Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 41

Sponsored Links

Abba ya kalli Islam yace “mesa kika aikata irin abin nan Islam?” Mum tace “Alaji bawanan ma kadai ba da Farida tamata magana shine fa takifa mata mari ranan harda fasamata baki, haba haka ake abu a duniya, daga yar uwarki tabaki labarin saurayin ta saikibi takasa kije ki kwace mata shi, kasan shi namiji wawane hala saisa lokacin ya biyemata ya yarda har aka turo, yanzu dai alhaji tunda komi yay daidai basaika hukuntata ba nariga na yafemata, faridama ta yafe mata shikenan magana ta wuce a cigaba da shagulgulan biki zamu aurar da ya” Ahankali Abba ya sauke ajiyan zuciya yace “hakane kutashi kutafi” fita sukayi daga dakin Farida ta bangajeta ta shige dakin Mum binta tai da kallo kafin ta wuce dakinsu a daddafe ta fada gado taci kukanta tai bacci.

Manya manyan hajiyoyi masu gyaran jiki Mum ta daukoma Farida nan fa aka fara gyara amarya ciki da waje idan kunga Farida en tai mugun kyau bakin fatarta har kara walkiya take, ko tak baya hadata da Islam idan Islam zata wuni tana mata magana bazata kulata ba hakan yasa kullum Islam na daki, Maman Miemie nema idan tazo aiki takan dan kawomata Miemie ta dauketa suyita wasa, Khaleel bai kara zuwaba, Farida bata damuba tunda wani zubin yanadan picking call dinta suyi magana daya biyu ya katse.

Yau saura sati daya biki yaune aka kawo akwatin Farida saitin goma sha biyar, su Umma da Mujiba datai kini kini da rai dawasu kawayen sune suka kawo inda Mum da kawayenta lecturers suka tarbesu akaci akasha, akasha guda, dazasu tafi aka basu tukuici. Da daddaren ranan Anty Hindu tadawo daga dubai da kayayyakin daki data siyo anata murna Koda Islam tazo gaishe ta kallonta tayi daga sama har kasa tace “ke ciwo kikayine haka wanan rama” murmushi tayi tace “eh amma naji sauki” tsaraba Anty Hindu tabata sanan ta wuce dakinsu ta kwanta.

Washegari da safe Abba yafita da wurin kasancewar yanada aiki, Mum ce ta turo akwatinan Farida ta shigo dasu dakin Anty Hindu one by one tace “ga akwatin Farida nan Anty?” kallonta Anty Hindu tayi cike da mamaki tace ” Farida Kuma wace Faridan?” kama haba Mum tayi tace “au Abban su bai fadamiki ba, ai Anty Kwai ne yafashe gaskiya ta futa, ashe fadan nan da yaran nan sukayi kan Khaleel ne, wai Islam kwacema Farida Khaleel fa tayi, shine da kanshi Khaleel din yay tattaki yazo yafadi ma Abba shifa Farida yakeso ba Islam ba” tunda take maganar Anty Hindu ke kallonta tace “Khaleel din yace hakan” “eh” murmushi Mum tayi tace “ga akwatin ki duba kisa mana albarka” tabe baki Anty Hindu tayi tace “nayafe fitanmun dasu daga daki” tabe baki mum tayi tafita dasu tana kunkuni tace “yar bakin ciki kawai” sosai Anty Hindu taji ranta ya baci da zancen, wanan wani irin abune.

Family Khaleel kodaya fadan musu abinda ke kasa basu wani damuba kasancewa sunsan Faridan dama.
Yau thursday da kyar Yusuf ya tirsasa Khaleel yatashi suje gidan su kaima Farida kudin fati, da wasu yan abubuwa, da kyar yatashi ya shirya dan wlh bayason yamaje gidan balle yamaga Islam shiryawa yay cikin shadda Light brown shadda daya mugun amsan shi ba karamin kyau kayan sukamai ba sai uban kamshi yake, fara tsayawa sukayi sukai isha’i sanan suka tafi.
Farida taci uban lalle dan gobene walima tasanya wata atampa da tasha uban stones, kallon Sameer dake kusa da ita tayi ganin kiran Khaleel ya shigo wayarta tace “jeka cemusu su shigo falo Ina zuwa” fita yay da gudu, ta zauna agaban mirro tana shafa hoda.

Ahankali take sakkowa daga stairs sanye da doguwar riga na atampa jada baki ta daura gyale black akai, so take taje kitchen ta dafa Indomie kamshin turaren dataji yasa ta daga kai hada ido sukayi daidai suna shigowa falon hanunshi rike da Sameer tsayawa yay chak yana kallonta hakan yasa Yusuf ya Kalli inda yake kallo, da sauri takarasa sakkowa ta shiga kitchen, jingina tai da fridge ta dafe kirjinta jin wani abu ya tsayamata awuya, tayi kusa 20 sec ahaka sanan ta shiga store ta dauko Indomie guda daya da egg daya tafito, kamshin turaren shi taji da sauri ta daga kai ta kallai suka hada ido ganin ya kulle kofar kitchen din yasa ta ijiye kwan da Indomie akan fridge tajuya da sauri ta bude kofar dazai satada da backyard tafita, babu haske sosai a backyard din dan kwan fitilar wajen ya mutu hasken wata ne kawai ke haska wajen, tafiya ta soma yi da sauri zata zaga, hanunta taji ankama da sauri ta juyo fizgota yayi da karfi fuskarshi a daure yasata abango yana wani irin kallon fuskar ta, ahankali yake matsowa har ya matso kusa da ita sosai wanda gab din tsakanin su baifi tsawon yatsa ba dan tanajin saukar numfashin shi, sosai kirjinta ke bugawa hakan yasa ta kawad da kanta gefe, ahankali yakai hannu ya kama habarta ya juyo da kanta kin kallonshi tayi ta saukar da idanunta kasa, hanunshi daya ya daura a bangon wajen dayan kuma na habar ta murya chan kasa yace “look at me, kin kasa kallonane sabida kinsan u are forcing me to do dis?” sosai kirjinta ke bugawa, lumshe ido yayi sanan ya budesu akanta ahankali yace “bakyacin abinci ko, look at your neck” yasa hannu yana shafa kashin wuyarta buge hanunshi tayi hanun nata ya kama da sauri yadan matse hakan yasa tai yar kara tana yatsine fuska yace “it hurt ko?” gyadamai kai tayi, dan murmushi yayi yace “zuciya hurt more than this sau dubu dabara sabida abinda kika sata tayi” yakarashe maganan tareda sakin hanunta yana nuna mata zuciyar shi da yatsa, dan shiru yayi yana kallon fuskar ta dan har yanzu taki yarda suhada ido, hannu yakai yarike habarta yadaga kanta kaman mai rada yace “kinfiso na auri yar uwarki ina dawainiya da sonki araina ko” shiru tamai, kasa daurewa yayi ahankali yahada goshin su yana kallon idonta, hakan yasa itama ta dago idanunta dasuka cika da hawaye ta kallai bakinshi taga yay motsi yace “I love you Islam” fashewa tai da kuka sosai, hannu yakai ya share hawayen dake zubowa batare daya cire forehead dinshi daga nata ba, ahankali ya saukar da yatsar tashi akan lips dinta, shafa su yayi yana kallon idonta, hannunta tasa ta bigemai hannu, lumshe ido yayi ya maida fuskar shi ta gefen kunnenta ta, goga mata sajen shi akumatun ta yayi wani yarrr tajj yabi kowani gashin fatarta sabida yanda gashin sajen suka tattaba fatar, kokarin tureshi tafara yi hakan yasa ya cigaba da gangaro da sajen nashi har wajen lips dinta, ahankali ya juyo da kanshi daidai ta wajen hakan yasa lips dinshi yahadu da nata.

Wlh kun daman saisa namuku typing. Gaskiya Naga Farida tafi fans, lol.
I love guys.
[6/22, 7:53 AM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button