Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 7

Sponsored Links

*YANCI DA RAYUWA*

©® Hafsat Rano

Page 7

Related Articles

****

“Gate man ne.”

“Gateman?” Ta maimaita sai kuma ta zare lock din kofar tana dan lekawa kadan

“Oga Refeeq ne yace a kawo miki.”

Ledar hannun nasa ta kalla sannan ta maimaita sunan Rafeeq din akan leben ta. Sake miko mata yayi sai ta karba sannan tayi godiya ta rufe kofar cike da mamaki. Zama tayi a kasan dakin sannan ta bude ledar mamakin ta ya karu ganin kalar abinda ke ciki. Naan bread ne da curry sauce sai Chinese rice da shredded chicken. A hankali ta fito da komai ta zuba wanda ztaa iya ci ta ajiye sauran ta zauna taci sosai tasha ruwa sannan ta koma ta zauna tana tunanin dalilin kawo mata abinci da yayi, tunowa da tayi mutumin dazu da sukayi karo har abincin ta ya zube yasa ta gano dalilin sa kenan. Dadi sosai taji mara misaltuwa karo na farko da wani ya nuna mata tsantsar kulawa bayan mahaifin ta da Hajiya Maryam. Addua tayi masa sannan ta kwanta lamo har bacci yazo ya dauke ta.

***A falon farko ya samu Aneesa a zaune tana cin milk cake yana shigowa tayi saurin ajiyewa ta mike ta soma kwalawa Mummy kira da karfi

“Keee.” Yace yana murmushi

Da sauri tayi kansa da gudu ya kauce yana sakin dariya kadan.

“Ba zaki girma ba wai?” Yace yana kallon yadda ta cika da farin ciki.

“Yaah feeqq sai yanzu zaka zo?”

“Nayi laifi, I’m sorry. Wani abu ne ya rike ni.”

“Ni dai nayi fushi, sai da kowa ya zo ana jiranka Ya Asim yace wai ka wuce wani waje.”

“Ayi min afuwa kinji? Ina Mummy.”

“Tana ciki, muje na rakaka.”

Da sauri ta kama hannun sa ya kalle ta, ta sakar masa murmushi sai kawai ya kyale ta suka jera zuwa part din Mummy din wadda take tsaye tana waya cikin fushi da bacin ran wulakancin da Rafeeq din yayi mata. Shigowar su yasa ta katse maganar da take yi ta kuma kashe wayar gaba daya tana maida kallon ta kanshi har suka karaso gabanta sai ya zame hannun aneesan daga cikin nasa sannan ya durkusa kasa cikin girmamawa yace

“Mummy barka da gida, mun same ku lafiya.”

Danne abinda yake ta taso mata tayi, cikin dakewa tace

“Lafiya kalou kamar yadda kake gani, sai yanzu kaga damar zuwa in da nake ko?”

“A ah Mummy, ayi min afuwa wani babban uzuri ne ya taso min .”

“Saboda kai ne agogo sarkin aiki, kuma ka ki daukar waya daga baya ma ka kasheta gaba daya, hatta mahaifin ku sai da ya kira amma baka dauka ba.”

Shiru yayi still yana kasa yana kallon zanen carpet din dakin yana Jin ta har ta gama sababin, kafin tace

“Ba zaka ce komai ba ko?”

“Ayi hakuri.”

“Yayi, ya hanya ka dawo lafiya?”

“Lafiya Alhamdullillah.”

“Toh Masha Allah, gwara da ka dawo ai, ayyukan sunyi ma kanin ka yawa yana bukayar taimakon ka.”

Da fada kamar da gatse

“Tunda na dawo yanzu zan yi taking over komai, zai samu saukin aikin.”

Yace mata yana murmushi kasa-kasa. Bata fuska tayi jin amsar da ya bayar, ta wuce gaban gado ta zauna tana dauke kanta daga kallon sa saboda wani irin mugun chanjawa da yayi, yayi wani irin fresh da wani irin kyau da kwarjini. Mikewa yai, yayi mata sallama ya fice ta raka bayan sa da kallon banza sannan taja tsaki yana Jin ta sai kawai ya girgiza kai yana sake murmusawa ya wuce zuwa part dinsa.

***Kasancewar ta yi matukar gajiya yasa har ta so ta makara da safe ta tashi a firgice tana salati ganin yadda time din ya tafi, gashi yau ne zatayi last paper dinta ga aikin gidan gashi ba wani ma karatu tayi sosai ba. Sallah kawai tayi da brush ko wanka bata tsaya yi ba, ta zura uniform din sannan ta dora hijab da nikaf din ta fito zuwa kitchen. A gaggauce tayi aikin tana yi tana kallon lokaci gashi abubuwan da suke bukata a safiyar yau din masu yawa ne fiye da kullum gashi ita kadai ce ba mataimaki. Tana cikin aikin ne Ben ya karaso suka gaisa sannan yayi mata introducing wata Igbo girl yace zata dinga taimaka mata in ji Hajiya idan ta haye screening din za’a dauke ta parmanently tana taimaka mata. Taji dadi sosai nan da nan tasa hannu ta tayata tana nuna mata yadda zatayi komai a tsaftace kafin kace me sun gama ta kwashi komai suka jera akan Island sannan Ben yazo tayi tasting kamar yadda ta saba ta dauki nata ta fito ta barsu tare da yarinyar. Bata zauna zaman cin abincin ba, ta rufe kawai ta cire hijab din ta dauki jakarta da ragowar chanjin ta, ta fice a gurguje tana ta sauri. A gate me gadi ya tsaida ta bayan sun gaisa ya dan matso kusa da ita sosai sannan yace

“Menene oga ya kawo miki jiya da daddare?”

“Naam?”

“Ehen? Dama kin san oga ne da zai kawo miki abinci? Tun jiya nake ta tunanin abun nan fa, akwai mamaaki.” Yace cikin gurbattaciyar hausar sa

“Bansan shi ba wallahi.”

“Toh you have to be very careful, shine first born na gidan nan gaba daya, Second big Oga da ya dawo jiya daga oversee, shine. If big madam suspect anything tsakanin ku, that’s the end of you.”

“Wallahi ba komai a tsakanin mu, dan Allah karka fadawa kowa abinda ya faru.”

“Wa ni? Bazai fada ba fa, idan na fada da nine Hajiya zata hada ta yi sacking namu gaba daya.”

Ya kama bakin sa ya rufe yana yarfe hannu. Jiki a sanyaye ta bar gidan ta bi gefe sosai ta chanja hanya gaba daya saboda tana son gujewa haduwa da Asim. Hanyar da ta bin tafi tsawo sosai dan haka ne yasa ta sake makara sosai sanda taje har an shiga exams din ta roki malamin su ya barta ta shiga duk da haka sai da aka hana ta exams sheet har sai da tayi ten minutes a tsaye sannan ta zauna ta fara answering tana adduar samun nasara.

***Yaye soft white duvet din da ya rufa dashi yayi ya sakko da kafafun sa ya zauna sosai akan gadon yana lalubar wayar sa ya bude ta. Duk wasu bayanan da yake bukata Saddam ya tura masa ta mail abu daya ya rage ya gano in da suke a yanzu daga nan zai yi duk yadda zai yi yaga ya dawo musu da abinda suka rasa ta dalilin sa duk da su basu san ma yana existing ba.
Mikewa yayi gaba daya ya wuce toilet ya sakar ma kansa ruwa sosai ya dade a ciki dadi da dan zafin ruwan na ratsa shi sumar kansa sosai, sannan ya dauro bathrobe ya fito ya hau shiryawa a tsanake. Suit dark ash da white long shirt ya saka da ash cover shoe ya daura neck tie ya fito sosai a shirin sa na zuwa first meeting dinsa da dukkanin stakeholders na companyn su both internal stakeholders da external din. Jirgin karfe bakwai Asim ya hau dan haka karfe takwas da wani abu yana gida yana shigowa Rafeeq din na fitowa da sauri suka rungume juna cikin matukar farin ciki.

“Welcome back bro, ya hanyar?”

“Lafiya lou, karfe nawa ka baro Kano?”

“7 daidai muka taso, bana so nayi missing first meeting din nan tare da kai.”

“Gashi yanzu na shirya ni, ko zamu hadu a chan?”

“Eh kar na tsaida ka, zan biyo bayanka nan da 30min, tunda sai 10:30 za’a zauna.”

“Ok,sai ka karaso.” Ya bugi bayan sa ya fice shi kuma ya shige ciki.

Su Saddam na zaune suna jiran sa yana fitowa suka taso da sauri duk suka russuna suka gaishe shi ya amsa yana kallon gate din gidan kafin ya zura kafar sa cikin motar yana katse tunanin da yake kokarin taso masa.

“Chan zamu fara zuwa sir?” Saddam yace bayan sun fito daga street din gidan. Daga masa kai yayi yana kokarin amsa kiran AJI da ya shigo wayar sa.

“Barka da safiya AJI.”

“Barka dai, kaga damar daukar wayar tawa ko?”

“Ayi hakuri.”

“Aikin ka kenan, ka bata ma mutum da gangan ka hanashi magana kuma da ban hakurin ka, kana ina yanzu?”

“Yanzu na fito zan tafi office.”

“Toh madallah, nasan ka bana jin ka, kayi abinda ya dace idan ka dawo ka same ni a gida bayan magriba.”

“In sha Allah.”

Bayan sun gama wayar ya ajiye ta sai ya maida kallon sa zuwa ga waje yana kallon yanayi da tsarin garin. Daga nesa sosai da gate din makaratar yasa sukayi parking, yana zaune yana duba lokaci har suka dauki kusan awa a zaune suna jiran tsammani, yana ji a ransa tabbas zata fito, in dai har tana zuwa school din har yanzu dole tana cikin masu yin exams din a yau wadda Saddam ya tabbatar masa itace last paper din su, baya so wannan damar ta wuce masa dan itace last hope dinsa akanta.

“Sir saura 30min a shiga meeting din.”

Kin magana yayi, ya cigaba da kallon hanyar kamar wanda idan ya dauke kallon sa zata zo ta wuce. Shiru Saddam din yayi ganin yaki cewa komai ya maida hankalin sa shima kachokam zuwa wajen yana kallon school din. Be ga amfanin zaman da suke haka ba, suna da dama da ikon shiga school din su samu duk abinda suke son samu din amma kuma ya rasa dalilin da yasa Rafeeq din yake wahalar da kansa da rayuwar sa. Duk da yasan yana tsoron rayuwar yarinyar ne da matsalar da yake ganin zai sakata din amma zama a haka ba shine solution ba, dole zai kayi taking risk sannan zaka samu abinda kake so.

“Sir gata nan ta fito.”

Saddam yace yana kallon gate din school din. kokarin tura question paper din take a school bag dinta tana kallon hanyar a nutse sannan ta tsallako side din da suke ta tsaya tana jiran taxi. Kokarin bude kofar motar Saddam yayi da sauri Rafeeq ya dakatar dashi

“Don’t, please don’t.”

“Why? Akan me zaka cigaaba da hurting kanka akan abinda be fi karfin ka ba? Akan me?”

“Just follow her, karku yarda kuma su bace mana, but for now just let her be please.”

Kasa sake magana Saddam yayi saboda tsabar mamaki, sai kawai ya bada umarnin su bi bayan taxi din da ta shiga yaja bakin sa yayi kum.

A hankali suke bin taxi din yadda ba zai gane ba bare ya tsorata ya kauce hanya. A nutse tsaf yake zaune a bayan motar kamar bashi da wata damuwa sai dai a kasan zuciyar sa wani irin tashin hankali yake ji,yana tsoron sake rasata kamar wanchan lokacin.
Traffic 🚦 ne ya tsaida su duk da haka suna daf dasu har aka saki suka sake daukar hanyar suna biye dasu, cikin rashin saa suna zuwa next traffic maimakon su tsaya su sai suka yi U-turn suka dauke hanyar saboda idan sun yi gaba taxi basa zuwa wajen dole akwai hanyar da suke bi ba iri daya da masu private car ba.

“Sir sun juya fa.”

“Na gani.” Yace calmly yana kallon motar ta wuce su ta dauke hanyar, yana kallon sanda ta dago ta kalli side din da yake, sai ya ga kamar an sake sauya ta, ta kara girma akan last ganin ta da yayi, sai dai babu wannan tsadadden murmushin da yake hanga a kowanne lokaci akan fuskarta.

“Ya Allah!”

Ya furta yana tura hannun sa cikin kwantacciyar sumar kansa ya birkitata yana jin duk laifin sa ne, shine ya shiga raguwar ta ya kuma katse mata dukkanin walwalar ta. Ajiyar zuciya ya dinga saukewa a jajjere suna jin sa, kafin ya samu ya daidai ta kansa cikin muryar gajiya da sarewa yace

“Mu wuce office.”

“Ok sir.”

 

🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
07040727902

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button