Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 33-34

Sponsored Links

33-34*_

 

*_Wattpad realfauzahtasiu_*

Related Articles

Tana gama fadin haka ta juya a fusace ta fara jijjiga qofar da dukkan qarfinta a qoqarinta na ganin ta bude qofar, tsayawa yayi sokoko a mugun mamakance cike da takaicin irin yanda yarinyar ta iya fidda hannu ta zabgansa mari kuma har ta sami damar gaggaya masa maganganu haka son rai.
Ganin yanda take jijjiga qofar idan ya qyaleta tsaf zata fashe masa glasses din jikinta yasashi finciko hannunta da mugun qarfi ya cillata bisa kujera ya nunata da yatsa batasan uwar daya tuna ba kuma ya juya ya fice daga parlourn ya kulleta ta baya ta yanda babu yanda zatayi ta bude qofar kukanta taci gaba dayi me gigita tunanin me sauraro ta dade a zanne ganin batada wata mafita yasata miqewa ta koma saman ta fada gado kanta na juyawa take wani zazzabi me zafi ya rufeta.

 

Shikam yana fita motarsa ya shiga ya zauna ya hada kansa da sitiyarin yana tariyo kalaman yarinyar akansa tabbas ba qarya tayi ba iyaye suna da darajar da bai kamata ace ana maka wasa da alfarmarsu ba to amma meye laifinsa don yace tayi hqr ta zauna? Numfashi ya furzar me zafi kalaman da Hajiya ta fada mawa Asman sunayi masa yawo ba itaba shi kansa baiji dadin kalaman ba yana danganta abin ace shine akace masa maye iyayensa mayu harma aka nasabta wani abu da zahirinsa ansa bashida alaqa dashi aka dora masa ya zaiji a ransa?
Sake furzar da iska yayi ya tada motar ya fice yana kallon fuskarsa a madubin motar sahun yatsunta sun fito sun kwanta rada rada a farar fatar tasa yakai hannu ya shafa tare da fusgar motar ya fice daga gdan lkcn 7:30pm asibitinsa ya nufa ya shige office dinsa ya zauna ya rafsa uban tagumi gabadaya duniyar tayi masa zafi duk wani tunani ya qwace masa kalaman Asmah sun kasa gogewa a mind dinsa a hankali kuma ya rinqajin tausayinta yana sauko masa.

 

Ya rinqa jinjina girman abinda Hajja tayi mata a ransa dole yakamata ace ta samu kalma koda daya ce me dadi daga gareshi amma sai akasin hakan ta biyo baya yaja ajiyar zuciya ya tashi ya nufi inda yayi parking ya shiga motar ya fice saida ya biya wani babban mall yayi musu siyayya samnan ya nufi gdan nasa part din Mimee ya shiga da yake kwana hudu kenan dayi mata aikin ta dawo gda gdan kuwa cike yake da danginta sunata faman mayar da mgn, shi dama ba ma’abocin mgn ba haka ya wucce bai saurari kowa ba ya nufi dakinsa ya cire kayansa yasa marasa nauyi ya sake fitowa ya fice Mimee ta dubi Naja qanwarta tace ta leqa mata taga ina ya shiga.
Tana leqawa taganshi yasa key yana bude qofar Asmah ya shiga ya mayar ya rufe ta juyo tace “gurin matarsa ya tafi” zaro ido tayi tace “wato baiji abinda hajiya ta fada masa ba kenan cewa fah tayi idan ya sake batamin rai sai tasa ya saki yarinyar nan”

 

Murmushi Naja’ah tayi tace “nifa da nice da wannan yarinyar a matsayin kishiya da tuni ta fice tabarmin gdana” kallonta tayi tace “ta yaya?” Sake fadada murmushinta tayi tace “ta duk inda akebi” nan Naja’ah ta rinqa bata shawarwari tana dorata a keken bera ita kuwa ta hau ta zauna ta suka tafa tare da cewa da ita “muddin zatabar gidannan nikuma nayi alqawarin ko nawa ne zan kashe akan mijina”

A kwance yaje ya tarar da Asmah kashirban tanata rawar sanyi ya matsa jikin gadon da sauri ya janye bargon a razane ya zubanta ido bacci takeyi amma na wuya sanye take da qaramar rigar bacci iya gwiwa yaja fasali ya matsa ya zauna a gefen gadon yakai hannunsa saman goshinta yajishi zau yayi saurin gangarawa qirjinta yaji yanda zuciyarta ke bugawa da qarfi ya janye hannunsa a razane ya dagota jikinsa yana jijjigata sai yanzun ya lura ashe bama bacci takeyi ba suma tayi sake dagota yayi yana jijjigata ganin batamasan yanayi ba ya miqe da sauri da ya fita har yana tuntube ya nufi part din Mimee ya dauko key din motarsa ya sake fita da sauri yaje ya ciccibota yasata a mota.

 

Duk abinda akeyi a kan idon Naja’ah tana fadawa mimee sukayi qwafa tare shikam bai masan sunayi ba yaja motarsa a guje yana tuqi yana leqenta tsoronsa na nunkuwa yanda yaji zuciyarta tana bugawa da qarfi dakansa ya sunkuceta har dakin da yake tunanin ya dace yakaita ya fara dubata ajiyar zuciya ya sauke lkcn daya tabbatar tsabar zafin zazzabin ne yasa bugun zuciyarta ya qaru, ruwa ya jorner mata yasa mata allurai ya zauna ya zubawa fuskarta ido yanajin faduwar gaba ya rasa meye yasa duk sanda ya zubawa fuskar Ma’uh ido sai yaji gabansa yana faduwa sosai kyawunta yake daukar masa ido baya gajiya da kallon fuskarta musamman cikin watannin nan da tafara zuwa school ta waye tayi wani mayen kyau me daukar hankali jikinta ya qara murjewa dake tadan qara qiba sai qirjinta ya qara cika hips dinta da bombom dinta suka qara bajewa abin yana mugun birgeshi gashi nema takeyi tafi qarfinsa da idan zai tafi office yake fita da ita ya sauketa yanzun kuwa duk sanda zai fita idan yayi mata mgn sai tace batada lecture dole haka yake qyaleta da abin nata ma ya shahara kawai sai ta daina daga wayarsa ta daina bashi damar shiga part dinta koda kuwa ya shiga to bazai ganta ba tana dakinta ta kulle abinta.
Numfashi ya sauke ya dauki alluran ya daga rigarta ya saita inda zaiyi mata ya soka mata yanajin dumin jikinsa na hauhawa yanajin wani wahalallan yanayi da yake kasancewa a ciki duk lkcn daya matseta, daqyar ya koma ya zauna ya kifa kansa a saman cinyarsa yanajin yanayin yana qara zagaya ilahirin jikinsa a hankali ya gane ashe mugun feelings nata ne yake dawainiya dashi, bai bambamce hakan ba sai tsakanin shekaran jiya zuwa yau da bashi da gurin hutawa dake a baya da mimee ko banza idan yaso kota qarfi zai karbi haqqinsa to yanzun babu dama babu lafiya.

 

Miqewa yayi ya fara zagaya dakin zuciyarsa na ayyana masa abubuwa da dama yaja fasali tare da qaryata kansa a fili yace “habadai tama isa kenan so nake ta qara rainani ashe ma” da wannan yaji taja ajiyar zuciya ya matsa gabanta tayi miqa tare da salati yabi qirjinta da kallo yana hadiye wasu mugun yawu ya zauna da sauri yaci gaba da kallonta idanunsa na rikida, a hankali ta bude nata idon ta fara kallon dakin kafin ta sauke idanunta akansa, lumshe nasa yayi ta yunqura zata miqe zaune daidai lkcn daya bude nasa ya sake saukesu akanta.
Tashi yayi ya matsa gabanta ya taimaka mata ta tashi zaune batare da yayi furuci ba ya koma jikin basket din daya sanya aka kawo ya hado mata tea ya miqa mata ta kawar dakai ya zubanta idanunsa fuskarsa a daure da alamun babu wasa, kawar da kanta tayi ya zauna ya diba a cokalin yakai mata bakinta taso qin sha so amma yanda ya dage din yasata dole ta rinqa karbar tea din tanasha daqyar take hadiyarsa kamar ruwan magani, ta kawar dakai yafi sau goma yana qara matsanta tasha saboda magungunan da yakeson bata aikuwa daya cika matsawa wankeshi tayi da amai da sauri ya miqe ya riqota tanata kakarin aman yana dannanta qirjinta bayan ta gama ya shiga bathroom ya wanke jikinsa ya hadanta ruwa ya dawo sai yanzun ya samu damar mgn da cewa “kije kiyi wanka zakiji qarfin jikinki” itamma zafi takeji hakan yasa ta zuro qafafunta yabisu da kallo komanta me kyau ne sai tsabar iskanci da rashin kunya dake damunta koda yake alamu sun fara ta fara laushi,
Da azamar gaske ya tarota ta fado jikinsa sabida jirin daya debeta ya sunkuceta cak ya nufi bathroom din da ita ya mayar da qofar ya rufe ya ajeta ya fara qoqarin cirenta kayan ta riqe hannunsa da sauri a galabaice tace “kaje zanyi….” Bai tsaya saurarenta ba ya kama rigar ya zare tasa hannu ta rufe qirjinta ya zubanta ido yanajin wani lugudan zucci dana jiki hakanan ta qarfi yayi mata wankan tana kuka tana komai amma yaqi qyaleta yanayi yana bama idonsa abinci duk da bai cirenta pant ba amma shatin HQ dinta ya dauki hankalinsa matuqa har hannusa yakai ya shafa gurin sai kuma ya tuna wani abu kawai ya basar…………

_Comments_
_Share_
_Vote_
_Please_

 

_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

 

_*Fauziyyah Tasiu Umar*_

*ELEGANT ONLINE WTITERS*

 

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button