Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 13-14

Sponsored Links

13-14_*

 

 

Related Articles

Tunda Asmah ta taji wannan hadi da mahaifinta ya shirya yi mata ta shiga  dimuwa da tashin hankali abubuwa suka jagule mata ta shiga  tsananin damuwa abubuwa duk suka rikice mata ta kasa gane ta Inda aka samu asalin barakar sosai take cikin qunci,
A bangaren Dr Aseem Shaheed jinsa yake  cikin walwala sabida ya samu yanda yakeso mahaifin  Asma’u sai ladabi yakeyi masa shima kuwa ya sakar masa kudi tunda ya fahimci kwadayi ne dabi’arsa tuni yasa aka fara gyarawa Mal Husaini gidansa tunma kafin a gama daidaita tsakaninsa da yartasa.
Itakuwa Innah tsallle tayi ta dire tace bada itaba bazaa taba yaudarar Sadiqu da itaba yaron tun asmah batasan kanta ba yakeyi mata wahala sai yanzu rana a tsaka wani yazo a dauki aure  a bashi wannan ai  rashin adalci ne, sosai Asmah ta samu goyon baya gurin Innah hakan ya dan  kwantar mata da hankali kadan.

Karatunta ta mayar da hankali tare da cin alwashin duk ranar da Dr Aseem ya kuskura yazo qofar gdansu saita tata masa asalin rashin mutunci, sati guda da zuwansu na farko tana kwance a dakin Innah abin duniya yayi mata zafi qarfi da yaji Yaya Mudam ya hana Sadiqu zuwa gurinta  saidai  su hadu dashi a burtsatse su tsaya suyi yar  hirarsu babban tashin  hankakinta yanda masoyin ya rame  yayi duhu da sun hadu sai ya fara yimata magiyar karta yarda a rabasu  a mafi yawan lokuta suna kuka suke  rabuwa duk da cewa Asmah bata gama gasqata mgnr auren ba,
Hakanan aketa gyaran gdansu ita  kuma tanaci gaba da zuwa makarantarta har tsayin watanni biyu sosai rayuwa ta fara canzawa a gdansu mal Husaini har buhun shinkafa yake  ajiyewa inda  itakuma a haukanta ta fara mantawa da aikin dake  tunkarota. Kwatsam ranar Wata alhamis sun dawo daga  tahfiz ita da Jiddarh Jiddarh ta biyo zata karbi wani text book.

 

Tun daga  nesa  ta hangi  wasu  manyan motocin alfarma a qofar gdansu guda hudu hakanan gabanta ya yanke ya fadi suka kalli  juna cikin sanyin jiki daidai lkcn da wasu  fararen dattijai suke fitowa daga  soron gdan nasu ta zubansu ido tanason ganesu amma ta kasa sai ajiyar zuciya kawai data suke ta rabasu ta wucce sudinma binta  sukayi da kallo.
Itadai ko arziqin gaisuwa basu samu ba tayi shigewarta gdan garama Jiddarh ta gaishesu suka shiga tabata abinda zata bata ta fito ita kuma ta dauko  buta  ta fito, mamakine ya cikata ganin matan  gdan nasu da yaransu Dijangala da Lantana a tsaye  cirko cirko to dake  ba shiri suka cika ba hakanan tayi shigewarta bandaki tanajinsu sunaja mata tsaki bata ko kallesu ba, fitowa tayi ta shige dakin Innah ta ishesu ita da mudam da Mal Husaini suna tattaunawa,
Kallonta mal Husaini yayi yace “nemi guri ki zauna duk na gama mgn da yan’uwanki kece kikeson ki bani matsala  kuma ke  dinma baki  isaba”

A gajiye ta nemi guri ta zauna Yaya mudam ya zabga mata harara ta sunkuyar da kanta Mal yaci gaba da cewa “dazu iyayen Aseem sunzo akan batun aurenki sun kawo kudin aurensu da sadaki sannan  sun nemi alfarmar ayi biki nan da Wata biyu dadai  nace  Wata biyar  nasa so munyi mgn dashi Aseem din yacemin babu komi zai dauki nauyin komai wannan tasa  da naga sauqi yazo na amince….”
Dagowa tayi da Sauri tace “Baffa Sadiqun fah….” Jitayi an buge mata baki ta dago da idanunta daya  kawo ruwa take ta fara tsiyayar da hawaye Mudam ya nunata da yatsa  yace “shegiya me qashin tsiya arziqi na kiranki tsiya na cewa nice taki  ana mgnr arziqi kina mgnr talauci ubanme Sadiqu zaici bare ya baki gayyar tsiya gayyar wahala…..”

Dagansa hannu Baffa yayi yace “yo miye na bata bakinka abuda babu fashi  sai anyi  kawai kije ki fara shiri nanda watanni biyu zan daura muku aure kowa ta kama gabanta” miqewa sukayi zasu fita  cikin gunjin kuka  Asmah tace “Innah bazakice komai ba don  Allah kiyi wani abu….” Janyota Innah tayi jikinta tana Shafa bayanta sukayi ficewarsu sannan ne Innah tasamu  damar  mgn tace “to me zance Ma’un Innah kinji irin  diban  albarkar da Mal yayimin yau har yana cewa nice nake  zugaki kiqiyi masa biyayya, Asma’uh wannan lamari son zuciya ne saidai kawai Allah ya sakawa wanda  aka zalumta kiyi hqr kiyi biyayya insha Allah zakiga Ribar hakan a gaba”
Kwantar da kanta tayi a jikin Innah tace “wlh Innah badon  Allah Aseem yakeyin duk abinda yakeyi ba akwai manufa cikin lamarin nan Innah kada  kibari son zuciyar su Baffa ya salwantar min da rayuwarta……”

 

Rufe  mata baki tayi tace “Asmah kiyi hqr kuma kisa  kyakkyawar niyya a ranki  insha Allah Ribar abin zaki gani” sosai Innah ta rinqa yima Asmah nasiha hardai ta daina kukan ta koma  ta kwanta  lamo akan gadon Innah tanajin zafin abinda Baffa yayi mata shi bayama  jiye mata wulaqanci?
Ranar ko diban ruwa kasa zuwa tayi saboda zazzabin da yake  damunta

 

Washegari juma’a duk da batajin dadin jikinta haka ta shirya ta fita domin zuwa makarantar daga  yanayin takunta Indai kasanta zakasan akwai  abinda yake damunta, cikin saa tana zuwa gdansu Jiddarh ta ishe  ta shirya suka nufi makarantar a qafa suka tafi  domin dukkansu babu mai kudin Mota suna tafe ne tafiya irinta kurame babu me cewa wani, sunci rabin  tafiyar sukaji Mota a bayansu tanayi musu horn basu  tsayaba saidai kaucewa da sukayi suka bawa mai motar  hanya, zartasu yayi sannan  ya tsaya tare da kashe motar ya fito cikin shigarsa ta likitoci fuskarsa dauke da murmushin da shi daya  yasan ma’anarsa ya tako  inda  taja  ta tsaya tana qare  masa kallo batayi aune ba kawai saiji tayi ya sanya  hannunsa ya dago fuskarta ya dora  bakinsa saman kuncinta ya janye a hankali yana murmushi  yace “to ya kikaga salon wasan  namu?”

 

Takaici ne yasa batasan sanda  wasu  hawaye masu  zafi suka zubo mata ba murmushin fuskarsa ya fadada yace “tun yanzu? Haba  karki karaya da wuri mana aike jaruma ce  kin iya  rashin kunya zaki qwaci kanki dadin dadawa gashi kinyi saa  gyatumai kwadayayyu Allah ya baki kada  ki matsawa zuciyarki wajen tunanin abinda ya dace duk wani Abu da yake ya dace nayishi bayan iyaye shima masoyin na bogine  tunda ya siyarmin da soyayyar a farashi me arha dubu dari  da hamsin kacal kinga ko yanzu zaki iya  bambamce tazarar dake tsakaninmu koda yake banson  ma ki gane  yanzu ki bari sai can gaba saiki gane  lkcn da hakan zaibada show na gaske a lkcn ne wasan zai fara nanda 2 months yanzu sharar fage ce”……….

_Gareku yan’uwanmu na Niger kuma fah kuna  da damar  samun wannan littafan guda biyu idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_

*_Oum Hairan_*
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: *_Zarrah_*

 

*_Fauziyya Tasiu Umar_*
*_Oum Hairan_*

 

 

Littafin _*_ZARRAH* na kudine idan kinason zaki biya 200 ta _account dina_
__0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTBank_ _ko kati MTN ta whattsAp a wannan number 09013718241 ko VTU ta wannan number 09031307566._

_Gareku yan’uwanmu na Niger kuma fah kuna da damar samun wannan littafan guda biyu idan kinaso kiyimin mgn ta WhatsApp akan wannan number,09013718241 sai najiku_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button