Munayamaleek 31
XXXI….
<31>
MunayaMaleek is 500, pay to 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta 07082281566.
Tsabar firgice da mamaki ne ya Kama munaya, hakan ya sanya tana kallo ya tafi da little Amnah. Sai a lokacin ta cire hannun ta daga kan kuncin ta.
Mai gadi ya cika da mamakin wulakanci Irin na Maleek, ya so ya fahimci abinda ya faru amma kasancewar baya nan suka fara shiyasa bai fahimta duka ba, ya dai san yayi laifin barin gida a buɗe Wanda garin sauri yaje ya dawo ashe bai rufe duka ba, ya shiga bawa Munaya hakuri yana kokarin mata bayani, kuma ta girgiza masa kai kawai ta nufi cikin gida, mai gadi ya bita da kallo, tsoron sa kada ta fadawa masu gidan aikinsa ya samu tsaiko, duk sai yaji babu dad’i, kiran iyalan sa da yake son yi ma a waya ya fita a ransa.
Munaya kai tsaye dakin ta ta nufa ita Maleek zai mara, magunguna sa sun ma fi kona mata rai, ita zai nuna wa yafi son little Amnah, taji wani ɓacin rai ya kara cika zuwa zuciyar ta, tsanar sa kuwa ninkuwa tayi a ranta, bayan ta shiga daki ta kwanta a gado, tayi kuka mai isar ta sannan ta ɗan ji sauki a ranta, idanun ta da fuskar ta suka kumbura, tana sakin shesheka ta nufi toilet, ta wanko fuskarta ta fito ta zauna a bakin gado tana sakin ajiyar zuciya.
Hankalin ta bai fara tashi ba sai da ta ga awa daya ta cika bai dawo mata da yarta ba. Me zata cewa barrister Abrar idan ta dawo? Nadamar bacciin data yi take, amma ta kasa hana kanta domin wani Irin bacci mai dadi da karfi ne ya fisge ta a dazun, yanxu wa zai fahimce ta, za’a ce sakaci ne ya janyo haka, za’a kuma ace wani irin bacci ne zai ɗauki mutum har yarsa ta fita Wajen gate bata sani ba, mamakin yanda akayi little ta fice daga gidan bai bar ta ba domin farfajiyar gidan da fadi hadi da tsayi.
Har aka yi sallar azahar bata ga alamar za’a dawo da little Amnah ba, hankalin ta ya kara mugun tashi, ta rude ta kuma rasa abinda zata yi, sai kuma tunanin Shakur ya fado mata rai, cikin sauri ta janyo wayar ta, ta danna wa Shakur kira.
Shakur na dagawa ta fashe da kuka, hankalin sa ya tashi ya mike tsaye yana fadin “innalillahi wa inna ilaihi raju’un! Munaya lafiya meye faru?”
“Ya Shakur, ya zo ya tafi da little Amnah” tace tana ƙara rushewa da kuka.
“Wa…waye ya tafi da ita?” Shakur ya tambaya gaban sa na faduwa.
“Shi mana, bab…” Wallahi ko sunan sa bata son kira.
Shima Shakur ya katse ta cikin ajiyar zuciya daya ji hannun da take, amma kuma yayi mamakin abinda ya saka Maleek din daukar ta.
“Munaya yi shiru ki min bayani how comes?”
“Kawai ina kwace a falo bacci ya dauke ni, ashe na manta ban datse kofar ba, shine ta fita har wajen gate…”
“Wait! Wajen gate kuma, shi mai gadi yana ina?”
“Shima ya fita siyo kati garin saurin yaje ya dawo kawai kare kofar yayi ”
“Ya Allah!” Shakur ya fada, kana yace “cigaba ina jinki “bayan na farka na cigaba neman ta ko ina ban gan ta ba, na fito compound din gidan, nan ma bata nan shina na fita wajen gate din, kawai na ganshi tsaye rike da little a hannun sa…”
Jin tana kuka sosai ya katse ta da faɗin “ya isa munaya kin ji, babu abinda zai faru za’a kawo ta”
“Toh dan Allah kace masa yayi sauri” tace tana katse kiran ta ja majina kana ta kwantar da kanta a jikin pillow.
Maleek dake tuki cikin bacin rai dan ma ya san angel din sa na cikin motar ne shiyasa ya rage gudu, duk bayan seconds biyu yake juyowa ya kalle ta, domin a kujerar mai zaman banza ya zaunar da ita ya daura mata seat belt.
Sai gwaranci take masa tana kallon titi cikin murna, hakan ya saka ya dan ji sanyi a ransa ganin ta da kuzarin ta, office ɗin ma ya fasa zuwa, wani private hospital Ya kai ta, bayan sun iso ya fito daga cikin motar, kana ya zagaya ɓangaren da take ya dan duka ya cire mata seat belt din kana ya dauke ta suka nufi cikin asibitin.
Nurses dake cikin asibitin suka zuba masa idanu domin da yawa ya yi bala’in burge su, ya kalli daya daga cikin su “where’s the paediatrician office?” ( Paediatrician Yana nufin kwarraren likitan yara) yace wa nurses ɗin fuskar nan a dinke tsaf, sai “baby baby” nurses din ke faɗa Cikin yiwa little wasa.
Wata mai iyayi da rawar kai daga cikin su ta mike tace “Muje na nuna maka”
Bayan ta shiga office ɗin ta fara sanar da likitan, likitan ya bada izinin a shigo, ta sanar da Maleek din tana masa murmushi, ko kula bai ba ya shige office ɗin, likitan dake zaune shima ya bishi da kallo yana neman mara lafiyar, domin bai yi tunanin little Amnah bace saboda ya ga y’a bulbul sai gwaranci take, amma kuma you never can tell domin ance shi mai daki shi ya san inda yake masa yoyo.
“Please have a sit” doctor’n ya fada.
Maleek ya zauna ya daura little Amnah a cinyar sa yace “na kawo yata check up ne”
“Me ke damun ta?” Doctor ya fada.
Maleek ya kalli fuskar little Amnah yace “kasa taci”
Likitan ya mike yace “Muje ka daura ta kan gadon can sai na duba ta”
Babu bata lokaci Maleek ya daura ta din, yana rike da hannun ta daya.
Sosai likitan ya duba Little Amnah kana ya Kalli Maleek din yace ” bayan kasar taci wani abu?”
Hankalin Maleek ya tashi domin ya zata akwai wata matsalar.
“Akwai datti a kasan waje dai, ban sani ba ko ta hadiye wani abu zuwa nayi na tarar da ita, akwai matsala ne?” ya fada yana cije labbansa, tsanar munaya ya kara rufe shi, how dare she ta bar masa Ya cikin datti, Allah kadai ya san tsawon lokacin data dauka a wajen nan.
“Babu wata matsala in sha Allah, zan dai rubuta wasu magunguna sai ka siya a pharmacy, amma a kula kada a bari irin hakan ta kara faruwa, zata iya hadiye wani abun, domin yanzu cututtuka sun yawaita ga Kuma jikin yara is very sensitive suna saurin kamuwa da kwayoyin cuta, Allah ya kiyaye gaba, zaka iya ɗaukar ta na gama”
Maleek bai ce komai ba ya dauki little Amnah ya dawo kujerar dake kallon likitan ya zauna, likita ya rubuta masa drugs din kana ya miƙa masa, Maleek ya karba, suka Yi musabaha ya cewa likitan “thanks” kana ya mike ya fita.
“Ke wallahi gayen nan ya haɗu sosai fa” nurse din dazu mai suna Safiyya ta fada.
Wacce ke zaune kusa da ita mai suna halima tace “baki ga su sister Aysha sai Maganar sa suke ba”
Nurse Safiyya ta tabe baki cikin jin haushi kana tace “ke Ni ba wanna ba, kina tunanin yana da aure? Ni kallon single father nake masa, ko matarsa ta rasu ko sun rabu”
“nurse Halima tace “ai bana jin yana da aure gaskiya, amma kuma suna kama sosai da yarinyar, idan kuma yana da auren ai da matar sa ya kamata su zo nan, ta bakin naki dai kila single father ne matar ta rasu” nurse Safiyya ta saki ajiyar zuciya tace “Allah ya sa hakan ne ” sai kuma suka kalli juna suka tafa suna dariya.
“Allah baki ji yanda ya shiga raina farat daya ba”
Nurse Halima zata bata amsa ta hango fitowar Maleek din sai tace “kin gan shi ya fito”
“Barin in je” nurses Safiyya ta fada wa kawar ta kasa kasa.
Tana wasa da hannun ta, cikin murmushi tace “kun fito, hope she’s fine Babu Matsala?” Duk da fuskar sa na hade amma yaji dadin kulawar da ta nuna wa yarsa, yace ” babu, thanks for the care”
Dadi ya kashe nurse Safiyya tace “Please kawo ta na rike ta naga kamar pharmacy zaka je” ta fada tana kallon farar takardar hannunsa, ba musu ya miƙa ta, little Amnah kuwa ta noke a jikin baban ta, cikin sigar jan hankalin yara tana mata wasa mai haɗe da dariya tana miƙa mata hannu, cikin sauri little Amnah ta fada hannun ta, sai ta nufi wajen kawar ta, ko kula sauran nurses dake kallon ta suna kuskus bata yi ba.
Ta mayar da hankalin ta wurin yiwa little Amnah wasa kawar ta nurse Halima na taya ta, little Amnah kuwa sai bangala dariya take.
Babu jimawa ya dawo, ya karbi yarsa har sun fara tafiya ta biyo shi tana cewa “hala wasan kasa tayi ko? Naga jikin ta ya bace, If you don’t mind sai na sanja mata wasu kayan, domin bazata zama comfortable dana jikin ta ba” ita fa lallai so take ta burge shi.
Ya juyo ya kalle ta kana yace “akwai wajen siyar da kayan yara ne nan?”
“Eh akwai a gefen asibitin nan”
“Okay ga card dina” ya gaya mata pin kana ya koma reception ya zauna riƙe da little Amnah.
Maimakon nurse Safiyya ta nufi waje sai ta zo wurin nurse Halima tace “ke anya shima mutumin can bai kyasa ba kuwa, Kinga atm card din shi ya bani nayi wa yarinyar siyayyan kayan da zata saka a store din *unique kiddies and more*
“Kina wuta kawata dan Allah da gaske kike?” Nurse Halima ta fada cikin murna.
“Wallahi, kin ga shi nan ma, barin yi sauri na dawo kada na manta pin din daya fada min”
Babu jimawa ta dawo kuwa, ta miƙa masa card din tace “kawo ta na sanja mata kayan sai na dawo maka da Ita”
“A ina kenan?” ya tambaye ta.
“A dakin da ma’aikata suke hutawa” ta fada tana murmushi.
“Why not ki sanja mata a nan, or just live it zan sauya Mata a mota, thank you”
Cikin rashin jin dadi tace “ka yarda dani, bazan cutar maka da ita ba, i don’t know who she’s to you amma yarinyar ta shiga raina Sosai, sanja mata kaya a nan yana nufin daidai da karya dokar asibitin nan, kaga there’s camera everywhere za’a ganni hakan Kuma zai iya janyo min matsala”
“Okay” yace Cikin amincewa da ita, ya mika Mata little Amnah ta karɓe ta.
*staff room* din mai girman gaske ne, ta nufi daidai inda locker dinta yake, ta bude ta ciro sallaya ta shimfida hadi da kwantar da little Amnah, ta nufi sink, ta kunna kan famfon ta taro ruwan Dumi, hankici dinta ta saka ta goge jikin little tas take yarinyar ta dawo da hasken ta daya dan dishe, masu hutawa a Dakin sai yaba kyawun ta suke, Wasu kuma na cewa “sister Safiyya ina kika samo yarinyar indiyawa haka” sai dai tayi dariya kawai, kanta na fasuwa, hatta ta pampers mai 12 ta siya ta farka ledar ta ciro daya ta fara sanya mata kana ta shirya ta cikin kayan data siyo, turaren ta dake cikin locker ta dauko ta ɗan fesa wa little Amnah kadan, tayi kyau sosai, ta sabe ta a kafada kana ta yi saurin harhada kayan ta Cikin ledar data yi siyayya a ciki ta fito, ta ga Maleek tsaye yana ta safa da marwa wani sai ya dauka ko mara lafiya ya kawo dake Cikin matsanancin halin ciwo, nan kuwa Rashin fito masa yarsa ne ya dame shi.
Yana ganinsu ya saki ajiyar zuciya, itama little ta fara daga masa hannu, ya nufi wajen su, ya karbe ta yana murmushi.
Bakinsa na fadin “thank you”
Cikin jin dadi tace “it’s my pleasure nace ko kai ma za’a samo maka riga ka sanja ne” ta fada tana kallon farar rigar sa daya dan yi dabbare da launin kasa, yace “I’m okay karki damu”
“Okay, ga kayan ku”
Ya girgiza kai yana fadin “dash it to somebody ko ki zubar” ya fada yana sumbatar kumatun little Amnah.
Ya lalube aljihun sa ya fiddo da dubu ashirin yace “ga wanna, manage it ki saka kati, ban fito da kudi ba” yana fadin haka ya nufi hanyar barin asibitin”
Takaici, haushi, kuka duk yazo wa nurse Safiyya a lokaci daya amma ta danne ganin all eyes are on her, iya abinda zai ce mata kenan? ita da take tunanin ta siye zuciyar sa da wanna uban hidiman ɗata masa, dama lambar ta ya karba daya fiye mata kuɗin nan daya bata ko ya furta yana son ta, domin tafi bukatar hakan, jiki a sanyaye ta nufi wajen zaman ta.
Maleek dake daf da isa Company’n sa ya ji wayarsa na ringing, amma bai duba ba bare ya ɗauka, domin da hannu daya yake tuki dayan hannun kuma na rike da bayan little Amnah data yi bacci.
Mafi yawancin Ma’aikatan sa da suka fito waje domin alwala suka cika da mamakin ganin boss din su rike da yarinya, da suna da iko da sun tambaye shi ina ya samo wanna kyakkyawar yarinyar, gaisuwar ma sama sama yake amsa musu ya nufi office ɗin sa.
Bayan ya shiga ya nufi dakin hutawar sa, a hankali ya kwantar da little Amnah kan sofa yana sumbatar goshin ta.
Ya nemi gefen ta ya zauna, ya zuba Mata idanun sa, tunanin abubuwa masu yawa da suka shude na zuwa ƙwaƙwalwar sa.
Karar da wayar sa ta kara yi a karo na ba adadi ya sanya shi dubawa sai ya ga Shakur ne, ya dauka ya kara a kunnen sa ba tare da Yace komai ba.
“Maleek ina kake haka ne ina ta kiran wayar ka?”
“Office” ya amsa a takaice
“Where’s little Amnah?”
“She’s fine” ya amsa.
“Toh alhamdulillah, Please ka mayar da ita wajen maman ta” Shakur ya fada masa.
“Ta gama zama a wajen ta” Maleek ya fada kansa tsaye.
“Ban gane ba, what did you mean?”
“You heard me right Shakur, angel bazata koma wajen ta ba, and that’s final”
“Ka fara ko Maleek, meye ma’anar hakan?”
“Kasan yanda na samu yarinyata kuwa? Kamar wata marainiya ita kadai a waje, ka…”
” Na san abinda ya faru, amma bada gangan tayi ba, she slept off lokacin ne”
Haushi ya kara kama Maleek yace “bacci! Kace bacci? Wani irin bacci? ita jaririya ce da har yarinya zata bar gaban ta ta fita waje bata sani ba, this is unbelievable” ya faɗa Yana dafe kansa.
“Toh ka mayar da ita, ina marking test din Dalibai yanxu, idan na dawo zan muyi magana” Shakur ya kara fada masa a hankali.
“Na fa ce maka bazata koma gidan can ba”
Cikin jin haushi Shakur yace “Toh yarinyar fa bazata sha abincin ta ba, kasan ba wani son madara take ba, a haka kake cewa kanason ta zaka barta da yunwa bayan da Mahaifiyar ta a raye”
“Da kaina zan dinga kula da ita, i don’t mind na daina zuwa Companyn nan har tayi wayo ta fara school, barin gaya maka wani abu, wallahi da wani abu ya samu yarinyar nan dana kai yarinyar can ƙara bayan na mata nawa hukuncin, a lokacin ban damu su Daddy su san sirrrin dake boye ba”
Shakur ya mike daga kujerar da yake zaune, ya dauki mukullin mota ba tare da ya gama abinda yake yi ba, domin ya ga abin na Maleek da gaske yake.
*Munaya*
Tun tana kuka sosai har ta yi shiru tana sauke numfashi ga lokaci sai ja yake, wani iri take ji a jikin ta kamar zazzaɓi, ko motsa wa bata son yi saboda ruwan mama ya cika kirjin ta sai ciwo suke mata, a hankali ta janyo bargo ta rufe har kanta.
Ta janyo wayarta ta ƙara kiran Shakur, bayan ya daga tace “ya Shakur har yanzu bai kawo ta ba, idan Mami ta dawo wani amsa xan bata idan ta tambaye ni” ta fada tana fashewa da wani sabon Kuka.
Shakur da ko AA DAWOOD MOTORS bai karasa ba amma domin kwantar mata da hankali yace “gamu nan za’a kawo ta yanzu, kwantar da hankalin ki kinji, idan barrister ta dawo kafin mu karaso just tell her ni na fita da ita”
“Toh ya Shakur” tace tana cire wayar daga kunnen ta, ta lumshe idanun ta.