Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 42

Sponsored Links

Wani irin jijjiga shi ta shiga yi bayan ta mirgina ta zame jikinta sai kanshi dake saman cinyarta. “Khalil? Ibrahim buɗe idanunka” Duk ta rikice ganin yadda ya sanƙame baya ko numfashi. Debeka dake tsaye jikinta ya ɗauki rawa, Allah yana gani bata yi don ta kashe shi ba, he so much loves him,She loves him very much, his jealousy makes her feel that she will never let him be with another woman other than her. Tsananin kishi ya rufe mata idanu ya sa ta kasa controlling kanta. Gang team ɗin kallon Debeka suke sun san ko da wasa suka taɓa ta sun shiga uku. Majeederh gently ta zame kan Abraham dake cinyarta tana zuwa bata tsaya jiran komai ba ta ɗauke Debaka da wani mahaukacin mari, sai da ta jera mata maruka guda biyar cif wanda suka nemi zautar mata da tunani. Tana pointing ɗinta da hannu ta ce.
“Baki da tarbiyyar da zaki iya haɗa inuwa da Khalil, mara tsafta irinki sam bata dace da shi ba” Debeka da kumatunta ya kumbura ta ce “Who are you? Waye ubanki a duniya bakiɗaya, da har kika mareni kike tunanin kin mari banza?” Ta cikin liƙab Majeederh ta watsa mata harara cike da tsana wacce bata taɓa yiwa kowa ba ta ce “Me? Forget about my father, ki tambayi wacece ni kaina, I Malama Majeederh Abdul’aziz Khan! Idan kin sani better, idan baki sani ba You can search on Google zasu gaya miki” Debeka ta girgiza kai sosai ta ce “Ok shi ne sbd abin kunya wata tsohuwa dake sbd kin rasa mijin aure kika liƙewa masa ko? Kinga sabon jini, daman ke ce wacce kika shiga tsakani kike masa yawo da zuciya har ya kasa accepting nawa matsayin budurwa balle ya kwanta dani? Kin fa haifeshi haba Mama” Sosai Majeederh ta ji zafin maganar jin ta kirata da tsohuwo hala bata san matsayinta a wajan Abraham ba. Ta juya ta kalli Abraham dake kwance su Taj na shafa masa ruwa ya riƙe mararsa gam zufa na yanko masa, ta dawo da ganinta kan Debeka ta ce “Me kika ce? To ina nan ina addu’a da izinin Ubangiji babu wata ƴar iska data isa ta ja hankalin Khalil sai matarsa da sunna wacce addini ya bashi ita duk wuya duk tsanani, ba zai taɓa aikata zina ba, naga kamar baki da cikakken hankali idan baki sanni ba su abokan nasa sun sanni, na raineshi da hannu na yi masa wanka da hannuna, na goyasa a bayan nan nawa, ya yi bacci a jikina akan ƙirjina tun yana 3yrs a duniya, Abraham is my son, ni nake da ikon zaɓa masa matar data dace da rayuwarsa wacce zata taimake shi ya ɗora shi akan tubalin zuwa aljanna, wacce zata ribaci ra’ayinsa ga taimakon al’umma, wacce zata dawo da shi akan hanya, mace mai tsafta da hankali nutsuwa kamala, mai addinin ba wacce ke bin gidan maza ba” She slowly heard him say “The woman you are praying for me to marry is none other than you” Debeka ta saki dariya ta ce “Kenan kanki kikewa fatauci ko? Sannu uwar guzuma kune hajiyoyin dake lalata ƙana nan yara kenan no wonder”
Abraham na jin su, maganganun Debeka kamar saukar mashi haka yake ji, amma ya yi shiru yana son Majeederh bakinta ya buɗe ta fara kwatarwa kanta ƴanci ba sai an shigar mata faɗa ba. Hakan ya sanya ya yi shiru yana mayar da numfashi yana jin yadda lokaci guda jikinsa ya ɗaukeki zafi sosai, mararsa sai harba masa take tana wani irin yi masa masifaffen ciwo. Ganin Majeederh taƙi cewa komai ya sanya Debeka cewa “Na miki al’ƙawarin zan tafi, ban miki al’ƙawarin zan bar miki shi na har abada ba, domin don ni akai Abraham, mahaifinsa ma ya san da zamana, ke uwar riƙo ci ki zauna a matsayinki na hakan, don’t interfere this is family issues, wlh wlh wlh ko wa kika aura masa, ko ke ya aura ku shirya zaman mace biyu a cikin gidan, ba lallai ki yarda ba, amma zaki tabbatar da hakan lokacin da na shigo cikin gidan Abraham Denial David matsayin mata, no one’s can stopping me even him” Tana faɗin hakan ta juya ta ɗauki wayarta ko kayanta bata ɗauka ba ta fice daga cikin gidan.
Takaici ya sanya Majeederh juyawa itama zata bar gidan. A shagwaɓe ya ce “Kin kureta kuma zaki tafi?” Ta juya suka haɗa idanu ya narkar da nashi idanun cikin nata, da sauri ta janye nata sbd abubuwan da take gani cikin ƙwayar idanun nashi ya dafe mararsa ya ce “Mami come and see zafi sosai” Bata saurare shi ba, domin gabaɗaya a dame take jin kanta, ganin zata fita ya sa ya daddafa ya miƙe tsaye yana dafe da mararsa “Taj Close the door” Cikin sauri ya sakawa ƙofar password. A hankali ya juya ya kalle su, ɗaya bayan ɗaya suka miƙe tare da barin parlourn zuwa can garden suka fara hausan dambe a tsakaninsu.
Tun kafin ya ƙarasu inda take ta haɗe fuska sosai, bai damu ba walking slowly yana marairaice fuska cikin salo na jan hankalin wanda ya sanya Majeederh ɗauke Idanunta sbd tsigar jikinta dake tashi tana zubewa, Abraham ya ƙarasa yana sauke numfashi can ƙasa ya ce “Ta nakasa miki ni” Ta yi masa banza ya ƙara narke fuska ya matsa tayi saurin ja baya, yana binta tana yin baya har ta ƙarasa jikin ƙofa, ya saka hannu ɗaya ya dafe jikin ƙofar ya yi mata rumfa da ƙirjinsa da sauri ta runtse Idanunta ta ce “Leave” Ta faɗa muryarta na rawa, sbd gani tayi gabaɗaya ya sauya mata kamar wani babban mutum ya haɗe fuska kamar bashi ne mai yawan ce mata “Sorry Mami ba” Wani irin kallo yake mata magana yake son yi amma bai ma san me zai ce ba, sbd abin baya kansa kuma bai saba ba. Hana ya miƙa zai riƙe nata tayi saurin make hannunsa ta ce “As frm today kada ka sake riƙe mini hannu,ko gigin shigewa jikina” Slowly ya ja idanunsa ya lumshe yana jin wani abu na bin jikinsa musamman da tayi maganar kamar faɗa ta ƙareta a sanyaye. “Me kike tsoro? Idan na riƙe?” Ta yi masa banza tunda magana take son yi amma ta lura idanunsa yana saitin bakinta kaɗan yake jira. Ya ƙara matsawa tare da sakar mata ƙirjinsa wanda yake buɗadɗe sbd ɗaga ƙarfe, ji tayi numfashinta yana fisga da ƙyar ta ce “Ka danne mini ƙirji, ni Maminka?” Ya ware idanu sosai wanda da ƙyar yake buɗewa ya ce “Tafiya zaki?” Kamar ƙaramar yarinya ta ɗaga masa kai sbd ta gama tsorata, a karon farko cikin harshen Hausa ta ji ya ce “To ni fa?” Hausar ko daɗi a baki ba tayi masa ba, abin dry kuma idan ya yi magana. Ta haɗe fuska ta ce “Look! Wai meke damunka ne Son?” Silently ya ce
“Call my name, bana so son” Da wani Expression na tashin hankali ta ce “Ok open the door” Speaking calmly ya ce “In one condition” Kamar tayi kuka ta ce “Wai son mene haka? What exlty wrng wiz you? Ni mahaifiyarka kakewa haka? Kana neman albarka?” Wani lalataccen murmushi ya saki iya laɓɓa da sauri ya matsar da bakinsa daidai kunnenta ya ce “You’re not my mother, u never be my mom, you’re my life partner” Yana faɗin hakan ya zame bakinsa tare da kai hannu ya ɗage liƙab ɗin, yadda fuskarta tayi jajir ya san kuka take daga can cikin zuciya. Ya ɗaga gira yana zuba hannu a aljihu kamar wanda akaiwa dole ya ce “Uncle I told me that, ke uwar riƙo ce, ba kene kika ɗauki ciki kika haife ba, and i also agree with him, tunda muryarki idanunki attacking ɗina ina jin sha’awarki, Uncle I ya ce zan iya aurenki” Jikinta ne ya shiga rawa tana girgiza kanta ta ce “Yanzu kai auren nawa zakai?” Ya ɗan ɓata fuska yana lumshe idanunsa har ga Allah muryarta kaɗan azabtar da shi take, Abraham bai wani damu da kyau ba a rayuwarsa, babban dalilin daya hana shi kula mata sbd duk yara ne shi kuma yana mutuwar son babbar mace, maturel enough. “Har ciki zan baki ma” Sulalewa tayi zata zube a ƙasa don tashin hankali ya yi saurin taro ta, tare da kwantar da kanta a chest ɗinsa a hankali ya yake bubbuga bayanta, wani irin kuka ne ya kwancewa Majeederh tana jin kamar ranta zai fita, me ya sa Uncle Isma’il zai mata haka? Sbd kawai ba tayi aure ba zai lalata tsakaninta da Abraham ya sanya masa ra’ayin da bashi da shi a zuciya? Ya ja mata raini? Duk yadda take da dauriya da riƙe kanta tana mamakin yadda take da saurin kuka a gaban Abraham, he couldn’t feel yadda tears ɗinta suke rige rigen sauka a ƙirjinsa, bai hanata kukan ba sai ma access ɗin daya bata ya kwantar da ita jikinsa ya riƙe gam ganin har wani jijjiga da take, kuka ne wanda yake fitowa tun daga ƙasan zuciyarta wanda ta tara shi shekara da shekaru yake cinta a rai. Idan ta buɗe baki da nufin yin magana sai ta ji wani kukan ya sake taso mata, Abraham idanunsa sukai jajur daman yasan zai sha fama da Maminsa ya riga ya fahimci rauninta tuni, duk wanda ya fahimci rauninka kuma ya gama da kai. Ganin kukan ba mai ƙarewa bane ya sa ya ɗan kwantar da kansa a wuyanta a hankali maganarsa ke fitowa kamar raɗa ya ce “Crying Mama, Crying jee cry as so much as you can!” Kamar wacce ya ƙarawa volume haka ta ƙara narkewa jikinsa tana wani irin kuka mai cin rai. A hankali ya fara rarrashinta duk da bai iya ba cikin kunnenta yake hura mata iska silently with sexy voice yake cewa “Shiii, sorry” Jin tsigar jikinta na tashi ya sanya tayi saurin haɗiye kukan sai hawaye, a hankali ta kalli Abraham kamar yadda yake kallonta ta ce “Enough is enough ka bar maganar iya nan” A hankali ya ce “Ohk, until we get Marriage” Idanunta na wani wajan ta ce “Tsaurin idanunka ya yi yawa, sbd ƙaddara ta faɗa mini har na kawo yanzu ba aure shi ne kake tunanin zan aureka? Kalleka U just 16 yrs, gwanini da kai kake cewa zaka aureni? Kai tsakani da Allah baka ji kunya?” Ta gyara tsaiwa ta ce “I understood, baka son ganina babu aure ne? To i promise you zan fito da mijin aure ka ji Yarona, kabar maganar u still be my son my baby” Abraham she dry ba ta bashi magana take amma bakinta rawa yake inda take kalla kuma da ban. A hankali ya taka har inda take tsaye ya ɗan leƙa fuskarta tayi saurin rufe Idanu ya taɓe baki numfashinsu na haɗiye can ƙasa daga shi sai ita ya ce “I want you Jee, i want to you to be in my side, Ina son ka ƴar madara” Ta watsa masa harara ta ce “Har abada, ƙuruciya ke damunka” Hannu ya miƙa zai riƙeta ta yi saurin yin baya ta ce “Is prohibited in my religion” baya ya ja kaɗan yana ɗaga mata hannu a taushashe ya ce “Ohk, Your religion is difficult” Ya ɗan shafa kansa yana maida hannunsa baya a shagwaɓe ya ce “Marry me, I’ll give u all the happiness in our life” Majeederh ta yi shiru, wannan kamar wani opportunity ne na gyara Abraham zuwa yadda take so, zata gyara masa rayuwarsa da tarbiyya da komai. Murmushi ta yi ta ce “Khalil” Calmly ya ce “Maa” Kujera ta nuna masa, ya miƙa hannu zai riƙe ta ta ƙara janye wa ta haɗe fuska. Zama ta yi saman kujera, shi kuma ya nufi wajan fridge ya buɗe ya ɗauki Favorite juice ɗinsa da apples guda biyu, gently ya juya ya ce “Maa i need food”
Ta yi masa shiru har ya gama kwasu komai, ya dawo ya zauna ya ɓalle murfin lemon idanunsa lumshe yake ɗan sha yana ya mutsa fuska he lost his appetite. “Who are you, Ibrahim?” Sosai ya jita ya basar ya ce “Yunwa ina ji” Ta ce “Ibrahim-Khalil” Ya zuba mata idanu sosai ta ce “Who are you? Where are you coming from? Me kke ɓoyewa?” Shortly ya ce “hiding?” Ya girgiza kai ya ce “Jesus” Ta numfasa cikin dabara ta ce “Ka taɓa ganin ayi aure ba a san mutum ba? Iyaye family e.t.c?” A hankali ya ce “Me kike son sani a kaina?” Ta ce “Ur Father, country da sunan mahaifiya” Murmushi kawai taga ya yi, tare da yin baya ya kwantar da kansa yana rufe idanun, bottle ɗin hannunsa ya matse nan take ta fashe juice ɗin ya zube hannunsa ya fara zubar da jini. “Khalil” ya yi mata shiru tana danne tsoranta ta ce “Abraham” Idanunsa ya buɗe tare da zuba mata su, wani irin ja taga yayi wanda bata taɓa ganinsa ba, a nan kuma ta ƙara tabbar da zuciyarsa rauninsa kuma iyayensa. Murmushi taga ya sake yi wanda ya fito da kyansa duk da baya yanayi na jin daɗi cikin sauyin murya ta ji ya ce “Mother? Uhm” A hankali ya sunkuyar da kansa ya ce “I don’t know her, ban santa ba, she’s alive or not I don’t know” Kallonsa kawai take a hankali ya sake cewa “Idan an ce uwa ke nake kallo, kece mace ta farko data kula dani ta nuna mini soyayya ta uwa, wacce na rayuwa da wannan soyayyar har yanzu, Bayanke maza ne kawai suke tare dani Gang team ɗin nan su ne ahhalina, ina da 10yrs na gama secondary school na fara University a wata ƙasa” Ya yi shiru ta ce “Wacce ƙasa?” Calmly ya ce “Germany” Ta ce “Ohk ina jinka” Ya ƙara lumshe idanunsa wanda duk suka rine ya ce “Daga nan na sauya University, har dai na kammala” Ta jinjina kai ta ce “Ur Father?? Mahaifinka fa?” Ya ce “I hate him” Da mamaki ta ce “Why? Me ya sa me ya yi maka?” Murmushi kawai ya yi yaƙi ce mata komai. Ta ce “Ok Shi ne ya biya maka kuɗin makaranta?” A nan ya yi wata kalar dry sosai yana girgiza ya ce “Funny, ina yaga kuɗin kai ni Germany? Kuma Karatun Likitanci, Welder fa yake” shi kansa ya san ya yaudari kansa sai ya ji kansa ya masa girma na ƙaryar da ya yi. Majeederh ta ce “Kuma ina kai kke samun kuɗi? Me haɗinka da Gang team ɗin nan?” Ƙuri ya yi mata da idanu ta ji ya saki dry ya ce “you’re asking too much, are you trying to change me? use your chance on me” Ya ƙara yin murmushi kawai idanunsa jajur jijiyoyin kansa duk sun fito kallo zakai masa kasan ba daɗin hirar yake ji ba, ya watsa hannunsa tare da cusa yatsunsa cikin suma ya birkitata ya zuba idanu ya ce “You can because I love you, kawai dai Gang team is my happiness in bani da lafiya sune, suke iya ɗaukan haukana” Idanunta ta ji ya ciko da hawaye sbd tausayinsa ya yi kamar bai gani ba ya ce “Me kike so?” Ta ce “Bana son Debeka” Da wani irin sauri ya ɗago ya kalleta bai ce komai ba, ta ce “Bana son Shaye-shaye, yawon banza, kula matan banza, bana son faɗa da kowa ka koyi controlling kanka, kana zuwa wajan mahaifinka bana son gajeren wando ka maida hankali akan sana’arka, idan ba wani doke ba bana son shiga cikin Gang team ɗin nan” Tunda ta fara magana yake kallon bakinta da idanunta ta ce “Kana jina?” Calmly ya ce “Ohk” A wannan karan da ƙyar muryarsa take fita ta miƙe tsaye zata ta fi ya bita da idanu ya saka remote ya cire password sai da ta je bakin ƙofa ta ji ya ce “Zan aureki dole, Abraham baya ƙarya” Da sauri ta fice daga cikin gidan tana sauke numfashi. Akan idanun Bar Aliyu ta fito da sauri ta shiga motarta tare da yin key, dake ya sauya mota bata sani ba, kuma bata hayyacinta hakan yasa sam bata gansa ba. Kifa kansa ya yi a kan hannun motar yana jin zuciyarsa kamar ta fito gabaɗaya ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa, he want Majeederh in his whole life, amma tsoranta yake sauya masa take a ko wanne lokaci, duk sanda ya yi attempting faɗa mata he loves her sai yaga kamar ba ita ba, nan da nan ransa ya ɓaci. He couldn’t sleep, eat, everything komai nasa ya tsaya ya yi asarar contract da yawan gaske. Failing a Shari’a ba a magana. A hankali ya kunna motarshi kai tsaye gidansu ya nufa, lokacin Hajia da Almustapha na zauna a parlour. Tunda ya shigo Hajia ke Kallonsa har ya nemi waje ya zauna yana mai da numfashi ta kasa daurewa ta ce “Aliyu lafiya?” Ba tare daya buɗe ido ba ya ce “Good, ina yini Hajia?” Ta yi shiru ta kasa amsawa. Wayarta ta ɗauka ta kira Dije ta ce “Ki haɗawa Babana abinci yanzu” Dije ta ce “Done Hajia” Ta ɗauke kallonta ga Aliyu ta ce “Almustapha ya matar taka?” Ya ce “Da tare zamu zo ma, bata jin daɗi ne” Ta ce “Ohk, Allah ya sauwaƙe” Ya ɗan juya ya ce “Papa fa?” A nutse ta ce “Ya je meeting, kasan an fara shirye-shiryen tsayar da ɗan takara” El ya ce “Kai, Shi Papa mene haɗin sa da wani takara ne, ban son ya tsaya wata siyasa wlh” Ta yi Murmushi kawai El ya ƙara cewa “Ohk i understand, jam’iyyar su ai ke kan mulki a yanzu, baya so mulki ya fita daga hannunsu” Almustapha ya yi dry ya ce “Kuma wallahi na ji jam’iyyar hamayya da ƙarfinta ta fito, suna da ƴan takarkaru har biyu dole sai sun yi primary election zaɓen cikin gida kafin fitar da gwani, amma da ina zaɓe Abuturab zan zaɓa, he’s a kind of person that i have never seen before, a dai ƴan siyar nan tamu, ya taɓa neman takarar ko house of representatives or assembly na manta, yanzu na kamar ya yi aure wai, amma baya ƙasar jinya yake” Aliyu zancen ya ji yana hawa kansa haka kurum kuma Abuturab ɗin bai masa ba. Hajia ta ce “To Aku, duk ina kake jin wannan labaran?” Almustapha ya ce “Hajia media, a twitter a nan nake ganin latest news na ƴan takarkaru, musamman wanda suka ke viral suna trending in the world” Almustapha ya ce “Kuma ƙyakƙyawa da shi so Masha Allah” Sai a lokacin Aliyu ya buɗe ido tare da kallon Almustapha ya ce “To kai mace ne? Da zaka na description kyan ɗan uwanka namiji?” El ya ce “Kai ban taɓa cewa kana da kyau bane? Idan kaga abu mai kyau ka yaba shi ne kawai, day before yesterday na je gidanka ai” A tsorace Aliyu ya ce “But baka faɗa mini ba?” Almustapha ya dinga kallon Aliyu, shi kuma Aliyu tsoro da kunya ya kama shi “Na je, matarka ta iya girki sosai fa, na ganta tare da wata kamar munafuka mai liƙab” Wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya Aliyu ya sauke, Majeederh ce ta yi girkin. Suna zaune Dija ta kawo Hajia ta saka Aliyu a gaba sai gashi ya tashi da abincin cikin babban plate Kallonsa kawai take tayi tambayar duniya ya ce “lafiya”…. Abuturab na zaune feeling better gabaɗaya kwanan shi biyu da dawowa ƙasar daga Switzerland. Idanunsa ya buɗe da ƙyar jin Maysoon na cewa “Ka fita duba lafiyarka, ka dawo and you’re still sick wai meke damunka ne Yallaɓai? Ina ta ƙoƙarin ganin na kyautata zamana da kai but i couldn’t, ka hana ni duk wata dama da zan kafa soyayyata a zuciyarka” Hawaye na zubu mata hannunta dafe da cikinta wata tara ta ce “Nasan baka so na, amma ni ina son ka, bani da tabbacin zan haife cikin nan lafiya, inma mu mutu tare inma na mutu na barsa ko ya mutu ya barni, don Allah ka nuna mini soyayya a kwanakin nan kafin cikar EDD ɗina na roƙeƙa Haydar” Kuka Maysoon ta saki sosai tana dafe cikinta, Abuturab ya zuba mata Idanu a hankali ya miƙa mata hannu ya ce “Come” Ta ƙarasa ya zaunar da ita saman cinyarsa idanunsa akanta ya riƙo fuskarta ya ce “Maysoon” Tana kuka ta ce “Sir” Ya ce “Ina da ƙulafuci ina da naci, zuciyata nada kafiya akan abinda take so,ki yi mini uzuri ki amsheni a yadda nake, first love ɗina tana wani wajen ke kuma Allah ya ƙaddara zan zauna dake matsayin mata, ina baki ci sha, suttura ina saka miki kuɗi a bank duk wata, Maysoon ina jin zafi a zuciyata ina jin raɗaɗi ki taimaka mini na samu abinda nake so ta hanyar addu’a, yadda nake son ta ko mulkin nan dake tunkaro ni bana so haka, mene matsalarki?” Kuka take sosai ta ce “Are you going to insulate me? Kana faɗa mini ƙarara baka so na, dole akai maka, me ya sa ba zaka duba irin son da nake maka ba Yallaɓai? Ni bani da matsala kaso ko wacce kawai kulawarka nake nema lokacin ka nake buƙata, hatta wannan cikin na jikina Ubangiji ne kawai ya ƙaddara samuwar shi, yaushe rabon daka raɓeni?” A hankali ya ce “Sorry Maysoon” Kuka take ta ce “Please ko sau ɗaya ne” Ya ce “Am not in the mood, ki je” Za ta yi magana ya daka mata tsawa tare da hankaɗeta ta faɗi ƙasa saman ƙaton cikinta, wata ƙara ta saki tana runtse Idanunta Abuturab ko ta kanta bai bi ma ya nufi part ɗinsa, ƙarar data kuma yi ya ya jawo hankalin Mama da mai aikinta suka shigo parlourn a guje jinin dake malala a ƙasan Maysoon ya sanya Mama rikice Maysoon tuni ta fara kokawa da ranta, Mama ta fara kuka sbd tausayi cikin ikon Allah kuma suka fara jin kukan jariri da sauri Mama ta ɗaga Maysoon ta matsar da babyn Salati Maysoon take tana kiran sunan Abuturab tare da yin wata jijjiga idanunta na rufewa, Abuturab Mama ta shiga ƙwalawa kira yana ji ya yi shiru ganin numfashin Maysoon na tafiya baya dawowa yasa Mama fara kalmar shahada,idan ta kira sunan Maysoon sai ta faɗi kalmar shahada cak numfashinta ya tsaya jikinta ya saki idanunta ya yi sama rai ya yi halinsa Maysoon died.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button