayi shima ya shige dakinsa ya shiga wanka bayan yayi ya kwanta zuciyarsa tab da tunanin ta inda zai tunkari iyayen nasu da zancen Umaimah matarsa ce saboda yanada yaqinin basu sani ba tunda lkcn da kakansu ya aura masa ita dagashi sai abokinsa Yusuf sai malam Isa abokin kakan.

 

*WAIWAYE ADON TAFIYA*

 

Shakara daya bayan rasuwar iyayensu Umaimah Alh Ahmad Hameed da matarsa Khadija sanadin hadarin motar da sukayi a hanyarsu ta dawowa daga Damaturu gano dan da babbar yarsu Jameelah ta haifa.
Abdulhameed ne da Abokinsa Yusuf a hanyarsu ta zuwa Maiduguri gaida kakan Abdulhameed Alh Yauri wanda yake kwance bashida lfy tafiyar sukeyi cikin nishadi inda gaban Hameed ya tsananta faduwa kallon abokin nasa yayi yace.

 

“Yusuf Ina tunanin faruwar wani abu fah wlh tun jiya gabana yake faduwa” murmushi yayi yace “babu komai insha Allahu sai alkhairi” da wannan tunanin suka shiga garin Maiduguri kai tsaye gdan Alh Yauri suka nufa a parlour suka tarar da Hajjah Gana kakarsu wadda itace ta haifi mahaifin Hameed dana Umaimah Daddy shine babba sai Alh Ahmad murna ta hauyi ta fara magana cikin yaransu na shuwa “Ah lale da manya baqi yau babban ango nane a gdan dama tun jiya Kaka yaketa tambayar ka yana kiran sunanka” murmushi yayi yace “to gani me zai bani da yake nemana kota matsone mu tafi maqabarta haqan kabari” daquwa tayi masa tace “kajini da dan qaniya yana neman jamin jarfa” ta jefeshi da pillow ya goce yana dariya dakin da kaka Yauri yake nan ya shiga ya qarasa da sauri gaban kakan nasu ya durqusa tare da kamo hanunsa shima kamawa yayi cikin rawar murya ta rashin lfy yace.

 

“Nayi farin cikin zuwanka Me suna ina inama burina ya cika akanku inama zankai lkcn dana diba muku domin tabbatuwar muradina” kallonsa sukayi da sauri yace “Ina amanar Allah Hameed ina Borno zuciyata na Kano a gdanka” cikin sanyin jiki yace “tananan qlau Kaka saidama na sauketa makaranta sannan muka taho ya jikinka” sake kama hanunsa yayi yace “tasheni Hameedu inason neman wata alfarma a gurinka nasan banida matsala dakai zakai” miqewa sukayi suka suka gyara masa zama ya kalli Yusuf yace “Kira Hajiya” fita Yusuf yayi ya kira Hajiya Gana Wayarsa ya dauka ya miqawa Hameed yace “ka kiramin Mal Isa” batare da gardama ba ya lalubo number Mal Isa ya dannan kirar cikin qanqanin lkc ya daga ya karawa kaka a kunnensa kaka yace “Mal kazo Hameed yazo yau zan sauke nauyin dake zuciyata yau zan cika burin dana Ahmad daya mutu dashi a bakinsa” yana fadin haka ya sauke wayar mamakine yasa Hameed sakin baki yana kallon kakan nasu da tunanin wannan wanne irin burine da koyaushe idan yazo sai kaka yayi masa mgnrsa.

 

Kama hanunsa kaka yayi yace “inasa ran amanar Allah bazata tozarta a gurinka ba Hameed babanka Ahmad ya mutu da qudurin aura maka qanwarka Umaimah wannan shine zancena na qarshe dashi ranar da sukazo Damaturu ganin danda Jameelah ta haifa mun hadu dasu a Damaturu yake cemin “Alh banida burin daya wucce ganin zuri’ar mu ta qara habaka ta hanyar hada dunqulalliyar zuri’a Alh inada burin idan Allah ya rayani har zuwa lkcn da Umaimatu zata kai minzalin aure na aurar da ita ga dan’uwanta Abdulhameed badon komai ba saidon nasan ko bayan raina bazatayi kukan maraici ba Alh koda Allah yasa bankai wannan lkcn ba na doraka kazama wakilina ka cikamin burina zanyi farin ciki da hakan, wannan itace mgnr da take damun zuciyata kuma in har ka amince Hameed a yanzu zan daura auranka da qanwarka Umaimah kafin nima qasa ta rufe idona inyaso kaci gaba da rainon matarka kuma qanwarka”

A tsorace ya dago ya kalli Alh Yauri yace “amma Kaka…” daga masa hannu yayi yace “bance kacemin komai ba Hameed wannan aurene me daraja da ya zama dole ka karbeshi” agogon dake saqale a hanunsa na gold da zaikai 500k kaka ya kwance yace “na karbi wannan a matsayin sadakin Umaimatu Mal Isa ka zama shaida Yusuf kaima shaida ne sannan kema gana shaida ce ga Mal Imam shima shaida ne ni Abdulhameed Yauri shuwa nabada auran jikata Umaimah Ahmad Hameed Shuwa ga jikana Abdulhameed Adam Hameed Shuwa kuma na karbar masa auran Umaimah akan sadaki mafi daraja da fatan Allah ya basu zaman lfy” nan akayi duk wani abu daya dace kaka ya dauki agogon ya miqawa Hajiya Gana yace “Ki adanashi kuma inason ya zama sirri tsakanin mu harsai lkcn da Umaimah takai mace sannan a bayyana mawa kowa ya sani” shidai Hameed jikinsa gaba daya a sanyaye yake wai Umaimah qanwarsa itace a matsayin matarsa? Ya tambayi kansa wasu hawaye suka zubo masa na farin ciki tabbas wannan wata kyauta ce ta ubangiji da yayi masa kuma ya zama dole yayi masa gdy Babyn Uncle ta tabbata tasa a lkcn da baiyi zato ba yanzu tashin hankalin sa yanda zai tunkari Sadiya da mgnr yasan baqin kishinta idan ya kuskura taji lbr an daura masa aure da baby ikon Allah ne kadai zai hanata kasheta saboda haka shima ya quduri niyyar boye auran nasa harsai lkcn da Umaimah tayi hankali.

 

Koda ya dawo gdan bai bari ta fahimci wani abuba cikin wasa suna zaune a parlour yake cemata yayi aure yanda yaga tatada hankalinta ne yasashi tsuke bakinsa ya mayar da abin wasa kawai aka tafi a haka, lkcn da Umaimah ta fara tasawa ta zama budurwa lkcn ne samari sukayi mata cahh amma irin wulaqancin da yake mawa masu zuwa gurin Umaiman ne yasa duk suka samawa kansu lfy suka hqr ganin yanda maza sukayiwa matar tashi cah ne yasa ya hanata fita ko qofar gda haka rayuwar taci gaba da gurgurawa har kawo wannan lkcn da muke ciki.

 

Satin Sadiya biyu da dawowa komai ya kwancewa Hameed kwata² Umaimah ta daina yarda ko a parlour su hadu da taji tsayawar motarsa zata gudu dakinta data fakeshi ta dauke key dinta yasha dawowa da rana kawai don ya ritsata amma ya gaza cimma nasara gashi koda safen ma yanzu dake anyima yaran hutu bata fitowa saiya fita sosai wannan sauyin yake damunsa dukan yayi masa yawa ya riga ya saba da Umaimah ta gujeshi ta daina bashi kulawa gashi itama Sadiya tunda ta dawo daga tafiyar sau daya ta yarda dashi shima gani tayi yana neman mutuwa.
Yanzu duk target dinsa bai wucce akan yanda zai samu kebewa da Umaimah ba cikin sati biyun baifi sau biyu yasata a idonsa ba kwana uku kenan da yayi Mata gani na qarshe lkcn suna zaune a parlour dukkansu suna kallo da magaruba bayan sunyi sallah ta fito sanye take da hijjab dinta har qasa ta tsugunna a gabansa ya zuba mata ido itama Sadiyan ita take kallo cikin sanyi muryarta tace “gani Uncle” mamakin hasken da tayi yakeyi duk da kanta a qasa yake amma ya fahimci ramar da tayi a kausashe yace “bakiga saqona bane” dagowa tayi da sauri suka hada ido shima itan yake kallo da dukkannin hankalinsa tsawa ya daka mata yace “ba mgn nake miki bane kika kafeni da ido” idonta ne yayi qwalqwal da hawaye cikin in…ina tace “da…dama Uncle bani da lfy ne sh…shine…” miqewa yayi ya dauki rigarsa yasa yace “shine bazaki iya fadamin ba saboda ban isaba to kitashi kizo muje Daddy ne yake nemanki” yana fadin haka ya fice.

 

Ta dade a tsugune kafin Aunty Sadiya tace “saiya kuma yimiki mgn ko?” Miqewa tayi ta shiga dakinta ta sako takalminta ta fito gabanta na wata muguwar faduwa ta nufi harabar gdan a tsaye ta tarer dashi jikin motar yana hangota ya nufi cikin motar ta zagaya ta tarar harya bude mata shiga tayi ya sanya hanunsa ya janyo murfin ya rufe yaja motar a guje ya fice daga gdan sunyi tafiya me nisa kafin ya waiwayo ya kalleta yanda yaga ta hade raine ya bashi dariya yayi murmushi yace “Babyn Uncle Hameed duk haushin na fito dake daga gdane yasa ake wannan cin maganin?” Shiru tayi batare data tanka masaba ganin sun wucce hanyar da zasubi takaisu gdan Daddyn ne yasata dagowa ta kalleshi ya kawar dakai kamar bai ganiba yaci gabada tuqinsa cikin kwanciyar hankali bayan Abdullahi Wuse Specialist Hospital yabi sunyi tafiya mai tsayi taga yayi parking a wani parkin speace qasa tayi da kanta ta kifashi akan cinyarta qamshin turaren jikinsa dana motar na qara hautsina mata zuciya fita taji yayi daga motar baifi minti biyar ba ya dawo ya bude mata ya ruqo hanunta tare da dannawa motar key ya jata suka shiga cikin gurin itadai bin gurin take da kallo takasa gane inane har saida suka shiga reception din taga an rubuta (WELCOME TO PRINCE HOTEL) gabanta ya qara faduwa a karo na biyu ta sake kallonsa yana riqe da hanunta wannan karon sun hada ido amma yanda taga fuskarsa babu annuri ya koma mata asalin Uncle Hameed din data sanine yasata qara tsuke bakinta wanda dama idan tace zata budeshi komai zai iya faruwa a qasan taga ya nufi wata qofa ya bude da key dinta yaja hanunta sun shiga ya mayar ya rufe tare da sakar mata hanun.

Zazzare ido ta hauyi tana neman toilet hango wata qofa ne yasata juyawa zata shiga yakai hanu ya ruqota fizgewa tayi ta nufi qofar da gudu ta budeta tun daga tsaye ta fara kwara amai babu komai a cikinta sai ruwa saboda bata iyacin komai sai ruwan Lipton da sauri ya shigo toilet din ya ruqota yana danna mata qirjinta cikin tashin hankali yanata zuba mata sannu ruwa ya bata ta kuskure bakinta ya ruqo hanunta suka fito ya cire mata hijjab din yana qara yi mata sannu kwantar da ita yayi sannan ya komai ya wanke gurin ya gyara ya fito ya zauna kusa da ita ya ruqo hanunta yana matsawa a hankali yace “kinyi period wannan watan?” Dago idonta tayi daya fara lumshewa alamun bacci tana kallonsa da mamakin tambayarsa ganin tana neman raina masa hankali ne yasashi qara tamke fuska yace “tambayarki nakeyi fah” a kasalance tace “sati guda kenan da wuccewar lkcn period dina nama fadawa Aunty…” da sauri ya kalleta hakan yasata hadiye mgnr yace “kikace mata me?” Cikin qosawa da mgnr tace “cemata nayi inason ta tambayarmin kai zani asibiti a dubani” sake kafeta yayi da lulu eyes dinsa yace “ke bazaki iya tambayata ba” shiru tayi masa saboda ta lura mgn kawai yakeson ja da ita sakin fuskarsa yayi kamar bai taba daure fuskaba ya matsa kusa da ita tare da kwanciya ya janyota jikinsa ya dora hanunsa a saman cikinta yace “ina taya kaina murnar samun qaruwar da nayi a jikin qanwata Babyn Uncle cikine dake…..”

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*

 

*🅱RILLIANT WRITERS* *ASSOCIATION* 🖊
( _Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writers)_

 

*GIDAN UNCLE*
( _Love and romantic story_)

*SHORT AND TRUE LIFE STORY*

 

*MALLAKAR*
👇🏻
*FAUZIYYA TASI’U UMAR*
*®FAUZAH*

 

Wattpad👉🏻 realfauzah

 

[email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button