Hausa NovelsNihaad Complete Hausa Novel

Nihaad 69

Sponsored Links

💖 NIHAAD 💖

69

Mami tayi shiru tana sauraron Janar jin ya fusata sosai, ya ci gaba cikin fada yana cewa “Me yasa tun farko basu kawo wannan batun ba sai yanzu da lokaci ya kure? Why will they say this just a week to the wedding? Dama ita uwar yarinyar kadai ta shirya abunta ta hada mu da masu amsan kudin auren yarinya ba tare da sanin dangin ubanta ba, me yasa ku mata ku ke da karancin tunani ne wai?” Mami tace “Haba dai ranka shi dade, aminin babanta ne fa, babanta ba shi da kamarsa har ya bar duniya, tun a yemen suka san juna suka kuma ci gaba da zumunci har a nan, yau ko da uban Nadeeyah na da rai ina tabbatar maka shi wannan Alhaji Mashkur din ne zai daura ma Nadeeyah aure ba shi, dama tun asali dangin uban basu son Hajiya Safeenah saboda Ubanta bafillatanin Nigerian ne uwarta ce er kasar yemen kaga ai ita bafullatana ce, bayan ubanta ya rasu kuma mahaifiyarta ta koma yemen da ita, kawai dai suna son daga ma Hajiya Safeenar hankali ne shi yasa suka billo da batun zuwa yemen gun dangin Baban Nadeeyah, me yasa tun da aka sanar da su zancen auren basu ce haka ba sai da lokaci ya zo, they knew nothing about the girls wellbeing, neman magana ne kawai, don haka kayi hakuri tunda har sun ce a kara dagawa ai sai a daga din a bi komai a sannu babu gaggawa, ayi making preparations na zuwa can Yemen din…..” Janar yace “Fatima” Mami tace “Ina jin ka” Yace “A dai nan kwana kusa daga sati daya har zuwa sati biyar masu zuwa bani da time din zuwa Yemen to be frank with u, i am occupied, nayi scheduling duk kwanakin nan, i don’t have time, wait ma dai tukun, idan ba rainin hankali ba ni me zanje yi masu a yemen, shi da yake neman mata a can ai sai ya shirya yaje ya gaishesu, ni me zan je in masu?” Mami ta girgiza kai tace “Aa mu ba haka ake a wajen mu ba gaskiya, da shi me neman auren, da ubansa, da kawun uban nasa ne za ku je gaishe da dangin uban yarinyar, kai har ma da dangin uwarta ko da a wani gari suke” Janar yace “I see” Mami tace “Ka daina duba cewa ai shekaru 36 da suka wuce baka je can neman nawa auren ba, kar ka manta a hannun wan mahaifina nake a kasar nan a wancan lokacin, you just have luck sai bayan da aka yi aurenmu sannan suka koma can din gaba daya, banda haka da dole ne sai kaje wallahi” Yace “To a sannan ina naga kudin zuwa Yemen?” Murmushi kawai Mami tayi, sai kuma tace “Da da kudin ma ai danginka baza su bari kaje ba tunda ba sona suke ba” Janar yace “Let me pick a call” Daga haka ya katse wayar, Mami ta sauke wayar daga kunnenta tana tunanin ta inda zata fara convincing dinsa yaje gaida dangin uban Nadeeyah, kallon agogo tayi ganin karfe uku ta mike da sauri ta shiga daki don tada Nihad ta shirya su tafi airport, suna gama shiryawa ta kira Hajiya Safeenah ta sanar mata ga su za su tafi airport, Khalil ya bi Mami da kallo babu ko kiftawa, ta tafi ta dau Handbag dinta ganin kallon da yake mata tace “Kana kallona haka, idan kuma in bar ka da ita ne to sai in bar ka ba sai naje ba, amma kada ka kuskura in ganka a US ko a mafarki wallahi” Ita dai Nihad ta sa Hijab dinta Mami ta saka ta a gaba suka fita daga dakin suka barsa nan tsaye kamar statue. Khalil na zaune gaban motar Mami, ita kuma tana back seat tare da Nihad suka iso airport, suka tarar da Hajiya Safeenah har ta isa airport din da wata er uwarta, Hajiya Safeenah kadai Nihad ta gani ta dauke kai cikin dubara ta kuma ki sauka daga cikin motar, Bayan Mami sun gaisa da er uwar Hajiya Safeenah tace “Ina Nadeeyah, tana gida ne” Hajiya Safeenah tace “Aa tare muke, ta hadu da wata Coursemate dinta ce, mun baro su can suna gaisawa” Mami tace “Allah sarki” Khalil ya zagoya ya gaida Hajiya Safeenah da sister dinta suka amsa da fara’a, Hajiya Safeenah tace “Ya me jiki? Tana ma ina ban ganta ba” Mami ta bude motar tana kallon Nihad da ta makale ciki, sai ta fara kokarin saukowa daga motar Mami tace “Aa zauna ba sai kin fito ba” Hajiya Safeenah na kallon cikin motar tace “Sannu kin ji, Allah ya sauwake, ya baki lafiya” Nihad ta sunkuyar da kanta tace “Ina yini” Hajiya Safeenah tace “Lafiya lau daughter, Allah ya baki lafiya kin ji” Ita dai Nihad bata ce komai ba, sister dinta ma tayi mata fatan samun lafiya, daga nesa Nihad ta hango Nadeeyah na tahowa haka kawai taji gabanta ya fadi, ta dai dauke kai daga kallonta har ta iso inda suke, Nadeeyah ta gaida Mami da ladabi, Mami tace “How are you dear” Nadeeyah tace “Alhamdulillah, ya me jiki?” Mami tace “Jiki Alhamdulillah” Hajiya Safeenah ta koma gefe tare da Mami tace “Kinga ko da dangin Mahaifin Nadeeyah basu tado da zancen aje can a gaishesu ba ai dole za a daga bikin nan har Allah ya ba takwararki lafiya Hajiya” Mami tace “Toh yanzu na dai fara ma Janar magana amma bamu gama ba gaskiya” Hajiya Safeenah tace “Aa da baki masa maganan yanzu ba ma, har sai Fatima ta samu lafiya, lafiya ai yana gaba da komai Hajiya” Mami tace “Haka ne” Nadeeyah na kallon cikin motar da Nihad take, har sannan da murmushi fuskarta ta ɗan saka kai cikin motar cin sanyayyen murya tace “Hi, ya jikin, hope u are feeling much better” Nihad ta ɗan kalleta, sai kuma ta mata wani kallo ta dauke kai ta tsuke fuska tana kallon daya side din, duk Khalil na kallonsu but sai yayi saurin kauda kansa, Nadeeyah ta bar jikin motar ta tsaya a gefe, gaba daya jikinta a sanyaye, Khalil dai bai yarda ya kalli inda take ba, duk da yana son mata magana amma ya kasa saboda Nihad, wanda ita ma sai kallo take taga ko zai mata maganan, Mami da Hajiya Safeenah suna gama maganar da za su yi aka yi Conveying din Mami da Nihad zuwa Lounge din da zasu jira har karfe hudu da rabi kafin tashin jirginsu, har zagawa Khalil yayi zuwa daya side din mota kafin Nihad ta sauka zuwa Lounge yana mata magana amma ta maka masa wani harara ta ki kulasa ta sauka Mami ta saka ta gaba suka wuce, ya kalli Nadeeyah da har ta koma gun motarsu tana jiran Mum dinta da Aunt dinta su karaso, yana kallon Drivern Mami yace “Bani makullin mota, ni zan dawo da shi gida” Sojan zai yi magana Khalil ya ciro wayarsa yayi dialing number Mami ya sa handsfree tana dagawa yace “Mami zan fita da motar ki” Mami tace “Ohk” Bai sake kallon Sojan ba ya cire Makullin jikin motar ya kulle, ya nufi motar su Nadeeyah, haka nan convoy da suka kawo Mami suka juya suka bar airport din leaving Mami’s Ride behind. Khalil na kallon Nadeeyah yace “Mu je in ajiye ki gida” ba tare da ta kallesa ba tace “Nah don’t worry za mu koma tare da su Mum” Aunt dinta ta kalleta tace “Ki je mana” Ita dai Hajiya Safeenah bata ce masu komai ba, Nadeeyah ta langwabar da kai tace “Na riga na shiga nan ne Aunty” Khalil yace “Ohk then, later” Ta gyada masa kai, Yayi ma su Hajiya Safeenah sallama ya juya ya koma gun motar Mami, Drivernsu ya ja motar suka bar airport din.
Umma ce zaune dakinta da ta kulle da makulli tana waya kasa kasa tace “Na gaya maki tun ranan har yau… kin ga dai kusan sati uku kenan ko to ban sa shi a ido ba, iyaka duk wani expenses na kudin magani da kika sani shi ke badawa bai taɓa cewa Aa ba, dama Farooq ne ke kai ni asibiti tun da ya koma bakin aikinsa sai Kamila ta rakani idan ta ga dama, wani lokacin da Amina nake zuwa….” Tana magana hawaye na zuba idonta, ta ci gaba tace “Usman kuma ai na gaya maki sati biyu kenan da ya fita Nijar yana buga bugansa a can, Turai duniyar ta min zafi, ji nake kamar zuciyata zata iya fashewa a ko wani lokaci, ga Kamila babu zancen komawa dakinta mijin har yayi wani auren, Ɗan nata guda daya ma ya amshe ya kai ma uwarsa, Nihal da nake sa ran wannan ɗan ministan zai aureta tace min basa tare ai yanzu, da na tambayeta waye kuma a kasa yanzu sai tace min babu kowa, to ina lafiya Turai? Gashi yau kusa da wata uku kenan gata nan gata nan ne dai kawai kamar ba Nihal dita ba, har da wannan sauyin nata ke damuna yanzu haka, sannan da na tuna Nihad ga gidan da fa take aure sai naji zuciyata kamar ta tsinke, Turai kinsan bani da komai kuma yanzu balle a ci gaba da neman taimako, zoben nan guda daya ne kawai ya rage min, ta ina zan fara Turai?” Turai tace “Sumayya ki kwantar da hankalinki kada kije damuwa ta sa maki ciwon zuciya, iya laluran hawan jinin da kika samu a kwanan nan ma ya isa haka, in sha Allahu komai zai dawo dai dai Sumayya, yanzu abinda zai faru zan aiko Fa’iza ta amsa zoben in siyar in je can Zaria gun malamin da ya fara mana aiki shekaru takwas da suka wuce, kince saki daya Alhajin ya maki ai ko?” Hawaye na sauka idon Umma tace “Ehh” Hajiya Turai tace “Toh babban abinda za a fara aiki a kai yanzu shine duk yanda za abi Alhaji ya maida ki dakinki, bayan ya maida ki sai a koma kan Nihad….” Da sauri Umma tace “Wacece Nihad, ga matsaloli kaca kaca a gabana kina kira min Nihad Turai, bayan dai an maida ni ayi kokarin duk yanda za ayi Kamila ma ta koma dakinta wallahi sai kinga rashin darajar da take min a gidan nan yanzu, bata ma damu da halin da nake ciki ba, dazu da safe ke kyace dukana zata yi daga nace tayi kokari ta rage baccinta ta dinga tashi tsakar dare tana gaya ma Allah matsalolinta, Turai bata da aiki yanzu sai waya da manyan mata wanda ko ni sun fi karfina, kusan kullum sai ta fita ta dawo da kayan ciye ciye tace Hajiya wancan ce ta bata ko tace Hajiya wancan ce ta bata, har iphone ta dawo da shi gidan nan wai macece er uwarta ta bata, idan ta fita tun safe sai dare take dawowa fa wllh, ke dai kinsan irin tarbiyan da na basu Turai ko nan da gate idan ba kwakkwaran dalili ba bana barin su fita, duk wani sa ido da uwa zata ma ‘ya yanta na masu bakin gwargwado Allah kuma ya gani, to wani hali ne wannan kuma Kamila ta tsiro da? Wannan ai ba tarbiyata bane, tsorona ma kada taje su sakata harkan lesbian, da farko ne mutuwar auren ke damunta har ta rame ta fita hayyacinta amma yanzu kam manyan mata kawai take bi Turai, shine hankalina ya kara tashi wllh, sannan sai a koma kan Nihal ita ma ayi duk kokarin da za ayi ɗan ministan nan ya dawo ace yau ita ma tayi aure tana dakinta Turai, sannan Usman shi ma Allah ya taimakesa ya samu wani aikin ko da ba na Abujan ba, wallahi yana cikin damuwa shi yasa ma ya fita Nijar ba dangin uwa ba na uba a can, kinsan yanda samun aiki yake a kasar nan idan ba kasan wanda ya san wani ba, Amina ma ayi addu’a Allah ya fiddo mata da miji wllh babu me zuwa wajenta abun har tsoro yake bani, hatta Hafsat din nan me aiki ana zuwa zance wajenta amma banda Aminata, abu na karshe wannan yarinyar Husnah a yi duk me ma za ayi kada Allah ya kara kado ta gidan nan don girman Allah, wllh wannan su ne babban matsalolin dake gabana a yanzu dai Turai, da su nake kwana nake tashi” Hajiya Turai tace “Duk kar ki ji komai zan aiko a amshi zoben, idan ma da ciko ni zan maki wallahi don kin fice haka a wajena Sumayya, banda rashi ai da ba sai nace ki bada zobe ba ni me maki ne ko da miliyan zan kashe, to bani da shi bani da dalilinsa Sumayya” Umma tace “Allah ya rufa asiri ni dai ki min kokari Turai, bani da me min wannan abun banda ke” Nan suka yi sallama Umma ta ajiye wayar ta jingina da gado abun duniya ya taru ya mata yawa, duk ta rame tayi baƙi babu kyan gani. Kwankwasa kofar dakinta aka yi tace “Wanene?” Amina tace “Ni ce” Umma tace “Ya aka yi? Ba nace kada wanda ya shigo min nan ba ina bukatar hutu” Amina tace “Nihal ce zazzaɓin ya sake dawo mata Umma” Umma ta sauka daga kan gadon da sauri ta tafi ta bude kofar tace “Tana ina?” Amina tace “Can dakinta” Umma tace “Tun yaushe zazzaɓin ya dawo?” Amina tace “Abinci ta ci, sai tace cikinta na ciwo sosai daga nan kuma sai amai” Umma tace “Wannan yarinya wannan yarinya da shegen taurin kai take, nace mu je asibiti taki to ya zan mata, tana ta zazzaɓi a tsattsaye yaki ci yaki cinyewa me maganin Chemist zai mata fisabilillahi” Suna isa dakin Nihal suka tadda Mumy zaune gefen gadon tana mata sannu, Umma tace “Me yasa kin fiye taurin kai ne Nihal, nace aje asibiti su maki treatment me kyau kin ki, to ya kike son inyi dake?” Mumy tace “Nima yanzu maganan da nake mata kenan, nace ta shirya mu je asibiti wai sai ta huta” Ko kallonta Umma bata yi ba don tun bayan da Abba ya saketa ta daina kula Mumy a gidan, ko taje dubata a can ɓangarenta duk sannun da zata mata ba um ba um um sai dai tayi ta sauke ajiyar zuciya, Umma tace “Tashi sa Hijabinki mu tafi asibiti” Nihal ta daga kai ta kalleta da kyar tace “Toh a bari anjima mana Umma” Umma tace “Anjiman ubanki, kin tashi kin shirya ko kuwa, dubi yanda kika lalace kamar warce ta shekara tana zazzabi” Mumy dai bata sake ce masu komai ba, Nihal ta mike zaune cike da karfin hali tace “Don Allah ki bari Anjima Umma wllh bacci nake ji kuma yanzu” Umma tace “Toh tashi ki koma bangarena ki kwanta” Nihal ta tashi tsaye ta fita daga dakin, Umma da Amina suka bi bayanta, ta koma dakin Nihad dake bangaren Umma ta kwanta, Umma na kallonta tace “In kin tashi daga Baccin sai Amina ta raka ki asibitin, ko dai kin ji za a sakar maku result ne a makaranta, tunda ke haka kike da kinji za a saki result kin fara zazzabi ba ji ba gani” Nihal ta gyada mata kai da sauri tace “Ehh” Umma tace “Ko da naji, to Allah ya sa a ga alkhairi” Daga haka ta juya ta koma dakinta. Karfe biyu da rabi na ranan Nihal ta shigo dakin Umma, Umma na zaune kan darduma rike da carbi, tun da ta idar da sallahn azahar wajen karfe daya da wani abu take zaune saman darduman take ta jan carbi, da taji hawaye ya zubo idonta sai tayi sauri ta goge, Nihal ta zauna gefen gadonta, Umma na kallonta ganin yanda ta rame tace “Anya baza kije asibiti a maki thorough Checkup ba Nihal? Kin ga yanda kika koma kuwa?” A hankali Nihal tace “Toh ba final exams bane da muka yi Umma” Umma tace “Toh naga ramar tayi yawa ne, and u look pale” Nihal tace “Umma zan je gidan Coursemate dita dake rijiyar zaki, ita zata duba mana result din ni bazan iya ba” Umma tace “Har an saki?” Nihal ta gyada kai a hankali tace “Eh” Umma tace “Toh Allah ya baku sa’a, ya baku nasara ya rabaku da spill over” Nihal tace “Ameen” Umma ta jawo jakarta ta ciro dubu daya daga cikin dubu sha biyar din da Farooq ya bata kafin ya koma aiki, tace “Ki rike wannan a hannu, ai driver ne zai kai ki ko?” Nihal ta gyada mata kai ta amshi kudin sannan ta mata godiya ta mike ta fita daga dakinta sai da ta fara zuwa bangaren Mumy ta sanar mata zata fita sannan ta bar gidan, Raliya Coursemate dinta ce kuma zata girmeta da kusan 4 years amma ko sau daya bata taɓa zuwa gidansu ba sai dai Raliyan ta zo wajenta, duk da dai sai a level 4 ne ma suka saba da ita har ta zo gidansu, bata da wata kawa da take zuwa wajenta a kaf garin kano, yawanci ko yan islamiyyarsu sai dai su zo gida wajenta amma ita kam bata xuwa, Suna isa kofar gidansu Raliya ta kirata a waya tace “Ina kofar gida” Raliya tace “Anya kin gane address din da na tura maki kuwa Nihal?” Nihal tace “Toh ai driver ne ya kawo ni” Raliya tace “Toh gani nan fitowa, Allah ya sa ba wani wajen daban ku ka je ba” Sai ga Raliya ta bude gate din gidansu, Nihal ta sauka daga motar tana kallon drivern tace “Kawai ka tafi idan na gama zan kiraka baba” yace “Toh Hajiya” Daga haka ya ja motar ya bar layin, Raliya ta rungume Nihal cike da farin cikin ganinta tace “Ya naga sai kara ramewa ma kika yi maimakon ki ciko da kika koma gida” Nihal ta mata murmushi kawai, Raliya ta kama hannunta suka shiga cikin gidan nasu, babban gida ne sosai, sai da Raliya ta fara kai ta ta gaida Mum dinta da Stepmom sannan ta tafi dakinta da ita, Nihal ta zauna gefen gadonta, Raliya tace “Kinji result nan da sati biyu za a saki?” A hankali Nihal tace “Allah ya kai mu” Mai aikinsu Raliya ta kawo mata ruwa da small chops, Raliya tace “Naji dadin ganinki wallahi, dama baki taɓa zuwa gidanmu ba sai dai ni in je naku, to yau dai ga ki a gidanmu and i really appreciate it” Nihal tayi murmushi amma bata ce komai ba, Raliya tace “Na gan ki wani iri, ko baki da lafiya ne dai Nihal?” Lokaci daya hawaye ya kawo idon Nihal, Raliya ta koma gefenta ta zauna da mamaki tace “What’s wrong dear?” Bayan few seconds Nihal tayi karfin halin cewa “Ni bani da kawa, and i have no one to confide with, kawai naji na yarda dake Raliya, For two months now…. ban ga period dina ba Raliya” Raliya was shocked ta koma baya ta dinga kallon Nihal tsoro fal idonta, a kaf department dinsu babu mutum da kana ganinsa zaka masa kallon holy somebody kamar Nihal, ita ko magana da maza ma bata yi sai taga dama, sannan bata shigar banza ko da bazata sa hijab ba bazaka taɓa ganinta da karamin gyale ba sai dai babba da zai rufe jikinta, sannan she is one of the loveliest soul da ta taba haduwa da warce bata san walakanci ba, abunta bai rufe mata ido ba sannan ga ta da tausayi, Raliya ta sauka daga kan gadon tana kallon Nihal still shocked tace “Ban gane ba Nihal? What are you trying to say now?” Kuka sosai Nihal take kamar ranta zai fita tace “Kin dai san halina duk da bamu wani dade tare ba Raliya, even male frnds i don’t keep, wallahi wallahi wallahi ni ban taɓa zina ba….” Sai kuma ta kasa ci gaba ta hade kai da gadon Raliya tana kuka sosai, cikin rawar murya tace “I wish Allah zai dau rayuwata yanzu, Allah ne shaidata ni ban taɓa zina ba, i was betrayed Raliya, yaudarata aka yi….” Raliya tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, amma don baki ga period ba ai u don’t have to conclude u are pregnant wani lokacin period na haka, ko nima last 3 months sai da nayi kusan wata biyu banyi period ba daga baya sai gashi ya zo, do not conclude Nihal” Nihal ta girgiza kai tace “Ni ban taɓa yin haka ba” Raliya ta ma rasa abinda zata ce mata don gaba daya kanta ya kulle, can tace “Abinda zai faru, ki tashi yanzu mu je mu siyo Pt test strip a chemist kiyi amfani da shi don mu tabbatar” Nihal ta goge hawayen da yaki tsaya mata cikin rawan murya tace “Toh” Raliya ta dau hijab dinta bayan ta je ta gaya ma Mum dinta za su je siyo abu su dawo ta fita tare da Nihal, ba a chemist din unguwansu ta siya ba sanin halin jama’a, sai da suka bar anguwan kwata kwata sannan suka samu wani chemist suka siya, Raliya ta tare masu ɗan adaidaita ya maida su gida, ba Nihal me test din ba, ita kanta Raliya gabanta faduwa yake sosai, ta dinga addu’a a zuciyarta Allah ya sa negative za su gani, ai ko Nihal na gama dubawa suka ga positive, Raliya was so shock ta zauna gefen gadonta ta kasa cewa komai, kuma bata hana Nihal kukan da take ba kamar zata shide, Raliya ta dinga tunanin wani taimakon zata iya ba Nihal wanda asirinta bazai tonu ba, gashi dai ita kanta ba wai idonta a bude yake ba, tana dai cin life amma gaskiya bata shashanci, wata kawarta warce tasan duniya, duniya ya santa ce ta fado mata, ta kalli Nihal cikin sanyin murya tace “I have this friend Zaliha nasan zata hada mu da Dr da zai cire cikin….” Ko rufe baki Raliya bata yi ba, Nihal ta dago da sauri ta girgiza kai hawaye na sauka idonta cikin rawar murya tace “Bazan cire ba, laifi biyu a lokaci daya Raliya?” Raliya tace “But kin ce yaudaranki aka yi Nihal, koma laifin ne astagfirullah sai dai daya na cire ciki amma ba na zina ba since yaudaranki aka yi” Kuka Nihal sosai take kamar ranta zai fita tace “Baxan cire ba, i can’t” Raliya ta zaro ido da mamaki tace “How did u want to face ur parents with this Nihal?? So kike ki sa masu heart attack? Ya kike son mahaifiyarki tayi? Ta yaya zaki fuskanci mahaifinki idan aka gano wannan cikin? Ohh no think about this plss” Kuka kawai Nihal take ta ma rasa abinda zata ce ma Raliya amma ita dai tasan bazata taɓa cire cikin nan ba Allah yayi fushi da ita, cire cikin will be the last thing she will do on earth, Raliya tayi tagumi duk ranta babu dadi, this is so sad, bayan few seconds tace “Since ni dai baza ki dauki shawarata ba, don’t you have any other person that u can confide in, ko namiji ko na mace wanda u are close with kiji shawaran da zata baki ko zai baki??” Nihal tayi shiru tana goge idonta tana nazarin who will that person be…..

Related Articles

*Manage this pls, bana jin dadi ina mura*

Nihad is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button