Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 29

Sponsored Links

30 – 31

 

_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba_

_3107021073 first bank aisha Muhammad pay 300 access fee in kinason this novel sai kituro evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

_masu fitarmin da novel waje kunma kanku_

Da sauri Abie yatashi yana kallon Aabid dayay wani irin zaman kalan tausayi yabi ta gefen Mami dake kuka sosai yawuce kitchen dinsu, bawani jimaba yafito dauke dawani bowl da towel aciki karami yakaraso wajen inda Suleman yake rike dashi ya ijiye bowl din akasa ya matso towel din yakai kan goshinshi yana kiran sunanshi ahankali “Aadil, Aadil, open your eyes” kara maida towel din yayi cikin ruwa ganin jikinshi ya soma rage kakkarwan yasake maida towel wuyanshi yana gogamai da sauri Mami ta tashi tarike hanunshi tace “sannu Aadil dina, wake up my baby please, tashi kaji ga Mamin ka anan kusa dakai” tai maganan tana sharemai fuskanshi da lema leman ruwan towel kekai ta manna mai kiss ahankali a kumatu, ahankali tamai whispering. “Aadil wake up” slowly jikinshi yay relaxing sosai yadena convulsion din da sauri Mami ta karbi towel din daga hannun Abie takai cikin ruwan taciro ta sharemai gefen bakinshi tanamai magana. “wake up Aadil, tashi tashi yaron Mami” ahankali yabude idanunshi dasuka kumbura sukai jajir ya daura kan Mami yay shiru yana kallonta batare dayace komiba, yay wani irin kalan tausayi kaman kamai kuka, da sauri Mami ta rungume fuskarshi a kirjinta tace “am sorry Aadil kaji, my babyboy tell me mekake so?” tai maganan tadago kanshi tana kallonshi tanamai murmushin da uwa kema yaro na tsantsan so, hawaye ne ya gangaro ta gefen idanunshi suna shiga kunenshi wani irin bakin ciki yakeji sabida rashin ganin Hamida kaman zai mutu, zuciyarshi sosai takemai zafi kaman ana soyawa amma bazai iya bayanin mekemai ciwoba, da sauri Mami tasa hannu ta gogemai hawayen muryanta narawa sosai tace “talk to me Aadil dan Allah kamin magana kaji” shiru yayi yana kallonta batare dayace komiba hakan yasa Abie ya karbe shi daga hanunta, ahankali ya kalli Abie hawaye na gangarowa daga idanunshi yay wani irin shiru kaman bashiba, murya chan Abie yace “menene Aadil mekema ciwo? Mutafi asibiti? Me kakeso” shiru yayi yana kallon Abie hawaye yasake gangarowa daga gefen idanunshi yakasa magana, dan ajiyan zuciya Suleman ya sauke yace “kodai natado Baba ne?” da sauri Abie yace “a’a kasan Baba nada hawan jini in gari yawaye yasani, mubarshi yay bacci yana bukatar bacci” kallon Aadil yayi ahankali ya sharemai hawaye yace “ga Hamida nan zuwa kaji, be fine kaga Mamin ka dukta damu” gyadamai kai yayi yafashe da kuka ahankali mara kara dake fita da kyar, zuciyarshi namai wani irin zafi sosai jiyake kaman zai mutu, kirjin Abie wani irin bugawa yake sabida abinda ke shirin faruwa, da kyar ya tattaro duka kuzarinshi ya kalli Sulemanu yace “mutafi dashi asibitin” tashi sukayi ahankali suka dago Aadil din dake kuka sosai mara kara Mami na sharemai hawayen sukai hanyar fita daga dakin, Suleman ne ya kalli Aabid dayay wani irin zama akasa kanshi akasa kaman wanda akama mutuwa hakan yasa yace “lafiyan ka Aabid kokaima ba lafiyar ne” ahankali ya dago kai ya kalli Mami da sauri Mami cikin fushi ta wuce tafita daga dakin Abie yace “muje Suleman” sukawuce suka fita daga dakin suka saka Aadil din a mota Suleman yaja motar sai asibiti, wani irin tari Aadik din yafarayi yana kuka agalabaice yana dukan kirjinshi dakemai zafi sosai, bottle water Mami ta bude ta mikamai da sauri tace “ungo kasha” ture ruwan yayi da hannu yana tari sosai jinin da Mami tagani jikin goran ruwan datake mikamai ta sanadin tarin dayayi mai karfi yafito yasa tasaki salati tasaki ruwan akasa. “innalillahi wa innailaihi raji’un, Abie Aadil, Ab…” baya Aadil yay luuu kaman ya sume jini duk a lips dinshi da gefen bakinshi, da sauri Mami ta kamoshi ta rungume shi sosai tama rasa mezakayi, chan kasan makoshi idanunshi a kulle yana wani irin nishi yace “Mami Hamida my wife, call her for me” yafara wani tarin jini na fitowa sosai, fashewa da kuka Mami tayi tace “Abie, Abie d’ana, Yaya Suleman ka kara gudu, Abie Aad….” denajin numfashin shi da tayi a wuyanta yasa gabanta yay wani irin mummunar fadi tawani irin sakeshi yay baya luuu daidai lokacin suka iso asibitin…..

Aabid yakai kusan minti arba’in a zaune kanshi yadau wani irin zafin daya dade baimai ba, da kyar ya iya tashi ya ja kafa yay hanyar dakinsu, ahankali ya bude kofar dakin yay shiru yana kallon dakin ya sauke idanunshi akan belt dinshi da Mami ta jefomai dazu akwance akasa wanda ya daki Aadil dashi, shiru yayi yana kallon ko ina yanda ya bugi Aadil na dawo mishi sabo a ido yana kallon fuskar Aadil yana kuka yana sosa inda ya dakai yana cemai. “stop beating me Bid” shigowa dakin yay ahankali yana jan kafa, idanunshi ya sauka akan aman da yasan Aadil dinne yayi sosai zuciyarshi tamai daci, miyan bakinshi ma yamai daci yakasa hadiyewa, fita yayi yakoma yadauko mop da bucket ya gyara kasan dakin tass ko ina ya dauki kamshi sanan ya shiga bathroom yayo wanka yafito sanye da bathrobe yarasa meyake mai dadi, zama yayi abakin gadon su ya kurama hotonshi dayay tareda Aadil din ranan salla ido yana kallon Aadil din, yay mugun nadaman dukanshi dayayi bana wasaba, har tsoron kulle ido yake dan ganin fuskar Aadil yake yana kuka yana cemai “stop beating me Bid” wani irin fadawa gado yayi ya daura hanunshi akan heart dinshi dake beating fast, kafin yatashi da kyar yabude wardrobe dinsu ya zaro white jallabiya yasaka, ya shimfida dadduma yay sallolin da ake binshi sanan yadau car key yafita yabisu asibitin.

 

 

 

**
Da asuban fari ta tashi daga baccin daya dauketa kan daddumar, jinginar da bayanta tai jikin gado tana karanto addu’an tashi daga bacci, ko kadan batajin dadi jikinta saima wani irin kanta dataji yana mata ciwo, bude kofar dakin da akayi yasa ta dago kai ahankali, Anty Lami ne ta shigo sanye da dogon hijabi tace “au harkin tashi” gyadamata kai tayi tana sosa ido hakan yasa yace “to tashi kije ki dauro alwala” gyadamata kai tayi ahankali ta mike tsaye Anty Lami tabita da kallo harta shiga bayi, yarinya kyau har kyau ga diri amma haryau bata da saurayi ko daya, shiru tayi tadan tabe baki dam bataso tasaka lamarin Hamida arranta da sassafen nan dan zata tashi da ciwon kaine abanza ta maida kofar ta rufe tai dakin yaranta maza danta tasosu subi Abban su masallaci.

Baki kawai ta wanke tafito daga bayin ahankali danji tayi cikinta namata ciwo sosai, drawer Anty Lami taja nanko taci karo da pad, guda daya ta dauka takoma bayi wanka tayo ta shirya tsaf sanan ta dauro alwala tafito daga bayin, adaddafe ta shafa mai tasa riga tahau gado ta kwanta dan sosai taji zazzabi na neman kadata, wajejen 7 Anty Lami takara shigowa dakin ganinta dukunkune kan gado yasa ta maida kofar ta rufe takaraso ciki da sauri dantasan Hamida bata komawa baccin asuba saitai karatun Al Qur’ani, ahankali ta yaye bargo data rufa dashi hakan yasa Hamida tabude jajayen idanunta ta kalli Anty Lami dake wani irin kallonta, ahankali tace “ina kwana Anty” dasauri Anty Lami takai hanunta kan wuyanta ganin yanda take maganan arude ta janye hanunta daga kan wuyanta tace “bakida lafiya Hamida, meke miki ciwo?” dan yamutse fuska tayi tace “cikina ke ciwo” da sauri Anty tace “kin fara kenan kinga pad a drawer na?” gyada mata kai tayi tana goge hawayen dasuka zubomata na wahala, maida bargon tayi ta lullubeta tace “sannu kinji bari nakarasa breakfast nakawo miki kici kisha magani anjima idan ya lafa saimu je gida” gyada mata kai tayi hakan yasa Anty lami ta shafa fuskarta tawuce tafita daga dakin. Fashewa tayi da kuka sosai tarasa meke damunta deep down jitaje kawai so take taga Aadil, she miss his innocence dakomi ma nashi, ko hanunta ta daga saita dingajin kamshin shi, hakanan ma saita dingajin kamshin shi kaman yana wurin, gashi batada waya balle yadan rage mata kewa kokuma wani abun, kasa dena kukan tayi har Anty Lami tadawo dakin da sauri ta share hawayen fuskarta gudun karta gani tafara mata masifa, karasowa ciki tayi rike da tray tana kallon fuskarta tace “kuka kike ko? Kodai muje asibiti ne” girgiza mata kai tayi ahankali, ajiyen abincin tayi akan rug tayaye bargon jikinta ta miko hannu ta dagata ta sauko da ita tace “ga kunun nan kisha da chips kisha magani saiki kwanta wuraren shadaya zamu je gidan, yanzun nan ma muka gama waya da maman ki” kallonta tayi ahankali tace “Mama” “eh maman ki tace nagaishe ki” murmushi tayi tadau kopin kunun takai baki hakan yasa Anty Lami tai murmushi tawuce tafita ta shiga kitchen ta kwaso lunch box din yaranta ta mimmika musu tace “kuje ku gaishe da Antyn ku saiku tafi driver na jiranku” da sauri sukai dakin Hamidan fadawa jikinta sukayi ta washe baki sosai dan tanason yara ta shafa kansu tace “byee ayi karatu da kyau” da gudu suka fita ta cigaba da shan kokon taci chips din kadan sanan ta tatatara ta kwashe tafita daga dakin ta shiga kitchen ta wanke duka kwanukan data gani a wurin ta share kitchen din tsaf konina na kyalli. kwala mata kira akayi. “Hamida jeki shirya Abban ku zai tafi aiki yanzu” ahankali tace “to” ta dauraye hanunta a sink tawuce tafita daga dakin ta shiga dakin Anty Lami kayan data gani anty Lami ta ijiye mata akan gado ta shirya acikin su bakin gown ne mai kyau tadau hijabin tasaka daidai nan Anty Lami tashigo dakin tace “iyye mai kama da mamanta kinyi kyau, mutafi to” murmushi tayi ta sunnar dakai tana wasa da yatsunta ta, tabi bayan Anty Lami suka fita tsakar gida motan Abban ta shiga bayan sun gaisa yatada motar suka shiga hanya dashi da Anty Lami sai hira suke gwanin ban sha’awa har jan bulo, ganin kofar gidansu yasa gabanta yawani irin fadi, akofar gidansu Abba yay parking suka fiffito daga motar, Anty Lami takama hanunta ganin takasa shiga jikinta sai wani rawa yake suka shiga cikin gidan, Abban su Ra’is biye dasu, agaban falon su Anty Lami ta kwada sallama ta shiga Abba da Mama dake zaune kan kujera ne suka amsa su Zainab da Ihsan kuma nakan dining suna gyaran wake a tray, Tashi Mama tayi tai murmushi jin muryan Anty Lami tace “shigo Yaya” shigowa Anty Lami tayi Hamida biye da ita abaya kanta akasa, ta kalli Abba dayawani irin kafe Hamidan da manyan idanu tace “ina kwana Abban su Ayush” dan murmushi yayi yace “barka da zuwa ga wuri” kokarin zama tayi tana mikama Mama jakarta tace “tareda Abban su Ra’is muke yana tsakar gida” da sauri Abba yamike tsaye yace “la shine kika barshi waje” yafita dan shigo dashi, wani irin kallonta Mama tayi yanda kanta ke kasa takasa dago kai sai wasa take da yatsunta yasa Mama buga uban tagumi, da gudu Ihsan ta sauko daga dining tazo tafada jikinta tace “oyoyo Anty Hamida naaa” Zainab kuma ta balla mata harara tacigaba da gyaran wakenta dan lamarin Hamida yanzu haushi yake bata, Sallaman su Abba yasa Ihsan tasaketa tai dining Anty Lami ta nuna mata gefen ta hakan yasa taje ahankali ta zauna akasa kusada kafarta, Abba kuma ya shigo tareda Abban Ra’is Mama kuma tadawo gefen yar uwan ta ta zauna, su Ihsan suka taso suka gaishesu ya amsa cikin fara’a Zainab tawuce kitchen tafito da tray da drinks ke ciki da snacks takawo ta ijiye sanan tadau tray din tawuce itada Ihsan suka wuce dakinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button